Chapter 16
Chapter 16
da albashin sa, to zai tsaya ya ga cewa Hauwa bata tagayyara a fannin ilmin sakandire sanadin makantarta ba. Wannan wani alkawari ne da Dr. Sarham ya yi wa kan sa a zuciyar sa, da yake fatan Allah ya bashi iko da tsawon ran cika shi. Sai washegari wajen karin kumallon su akan dining suka hadu da Maman sa da sauran kannen sa biyu wato Sumayyah da Surayyah. Bayan ya gaida iyayen nasu shikuma kannen sun gaishe shi yadda suka saba ya ja kujerar sa ta dindindin a dining din ya zauna. Mama ta tambaye shi me ya faru da shi ne jiya? Nan yake gaya mata labarin aikin da yayiwa Hauwa da yadda yake blaming kansa kamar yadda ya gayawa Abban sa. Barr Mama. itama kamar Abban nasa cewa ta yi ba laifin sa bane. Ta kuma kara da cewa kada ya kara sakawa kansa damuwa irin wannan kan aikin sa in har yana son cimma nasara a gaba, don hakan zai iya sawa ya tsani ‘profession’ din nasa da ya tashi da burin sa. Surayya ta gatsine baki ta ce, dadi na da mutum daurawa kai damuwar wasu, damuwar da Allah bai dora masa ba, to sai me zai faru don aiki bai yi nasara ba da zaka bi ka wuni cikin damuwa har da kulle kofa da yiwa kai horon yunwa ta hanyar kin cin abinci wuni guda haka Yaya Doctor, ina dalili ina dan mafari? Sarham ya jefe ta da harara, Mama ta ce ke bana son rashin kunya, wa ya saka ki a maganar mu? Dagagefen sa inda take zaune Sumayya ta ce cikin jimami. Bhaiya, kayi wa Allah ka kai ni in duba ta, haka kawai naji tausayin ta ya kama ni nima, makancewa fa totally, a hannun ka, ai da tausayi da sanya damuwa, dole ka shiga phobia dinka, dama dai a ce a hannun wani liktan ne ba kai ba bazaka damu har haka ba, Allah sarki Bhaiya na!. Yace I know you always pity me Summy, and you are with me especially in such a bad situation (nasan koyaushe kina tausayamin Summy, kuma kina tare dani musammman a lokaci mara dadi). Madallah da wannan kanwa tawa. Karamar su-babbarsu!. Haka suka karya kumallon suka tashi, masu zuwa aiki wato Sarham da iyayen su suka shiga motocin su daban daban suka wuce wajen aikin su, Surayya ta wuce cikin makaranta inda take karatu anan cikin jamiar Bayero, tana aji daya na digiri a tsangayar ilmin lissafi (mathematics). Sumayya na aji biyu na babbar Sakandire a makarantar Musa Iliyasu College, dake nan daura da sabuwar jamiar Bayeron, suna fitowa ne kullum tare da Yayan ta Dr. Sarham tun bayan fara aikin sa, sai ya sauke ta sannan zai mika zuwa asibitin Murtala inda bai jima da fara aiki ba, bayan yayi aiki na dan lokaci da asibitin Abdullahi Wase da aka fi sani da asibitin Nasarawa, suka maida shi can don an fi bukatar kwararru a asibitin Murtala fiye da kowanne asibitin gwamnati a Kano. Wannan ya faru ne jim kadan bayan dawowar sa daga kasar Saudi-Arabia da kadan, inda ya karanci fannin likitancin ido a jamiar Sarki Abdul Azeez dake Jeddah. **** **** **** Bayan ya sauke Sumayyah ta daga masa hannu, ya ja motar sa zuwa asibiti. Koda ya zo ward round na wannan ranar sai idanun sa suka hango masa gadon da “Hauwa-Kulu” ta kwanta jinya. Nan da nan ya tuno su, wadanda dama da su ya kwana ya kuma tashi a ran sa. Sai ya ji yana son sake zuwa ya duba su, ya ga lafiyar su itada Innar ta. Haka kawai yake jin Innar Hauwa a ran sa, jinta yake kamar uwa a gare shi, sabida halin kirkin ta da dattaku, da kuma tawakkalin data nuna akan abinda ya samu yar ta a hannun su. Don haka da ya fito daga asibiti sai ya samu kansa da juya sitiyarin motar sa zuwa unguwar su Inna, da ya isa bayan Badalar kofar Naisa kasa gane gidan yayi, da tambaya ya isa har kofar gidan su Hauwa don ya kasa ganewa da farko, kansa ma juyewa yayi ya rasa direction abode gidan yayi cikin lungu sosai, amma da yake ya rike sunan maigidan da Inna ta gaya masa kamar ta san zai bata din sai baa sha wahalar kai shi har kofar gidan ba. Dr. Sarham yayi sallama a kofar gidan Mal. Bilyaminu, Inna dake duke tana share tsakar gidan ta amsa sannan ta leko, koda dau taso daukar muryar dama mai kaifi kamar an fike ta anyi sharpening fitar ta gently daga makogaron sa, bakin ta ya koma har kunne da ganin Dr. Sarham, ta dau wankan ta tsaf ta sha wankakkiyar atampa, kodayake dama ta dauki muryar sa, Inna ta bashi iznin shigowa ya sa kai ya rage dogon wuyan sa ya shigo da sallama. Inna ta amsa cike da faraa ta shiga lale marhabin da shi, sannan ta dauki tabarmar karauninta ta shimfida masa. Sarham ya tsuguna har kasa ya sake gaishe da Inna, ya kuma tambayi jikin Hauwa. Inna ta ce cikin damuwa, ai tun bayan tafiyar ka jiya zazzabi ya rufe Kuluwa, ko tashi bata iya yi, sallah ma sai na taimaka mata take iya yi daga zaune, ta dauki damuwar duniya ta dorawa kanta a banza akan abinda Allah ya kaddara mata. Dr. Sarham ya ce, ashsha! Kakata jiki bai yi dadi ba ashe, ki barta Inna, dole ne ta damu, amma a hankali damuwar zata bi jikin ta in sha Allah, bari to in koma in samo mata magani. Har ya mike zai saka takalmin sa sai ya dubi Hauwa dake zaune a kan tabarma daga gefe, ta jingina da filo, ga idanuwan tarr a bude kal dasu, amma shi a iya dan ilmin likitancin ido da Allah ya bashi, da abinda ya karanta, ya san wadannan idanun na Hauwa’u in ba wani babban kudurar Allah ba sun tafi kenan, wato sun tashi aiki sai ko wani ikon Allah, wanda ya fi gaban ilminsu su likitocin fidar idon. Ya matsa gaban tabarmar ya russuna yace sannu Kakus, ina yake miki ciwo? Don in san irin maganin da zan karbo? Ko allura kike so?” Hauwa ta bata rai sosai saboda sunan da ya kira ta da shi kamar wata tsohuwa, haka mafa a asibiti yace mata Kululu bata ce masa don me ba, yanzu kuma yace mata kuskus, ta dan fiddo manyan idanun kamar tana ganin sa irin warning look dinnan, ta yi fuska sosai ta ce masa, sunana Hauwau Bilyaminu ba kuskus sunana ba, kuma ni ai bana tsoron allura inda a hannu za’a yimin, ba sai na kwaye zani ba”, Inna ta ce an ce miki Kuskus din, ke da baki san wasa ba. Yayi murmushi ya sake cewa. Kakus, idan na ce miki sunan Kakata gare ki, wadda ta haifi mahaifina zaki yarda? I mean you have my Grandmas name, Hajiya Kulu Shanono”. Anan kuma sai tayi shiru, don ta san ba karya yake ba, ba kuma zolaya a maganar sa ta yanzu, ta zuba masa gululun idanunta kawai kamar tana ganin sa, yace to sunan ki daya da Kakata Hajiya Kulu (Hajiyar Gadon kaya), ni kuma Kakus nake kiran ta, idan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31