Chapter 24
Chapter 24
karfin su. Mai neman kuka ne aka jefe shi da kashin awaki. Ta ce dama kullace kake da ni haka duk tsayin lokacinnan ban sani ba?. Nake kullace da ke? Ko kike kullace da ni?. Inna bata san me yasa ta kasa sauraron takaddamar tasu ba, ko don cikin zafin rai kowanne yake furucinsa, sai ta tashi salin alin ta saka takalmanta ta dau buta da niyyar ta zagaya bayan gida, ba tare da tana jin fitsari ko kashi ba, kawai ta kasa jure ganin hawayen Hauwa shi kuma ta kasa jure ganin bacin ran sa karara yau, don bata taba ganin sa cikin bacin rai ba, shi Sarham ta fahimci kullum mai kirki ne, mai fara ne, mai walwala ne kuma mai farin-ciki da kowanne yanayi (jovial person). Kasancewar bai taba nuna bacin rai a kan share shin da halin koin kulan da Hauwa-Kulu ke nuna masa ba sai yau, wanda itama ta sha yi mata fada a kan bata kula shi, bata kyautata muamala da shi, bata masa fara kamar bata so yake zuwa gidan su, amma Hauwa sai ta ce, to Inna me kike so in dinga ce masa? Magana ba sai ta dauro ake yin ta ba? To ni ban da wata magana da shi banda gaisuwar da ta zame min dole, kuma ina gaida shi”. Rannan da Inna ta hau ta da fadan ya zo har ya fita ranar ko gaisuwar ma bata yi masa ba, Hauwa ta zaro manyan idanunta waje (ta manta da wa take magana) ta ce, Inna! Idan kin manta ni ban manta ba, daga gyaran ido ya karasa makanta ni, ni duk wannan kirkin nasa gare mu ta baya ta raggo, ido fa na rasa a hannun sa, Inna! Wani abu zai min ya biya ni?” A ranar Inna ta sha mamaki ta kuma tsorata, ta ce au, dama dalilin ki na kin girmama alamarin likita kenan?. Hauwa ta yi shiru, sai can ta kama hawaye. Tace Inna dalili na kenan, amma ba wai na rike shi a raina bane na san kaddara ta ce, amma kullum na tuna shi yasa idon ya karasa macewa saboda careless na aikin sa sai naji tsanar sa ta darsu min, tunda Inna ba abinda zai yi ya biya ni ido na, ba kuma abinda zai min da zan yi farin ciki da shi idan ba idanuna ne suka dawo min ba!”. Inna ta kai hannu zata mari Hauwa, ko me ta tuna? Malam Bilyaminu! Ya taba rokonta ko me Hauwa zata yi nasiha ta kasance tsakaninsu ba duka ko zagi ba, duka baya biyar da yaro yayi abinda kake so saidai ya kara kangarar da shi musamman mautum mai riko irin Hauwa-Kulu. Sai Inna ta rike hannun nata da daya hannun, ta hana shi isa ga fuskar Hauwa. Cikin tashin hankali tace mata na rasa me zan ce miki, Baban ki ya sha gaya min kina da kullata ban taba yarda ba sai yau, amma ina so ki sani Allah ne ya dora miki makanta ba Likita Sarhamu ba, su kawai masu taimakawa ne a samu lafiya amma suma basu hada sani da Allah ba, lalube suke cikin abinda suka karanta don su taimaki alumma kawai. Inaso ki sani Hauwa-Kulu, komai na rayuwar dan adam a rubuce yake a Lauhul Mahfuz, tun kafin halittar sa balle haihuwar sa. Ban so kika saka wannan mummunan tunanin a ranki ba Hauwa-Kulu, domin ya zama rashin yarda da kaddara, ya nuna baki dauki kaddararki da kyakyawar zuciya ba kenan, wanda yana cikin sharuddan imanin mumini. Yi maza ki ce “astagfirullah domin wani Likita duk kwarewarsa ko akasinta, bai isa yayi abinda Allah bai yi ba, kuma shi ba Allah bane da zai bayar da lafiya ko ya hana. Banda son zuciya irin naki, in ma tuhumar ne ni ya kamata ki tuhuma, ni da tun farko ban kai ki asibiti ba tun ciwon yana apolonsa, sai da idanun suka kusa tashi aiki. Haka Inna tayi ta mata waazi mai shiga jiki a lokacin, amma Hauwa-Kulu bata kara tankawa ba saboda miskilancin ta, don haka yanzun ma da Inna ta shige bayi ta bar su a nufin su gama fadan sannan ta dawo, Sarham ya ce wai ta fadi abinda ke ranta yau, kada ta bar shi a ranta ya kashe ta, sai taji kuka ya kwace mata ba kakkautawa a gaban sa. Sarham sai gashi jabar! Ya koma ya zauna dabas a kasa, akan rairayin tsakar gidan su Hauwa. Taja gefen hijabinta ta rufe fuska cikin kakabi da fushi da muryar kuka ta ce, babu komai a raina, sai fatan alkhairi ga kowa”. Sarham ya ce karya kike yi, kuma ni bana shiri da mai karya. Ko amon muryarki ya karyata ki, ya karyata abinda kika fada. Fatan Alkhairi ne a ranki game da kowa? Amma banda a kaina ni Sarham ko? Wa na kashe miki? Ko me nayi miki haka da zafi da kika kullace ni?. Hauwa ta rasa yadda zata yi da shi, don ba zata iya ce masa tana jin maqaqin sa a ranta ba, da cewa bai iya aiki bane ko kuma carelessness dinsa ga aikin sa ne yasa ta makance gabadaya. Sai ta samu bakin ta ya bige da cewa cikin rawar murya da rishin kuka. Ina dakace ne na cewa, inama ina gani! Inama in ga fuskar ka a zahiri in san kamannunka! Rashin idona yana hanani farin ciki da kowa da komai”. Mamaki ya kashe Sarham daga zaunen da yake na yadda nan da nan ta kirkiri karya don kaucewa tunanin ta na hakika, ya dube ta sosai cikin manayan idanun ta kamar tana ganin sa, zai so ace a lokacin da zai fadi abinda zai fada yanzu sun hada ido, yace cikin wata irin murya mai rauni. Maijidda you are accusing me for being the cause of your blindness, (Maijidda kina tuhumata da zamowa sanadin makancewar ki), hakane ko ba haka ne ba?!” Hauwa ta cira ido a firgice, zuwa inda take jin tashin sautin sa, ya daga gira yace Yes, ba wani son ganina da kike yi, karewa ma ba kya son gani na, you are just accusing me. Ni kuma na san bani na makanta ki ba ALLAH ne ya tsara miki wannan jarrabawa domin ya jarrabi imanin ki Maijidda. Nakaa ba komai bace face jarrabawar Ubangiji ga wasu kebabbun bayinsa. Unfortunately, kina neman faduwa jarrabawar ki Maijiddah, domin a zuciyar ki babu TAUHIDI babu IKHLASI. So ya rage naki kiyi maza ki gyara, kiyi istgfari, ki yi kokarin cin jarrabawar ki, ko ki bari shaidan ya ci nasara da galaba akan jarrabawar ki ya barki da biyu babu; ba ido ba imani. Don ni, da ke duka mun san yarda da kaddara yana cikin cikar imani. Hauwa ta dan tsorata da bayanin nan da Sarham yayi mata, amma dai ko ta gamsu da bayanin Sarham bazaka taba gane hakan akan Bakanuwar fuskar ta ba, mai iya boye abubuwa iri-iri da ki-fadi, tace, ta yaya zaka fadi abinda baka shiga zuciya ta ka gani ba? Saidai in dama kana tuhumar kanka ne”. Sarham yayi dan murmushinsa mai ban shaawa domin yanzu ya gama gane manufar ta, da abinda ke cikin ranta a kansa tuntuni da yake
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31