Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 25

Chapter 25

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

saka shi ganin sad expression akan fuskarta, yace. Nayi laakari da maganar hausawa ne da suka ce labarin zuciya ai fuska ake tambaya, kuma dai ‘Im older than you, and Im good at reading minds. Da babbar murya zan iya kiran kaina ‘behavioural analyst’, amma mu barshi a abinda kika fada din, watau kina son ganin fuskata ne, me kike kissimawa akan fuskar tawa? Idan kuma ni din mummuna ne fa Maijidda? Irin munin da in an gani sai an rufe ido don muninsa? Hauwa bata san sanda tayi murmushi ba, alhalin ga hawaye face-face a fuskarta, ta ce mummunan mutum ba mutum bane? Ai mummuna da kyan hali irin naka, sai yafi kyakkyawan gaske nagarta da shiga ran mutum, bayan haka ma a hakikanin gaskiya ni ba wannan nake kissimawa ba, ina kissima yadda fuskar zata yi dai-dai da irin kyawawan kalaman ka ne, koyaushe kana magana wadda ta dace da muhallin ta, kana da tunani na ilmi (with abstract reasoning)”. Sarham wani irin kallon bakinta dake motsi a hankali yake yi, da murmushi yace ikon Allah. Ya akayi ni ban sani ba? Kamar wadanne iri ne kalamai na masu kunshe da abstract reasoning? Irin dai wadanda kake yawan yi cikin surutun ku kai da Inna, wani lokacin ina saurara, nafi zama mai sauraro a hirar mutane fiye da mai contributing, ta nan nake fahimtar yanayin zancen kowa, na fahimci maganganun naka duka a muhallin su kake yin su, kuma a takaice, amma cike da tarin maanoni da alfanu, sannan duk wani cukurkudadden alamari ka san ta yadda zaka bi ka warwareshi cikin hikima irin taka”. Sarham ya zura takalman sa, ya mike idonsa akan Hauwa, yana sakin dariyar da bai shirya zuwanta ba, ya lura yau in zasu kwana a haka, bazai gaji da sauraron dadadan furucin Maijidda gareshi ba, ya ce SAI WATARANA Maijidda sai watarana, ina rokon ki, duk runtsi kada ki bar zuwa makaranta, koda kin rasa dan jagora! Ina nufin against all odds, koda da rarrafe ne ki jure ki nemi ilmi, duk da nasan ba zai zamo abu mai sauki gareki ba, dama duk masu lalura irin taki, amma ki sani Allah ne gatan ki sai kuma shi (ilmin)”. Idan na rasa dan jagora da wanne idon zani makarantar? Misali, idan Salele ya daina kaini ko ya mutu?” Hauwa bata san sanda ta jefe shi da wannan tambayar ba, a lokacin har ya saka kai zai bar tsakar gidan su. Amma jin yadda muryarta ke rawa da karkarwa kamar kuka zai kwace mata yayin fadar hakan, a lokacin da take fadin hakan ma tuni hawaye ya ciko idonta, sai Sarham ya juyo yana kallon Hauwa da wani irin expression a idanunsa, cikin wata irin karaya da kewa, hasken farin wata ya haske masa fararen idanun ta suna jujjuyawa a cikin lalurar rashin gani. Ya kamata ya bata amsar wannan tambayar ta yadda zata dade tana tuna ta, wato tayi ta shawagi a kwakwalwarta, har ta zame mata tsani a rayuwa. Ta hanyar sakawa ran ki cewa zaki iya komai da mai lafiyar ido zai iya, hankali ke gani ido gululu ne, ki tuna kullum da karin maganar da Bahaushe ke cewa “ba nakasashshe sai kasashshe”. Bature kuma yace “theres ability in disability!”. Sannan kullum kisa a ranki “nakasa ba komai bace face wata kankanuwar jarrabawar imani ga wasu kebabbun bayin Allah na kwarai daga Azza wa Jallah”. Wadannan kalaman nasa su suka zamewa Hauwa-Kulu a food for thought, har bayan tafiyar Dr. Sarham daga rayuwar su, bata bar mayar dasu madubin ta na rayuwa ba, fitilar dake haska mata duhun koina dake cikin nakasar ta, sannan jagoran ta a duk lokacin da ta rasa dan jagora, wato kalaman sa ta saka a gaba suke saita mata hanya a duk inda ta nufa, don cimma rayuwa mai amfani a cikin halin data ke ciki na nakasar idanu. Watanni masu dama suka biyo baya suna cikin kewar sa mai yawa itada Inna. Cikin tuno ‘precious moments’ din su tare dashi. Ko na rana guda sun kasa mantawa da shi. Sun kasa mantawa da tarin gudunmuwarsa ga rayuwar su, da lokutan da suka kasance tare da shi cikin yanayi na zumunci da yan uwantaka. Zaman sa na dan lokaci cikin rayuwar su ya dauke musu kewar Baban ta watau Malam Bilyaminu kaso 50% data dan uwanta mai rasuwa wato Zulkifl, duk da a sanda yake zuwa wajen su din bata wani damu da shi ba, sai ma kullata data biyo baya, duk da repentance dinsa gare su akan laifin da ba lallai a kira shi nashi ba, amma bayan tafiyar sa, da irin emotional sallamar da suka yi mai zaunawa a rai, hakan yasa ta yin kewar sa bad an kadan ba. Guzurin kudi da ya bar musu har naira dubu daya sun dade suna cin moriyar su, kafin bayan wasu watanni masu yawa su kare, duk da haka Inna bata bar sanaar ta ba ta sayar da wake da shinkafa da juyen dabbobi a kasuwa duk shekarar sallahr layya. A lokacin Hauwa ta shiga babbar sakandire aji biyu, watarana ta dawo daga makaranta tare da Salele kafin su hawo motar bus da zata kawo su kofar Na’isa Salele ya hango ana hawan kilisa a kan dawakai a tsallaken titi. Saleleh mayen dokuna ne na gani kashe ni, yana matukar son wasan Polo da hawan angonci ko hawan sallah na sallah da sarki ke yi a Kano, tuni suka kwashe hankalin sa daga kan Hauwa, ya bata jakar makarantar ta ya ja sandar da suke kamawa shida ita a matsayin jagora tsakanin su, don ba hannun ta yake rikewa ba duk da ta girme shi, yace. Hauwa, zauna kan bencin can ki dan jira ni in ga wucewar masu kilisar can akan dokuna Hauwa tace toh, amma don Allah kayi sauri Salele, ka san yanzu Inna tana duban hanyar mu, kada ta ga mun dade ta damu. Salele tunda ya nausa cikin yan kallo ya bace mata bat! Shiru shiru Hauwa na jiran Salele bai dawo ba, karambani irin nata yasa taga cewa bari dai kawai tarabu da shi yau tayi kokarin kai kanta gida kada hankalin Inna ya tashi. “Dr. Sarham” yace ba ido ke gani ba hankali ne ido gululu ne kawai. Sai ta tashi da zummar ta tsallaka titi ta tari motar kofar Naisa, don daga yadda take jin karar motoci ta san a bakin titi suke, tana tafiya a hankali abunta kanta a kasa ba tare da ta san ina take saka kafa ba ai dai mutum ya gane da kansa bata gani shi ya kauce mata. Ai kuwa bata jima tana tafiyar ba taji ‘horn’ din mota a tsakar kanta, wanda ya kidimata ta diririce ta kwasa da gudu, motar kuwa bata yi kasa a gwiwa ba wajen kwasheta, ta yi sama da ita sannan ta nana ta da kasa. Salele dake tsallakowa titi akan idon sa mota ta kwashe Hauwa. Ya dora hannu a ka ya rafsa ihu yayi kanta a tsakiyar titin yana fadin na shiga uku, Hauwa ban ce ki jira ni ba? Hauwa!!!” Mai motar ya gangara gefen titi ya tsaya, ko kafin ya fito daga motar jamaa sun taru a kan Hauwa ana salati. Da yake

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});