Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 10

Chapter 10

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,203 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sai hakikanin kamannin fuskar sa, ba don komai ba sai don ta kwatanta su da kyawun kalaman bakin sa. Ta kasa manta sautin murmushin nasa. Haka kalaman karfafawa marar lafiya zuciya cikin mutumtawa wadanda Dr. Sarham ya yi mata a lokacin, bata jin har abada zata manta su. Ya bata hope na cewa zata rayu, kuma zata warke cikin yarda da amincewar Ubangiji; wanda ya saukar da cuta kowacce iri tare da maganin ta. Tsananin tsoron da Dr. Sarham ya gani cikin idanun Hauwa-Kulu, da karkarwar da jikin ta ya fara lokacin da zaa yi mata allurar anaesthesia, ita ta saka shi dakatawa daga abinda yake yi wato saka safar hannu, ya sake matsowa daidai kanta har tana iya jin kamshin balaraben turaren sa, cikin taushin murya da lallashi Dr. Sarham yake cewa, Relax Hauwau. Zamu yi aikin nan lafiya da iznin Ubangiji kinji, kuma zaki samu lafiya Insha Allahu, zaki warke, saki ranki kin ji ko Hauwau? Daga haka aka soka mata allurar ‘tafi-da-ran ka wanda hakan yasa Hauwa runtse idanun ta, kuma ta tafi cikin barcin ne da mafarkan kamannin LIKITA SARHAM! Da fatan ko a lahira Allah ya hada fuskokinsu. Don gani take kamar ta tafi kenan, duk kuwa da hope din da ya bata, har abada ba zata farka ba. Wato dai Hauwa ta tafi barcin ne da kintacen fuskar Likita Sarham a zuciya da kwakwalwar ta, na wani irin kintace, da dakace, da kuma hasashen ko shin yaya kamannin sa na zahiri suke? Idan aka yi laakari da irin kyawawan furucinsa/kalaman sa??? Dr. Sarham na iya ganin yadda Hauwa ta runtse marassa lafiyan idanun ta masu cike da ciwon hakiya a kan saitin fuskar sa… (with utmost curiosity) na son ganin hakikanin kamannin sa.. Lokacin da ya dora hannnu akan idanun Hauwa-Kulu domin fara aikinsa da bisimillah dauke a bakin sa, sai ya ji wani sako na kwakwalwar sa kamar yana yi masa amsa kuwwa akan kada yayi, yana janye shi daga yi wa Hauwa aikin ido, yana ce masa kada yayi wannan aikin, don 10% ne tsammanin waraka wato nasarar wannan aikin kashi goma ne cikin dari. Amma aka ce kaddara ta riga fata!!! Ya ci gaba da aikin sa cike da fargaba don ji yake tamkar wani dabaibayi ya zo ya dabaibaye hannayen sa ya rikita shi, ya hanashi yin komai daidai, don wannan itace tiyatar hakiyar ido (cataract surgery) ta farko da zai yi a rayuwar likitacinsa. Amma wannan bai isa ya zama dalilin kwacewar azancinsa da kwarewarsa ba ai. Lokacin da yayi nisa da yi mata aikin, sai ya ji hannun sa da jikinsa sun karasa rikice masa da karkarwa gabadaya, zazzabi na shigarsa, zuciyar sa ta hau raurawa, ilmi da fasaha da training din abun duk suka kwace daga kwakwalwarsa ga wani gumi da ya hau yanko masa ta koina, zazzabin da wani irin ciwon kai na kara karfi, ji yayi ya koma tamkar wani dan koyo anan take, ya nemi iyawarsa da jajircewar sa a aikin tiyata da jaruntar sa wajen yin ta duk ya rasa. A karshe ma Sarham ji yayi ya koma dalibin ajin farko da ko sakandire bai gama ba, exactly dai yadda maaikatan jinyar nan masu gulmar sa su Nos Saratu suka suffanta shi, har daya daga cikin su ta ce tsautsayi kadai zai sa ta bashi idon ta. Watakila kwacewar azancin da ya same shi a take, yana da nasaba da gulmar su Nos Saratu dasu Metron Maria, da ya saka a ran sa ya dameshi tun ranar, da suka saka shi cikin wani hali na rashin yarda da kansa. Gulmar tasu ta dade tana yawo a cikin kwanyar sa, domin a zahiri sun ci fuskar sa, sun kuma raina matsayin iyawarsa da darajar kwalayen sa kamar yadda suka raina shekarunsa. Bai san ta ina zancen nasu mara dadi ya samu halartowa cikin kwanyar kan sa ya hargitsa shi irin haka ba, musamman a daidai yanzu yayin gudanar da aikin nasa da ya kamata ya samu nutsuwa fiyeda kowanne lokaci, ya ji ya koma tamkar lokacin da yake cikin ajin sakandire a Science College Dawakin Tofa, ko kuwa sanda yake dan koyo na matakin farko a MBBS, inda ya koyo aikin likita a jamiar Sarki Abdul Aziz. **** **** **** HAUWA _ KULU A n yi aikin Hauwa lafiya an basu gado domin su yi jinyar idon kafin lokacin da likita zai kwance mata shi, a duba nasarar aikin ko akasin ta. Makwabtan su Inna da yawa sun zo har asibitin domin duba Hauwa. Tun ranar da ya yiwa Hauwa aikin nan Dr. Sarham bai dawo asibitin ba yana gida ya killace kan sa a dakin sa yana fama da zazzabi da masassara da ciwon kai na damuwa da zullumi, domin kaso 80% na zuciyarsa na gaya masa cewa yayi kuskure a cikin aikin tiyatar da ya yi wa Hauwa. Ilai kuwa ranar kwance idanun Hauwa ta zo, sai ranar ne Dr. Sarham ya shigo asibitin Murtala Muhammed. Bayan ya gama abinda zai yi a ofishin sa cikin rashin fara da rashin walwala kamar da (wanda ba halin sa ba kasancewar shi mutum ne mai yawan sakin fuska ga maaikata, mai fara da faram-faram da mutane musamman marassa lafiyan da suka zo gare shi) amma yau bai tsaya ganin kowa ba yana gama abinda zai yi a ofishin sa sai ya nufi dakin kwantar da mata domin ya duba aikin da ya yiwa Hauwa Bilyaminu. Tun daga bakin kofa marassa lafiya da masu jinyar su ke gaisar da Dr. Sarham A. Shanono, shi Sarham, an yarda likitan kowa ne, sannan marasa lafiya na son shi saboda kirkin sa da farar sa, yana dakatawa a gaban kowanne gado yana amsawa cikin mutuntawa da tambayar kufan jiki, saidai fuskar nan ba murmushi kamar na kullum, murmushin nan da baya rabo da kyakkyawar fuskar sa ta fulanin Shanono yau babu shi. Haka yayi ta bin su daya bayan daya yana jin lafiyar su. Kusan kowa ya gane cewa shi din mutum ne mai mutunta jamaa ba Innar Hauwa kadai ba. Har ya iso ga gadon Hauwa, wadda itace a gadon karshen dakin, suka gaisa da Inna da ke zaune a gefen gadon kan Hauwa bisa cinyar ta, ya tambaye ta ko yaya jikin na Hauwa, ta ce tun jiya take min korafin ciwon kai, amma Nos dinnan ta zo ta bata magani. Ta nuna daga cikin Nosis din da ke bayan sa, wadanda suke take masa baya su biyu suna gatsine mata fuska na kin zama ba yadda zamuyi dake. Bai kula da zancen Inna ba don hankalin sa kusan baya jikin sa. Bakidaya ya tafi ga son sanin aikin sa yayi nasara ko aah. Ya dauki file din Hauwa ya duba yayi rubutu a ciki sannan ya karasa gaban gadonta, yace cikin murmushin fatar baki wanda bai je koina ba. Kululu-Kuluwa, Kuluwa yar gidan Innarta, yau zaa kwance ido, ina fatan kin shirya? Daga kwance ta amsa na shirya mana Dr, yau sati guda ban ga hasken rana ba, ka bi ka kunshemin ido da bandeji. Ta bashi dariya amma sabida yana cikin fargaba murmushi kawai yayi, ya fara kuncewa. Da adduoI a bakin sa. Nos din da ke bayan sa ce ta taimaka masa, suka

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});