Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 17

Chapter 17

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ban kira ki Kakata ba bazan iya cewa Hauwa ba, don in ta ji na fadi sunan ta haka gatsau, ba sakayawa, sai tayi kuli-kulin kubra da ni. Hauwa bata san sanda ta yi dan murmushi ba, sabida yadda Sarham ya fadi kuli-kulin kuburar ya bata dariya matuka. Ya ce daga yau ni da kaina zan saka miki sunan da ya dace da kyakkyawar diyar Inna kamar ki, kin ga daga Hauwa, har Hauwau, har Kulu, zuwa Kuluwa duk na tsofaffi ne Inna ta lika miki, don haka ki lamunce min daga yau in kira ki da MAIJIDDAH!. Ai kuwa nan da nan Hauwa ta washe baki, fararen hakoranta suka bayyana, batun yau take so a kirata da Maijidda ba amma ba mai kiranta da hakan. Dr. Sarham ya ce, amma bisa yarjejeniyar banni arawa kowa sunan nan, nawa ne nikadai, ni na saka miki, don haka nikadai zan kira ki da shi, ke ko wani kika ji ya kira ki da shi ki gaya masa ba nasa bane nawa ne, ban yarda ko Inna ta kwaikwayar mun ba. Inna tayi dariya tana cin goro ta ji Sarham ya kara burgeta, ko ba komai yau ya saka Hauwa murmushi don ta manta rabon Hauwa’u da murmushi (ear to ear) irin haka, watakila tun kafin ta fara ciwon idon yayi na apolo. Yadda Sarham yayi ta yi musu hira sai da zazzabin Hauwa ya sauka a take, ba tare da sun san lokacin da ya sauka ba, ko dama damuwa ce ta sanya a ranta ta hanata sukuni har ta saukar mata da zafin jiki, amma duk da haka Sarham bai kyale ta ba saida ya fita chemist din Lamco ya samo mata magunguna da first aid kala-kala ya dawo, har da gorar locozade da daurin gasassar kaza da biredi. Ga kayan shayi ya sayo musu makil, tun daga kan sukari, milo da madara har da lipton. Lokacin da ya dawo ya tsugunna gaban Inna yana nuna mata komai kasa magana ta yi ta ce dan nan ya da wahala haka? Ya murmusa yace kada ki damu Inna, na neman albarka ne. Inna ko ta shiga shi masa albarka kwando kwando sannan shi da kan sa ya dau kunshin naman ya isa gaban Hauwa, ya bude ya tura mata gabanta, kamshin kazar nan wadda taji kayan kamshi na gargajiya har cikin kwakwalwar Hauwa wadda rabon ta da abinci dama tun kokon safe da ta dan kurba, don ta rasa ‘appetite’ dinta gabadaya, yace kanwata ci nama ko zazzabi ya idasa tafiya sosai yana ganin yadda ta hadiye miyau, mukut, a makoshin ta, amma don karfin hali da ki-fadi irin na Hauwa sai tayi fuska, ta ce ita ta koshi, sai ya ce “to in ni ne baki so in ga lomar ki, bari in tafi, Inna zan wuce gida sai an kwana biyu, kin san na zama dan ki yanzu, zuwa gidan mu sai kin gaji kin kore ni. Inna tace wane mutum ya kori mai kaunar sa, likita Allah ya jikan mahaifan ka, idan suna raye kuma Allah ya kara musu lafiya da nisan kwana mai albarka. Wannan addua tafi komai dadi da ga Sarham, da sauri Dr. Sarham yake amsawa da Amin-amin ya rabbi Inna, Abba da Mama duk suna lafiya, cikin koshin lafiya. Allah ya karawa kanwata Maijidda lafiya, da Yakanar karbar kaddarar ta. Tun daga wannan ranar gidan su Hauwa ya zama wajen zuwan Dr. Sarham hira, wato tsakar ginan Inna ma tsafta da wadatar iska ya zama dakalin hirar sa, kusan kullum ya taso aiki sai ya je, su yi hira su yi dariya shi da Inna, hirar duniya iri-iri haka suke yini yin ta suna nishadantuwa da daukewa kai damuwar duniya. Inna tayi girkin ta mai dadi ta zubo masa, tuwo ne, dambu ne ko danwake ko dafadukan alkama da ire-iren su, ko gudun kurna da miyar taushe, sai ka ga Dr. Sarham ya mike kafa a kofar dakin Inna ya nade hannun riga ko yayi loosing tie din suit din jikin sa yana kwasar girkin Inna na gargajiya irin wanda baya ci sam a gidan su koda sadaka zaa hadashi, musamman da ya fahimci irin tsaftar Inna, har yan gidan su saida suka gane ya daina cin abincin ranar sa yanzu a dining. Ballde ya zana ya ci abinci tare dasu. In sun yi magana ya ce ya ci wajen wata Innarsa ne. Ga Inna da jin radio komai ta ji a radio sai ta kwashe ta gayawa likita Sarham, shikuma da yake ba maabocin sauraron radion bane sosai yake jin dadin labaran duniya daga radio mai jini wato Inna, sam Hauwa bata iya saka musu baki don ta fahimci daga Innar har Sarham maganannu ne na karshe (talkatives), ita kuma Allah bai halicce ta da yawan magana ba, ciwon kai take saka ta, don haka sau tari haushi sosai suke bata. A wani hutun karshen mako wato ranar wata lahadi Sarham ya zo gidan, Hauwa na duke gindin famfo wai wankin kayanta take yi, ba yadda Inna bata yi da ita ba kan ta bar su zata saka Salele ya wanke mata in ya shigo, Hauwa ta ki, wai wankin Salele baya fita, Inna ta ce cikin subul da baka, “da wanne idon zaki ga wankin har ki san ya fita ko bai fita ba? Ai kuwa Hauwa ta fashe da kuka sosai, wai Inna ta yi mata gorin ido. Ta tattara kayan wankinta ta yi bakin famfo tana ta dirzar su kamar Allah ya aiko ta tana kuka wurjanjan. A haka Dr. Sarham yayi sallama a gidan. Inna ta amsa daga dakin ta, ya shigo har dakin nata don yanzu ba bakon sa bane, dardumar Sallahr ta ta shimfida masa tace Lale Maraba da Da na Sarhamu yayi dariya yana kokarin zama ya ce Inna kema sunan bakin Abban mu zaki koyi lika min, don a ce ni din wani tsoho ne ko? Bayan ko talatin ban rufa ba, ina cikin twentieth dina? Inna ta ce kai da Kuluwa ban san waya fi wani son yarinta da gudun tsufa ba, ita ta hana a kira ta Kulu, kai ma kace Sarhamu tsoho ne, bayan ainahin sunayen kenan kuke bata maanar su da zamananci. Sarham yace by calling Hauwau da Maijiddah, ai baa bata maanar sunan ba Inna, tunda inkiyarta ce ta hakika. Inna ta ce “hakane kuma, duk inda Hauwa take, Jidda ce. Sai ya dubi inda Hauwa ke wanki bata kula shi ba yau, duk da dama ba wai kula shi ta ke sosai idan ya zo ba, amma akalla ta kan ce masa sannu da zuwa, tacigaba da sabgar gabanta ta manta dasu, ta hanyar kame bakin ta, amma yau kam ko uffan bata ce masa ba, bata kuma kai hankalin ta kan su ba, sai wanki take dirka lokaci zuwa lokaci ta na tsane ido da habar zanin ta. Inna me ya samu autar ki haka? Wa ya taba miki Maijiddah? Kamar kuka haikan naga tana yi? Inna tace “ai tana jin ka, tambaye ta mana. Waka a bakin mai ita tafi dadi. Wai daga cewa ta bar wakinnan Salele yayi mata, shikenan ta maida abun tashin hankali. Sarham ya ji wani iri, ganin kukan Hauwa’u ya karu da

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});