Chapter 4
Chapter 4
Allah ya hore masa a lokacin da yake tare damu, bai yarda ya tara komai ba, in dai iyalin sa bazasu nemi komai su rasa ba. Kafin ni Hauwa, Innarmu Safiya da Babanmu Malam Bilyaminu sun haifi Yayana Zulkifilu, wanda ya jima da rasuwa tun yana saurayi dan shekaru sha biyar da haihuwa, ya rasu ne a sanadin wankan cikin rafi (wankan kogi) na samari irinsa marassa ji da fitina, sai ni kanwar sa Hauwau, Hauwa – Kulu, ko kuma ace Kuluwa” duk babu wanda bana amsawa sai Kuluwa. Mahaifiyar mu wato Inna ita kadai take kirana “Hauwa” ko ta ce Kulu”. In kuma ta bushi iska ko in ta so ganin zumburo bakina, sai ta ce Kuluwa din. Malam Bilyaminu Ya kasance mutum mai kyakkyawar muamala da makwabta da abokan sanaarsa a kasuwa, kai dama duk wadanda suka zauna tare da shi a unguwar Kofar Naisa da Wambai sun yi masa kyakkyawar shaida. Shiyasa alamarin bacewarsa rana daya ya girgiza duk wanda ya san shi. Ni kadai ce yar sa a raye a duniya yanzu, a yayan da ya Haifa wajen guda biyar, wasu sun mutu a ciki, wato wasu an haifesu stillbirth, daga kaina kuma ni Hauwa-Kulu, ko batan wata Innata bata sake yi ba, ni nasan Inna tana matukar so na, watakila don ni kenan guda da Allah ya bar mata. Tun daga wata fitar Babana kasuwa bai dawo gida ba, babu inda Inna bata je neman sa ba, haka ba inda bata turani ba data san yana zuwa. Har gidan kanin sa Zakari ta je neman sa, duk da ta san ba wajen zuwan sa bane, masu iya magana suka ce “in abinka ya bata, duba har inda baka tsammanin shigar sa”. Wannan ne dalilin ta na zuwa Dan agundi gidan Baba Zakari cigiyar mijin ta Malam Bilyaminu. Baba Zakari da ya fito sai ya gyara tsayuwar sa a kofar gidan sa yana gyatsa, sannan ya dubi Innar Hauwa da wani kallo a tsiyace, irin na kashi wannan ya fi ku daraja a ido na, yace cikin gatse, “Halan kin yi batan kai ne? To yana inda kika bani ajiyar sa a kuryar daki na ko, in banda neman jidali yaushe rabo na da matsiyacin mijin ki da bai san hakkin zumunci ba, yo banda neman magana irin naku na mata me zai zo yayi min? Ko ya gaya miki akwai wata sauran kadara tsakanina da shi ne bayan ta yan ubancin da ke tsakaninmu? Don haka sawun ta a likkafa ta bar kofar gidan Zakari. Bayan ya caccaba mata bakaken maganganun da gobe koda sadaka aka hadata bazata yarda ta sake tako kafafun ta kofar gidan sa ba. Tun ana maganar batan nasa kadan-kadan, har Innar Hauwa ta tabbatar mijin ta wani abu mara dadi da bazata ce ko meye ba watakila ya same shi, ko daga irin muggan mafarkan data ke yi a kan sa, ko dai ya bata, ko ya mutu a wani wuri inda baa san shi ba, don bai taba kwana a wani waje tun sanin ta da shi da ba a gidan sa cikin iyalin sa ba. Batan mahaifina ya faru ne tun ina yar shekaru goma, wannan alamari ya sanya mu cikin wani hali na damuwa da dimuwa mai tsanani, wanda ya kusa haukata Innar Hauwa, kasancewar mahaifiyata wato Innar Hauwa, irin matan nan ne da miji ya gatanta ta hanyar dauke musu nauyin komai na rayuwar yau da gobe, don haka bata sanaar komai sai kiwon dabbobin ta, duk abinda zasu ci shi yake kawowa, hatta omon wanki da sabulun wanka Malam Bilyaminu ya daukewa iyalin sa. Don haka batan sa ran daya ya daga hankalin ta dana duk wani mai kaunar mu kamar Malam Isa, kada tilon yar sa wato ni Hauwa in ji labari, domin na saba da shi kusan har fiye da yadda na saba da Inna don shi kam Baba ba kwaba ne ba hantara ba kamar Innata ba. Daga baya da watanni suka mika baa gan shi ba, kuma babu labarin sa, sai aka tattaro duka kayan sayarwarsa na gwanjo da ke rumfar da yake ajiyewa a kasuwa aka kawo mana gida. Daga wannan lokacin rayuwa ta sauya mana nida Innata, takalihun rayuwata ni Hauwa ya koma kan Innata kacokam, kasancewar bamu da tabbacin Malam na raye ko mutuwa yayi ya fi komai daga mana hankula, sannan a wancan lokacin baa satar mutane balle a yi tunanin ko an yi garkuwa da shi ne mu jira kira. Daga baya daga ni har Innar Hauwa muka ga babu mafita banda addua agare shi, sai Inna ta maida komai ga Allah ta kuma saka nima na koma yi masa addua kan Allah yasa a koina yake ya fada a hannu nagari, hannun da ba zai taba cutar dashi ba. A duk sallahr farillar Inna tana rokon Allah idan Baban Hauwa yana raye, Allah ya bayyana mana shi cikin koshin lafiya, idan mutuwa ya yi, Allah ya bayyanar da hakan a gare mu hankalin mu ya kwanta, ta maida hankalin ta kacokam! Kan kula da rayuwar tilon yar ta wato ni (Hauwa-Kulu). Ganin cewa yanzu bamu da mai taimaka mana ta fuskar ciyarwa sai Allah sai makwabta da muka saba ciyar da junan mu, musamman gidan malam Isa, komai na gidan da Malam ya ajiye mana a rumbun abinci a hankali ya kare tas, sai hakan ya sa Innar Hauwa ta fara tunanin sanaar yi, daga karshe ta tsayar da sanaar da ta fi yawa ga matan cikin Badala wato sanaar dafa abincin sayarwa a cikin gida don nemar mana na batarwa dana cefane da bukatun yau da kullum. A kullu yaumin Inna ta kan dafa shinkafa da wake tiya daya, dahuwa mai kyau, ta soya mankulin ta da albasa, ta daka yajin maggi, bata dora min talla a dalilin tana cikin masu adawa da tallan yara mata, ta fi yarda da in je makaranta fiye da in nemar mata kudi, don haka tun Baba yana nan ina zuwa makarantar boko da safe, da ta allo da yamma. A rashinsa kuma ban fasa zuwa ba. Da aka gane tsaftar abincin ta a hankali har gida ake zuwa a saya, kuma akwai wani yaro anan makwabtanmu wai shi Saleleh, yaron ya saba da Inna ya shiga jikinta don shi yake zamarwa Babana a shago in zashi wani wuri, bayan batan sa ya cigaba da shigowa gun Inna tana bashi abinci da haka har suka saba don haka shi ta roka yake zuwa ya fitar mata da abincin makarantar bokon da nake zuwa, wato makarantar firamare ta gwamnati ta Kofar Naisa, wadda bata da nisa da gidanmu. Ita kuma tana bashi abincin data dafa da naira goma daga cikin cinikin kullum ya dawo. Kafin sha biyun rana Saleleh zai dawo da kudin ta a kulle a leda cif. An sayar da wake da shinkafan, har ana neman kari, sabida dadi da tsaftar abincin Innar Hauwa. Sai mu yi cefanen abincin gobe kuma, mu kuma yi amfani da ribar da muka samu. Idan shekara ta zagayo Innar Hauwa na fitar da ragunan data kiwata ta sayar a kasuwar Raguna duk sallar layya, sai ta sayi wasu kanana ta kara kiwatawa zuwa shekara ta gaba. Da wadannan sanaoin guda biyu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31