Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na zai kwanta, to amma ga yadda Allah ya tsara min. Ina fatan kafin in dawo Inna zaki tsaya akan karatun ta na sakandire har Allah ya cika min wannan burin nawa”. Inna gaba dayan jikin ta ya mutu. Bata san ta saba da Sarham ba sai yau da yake maganar barin kasar mu baki daya, bata san dimbin alkhairin sa mai yawa bane a gare su, sai yau da zai bar su. Kokari take ta mai da hawayen da suka kawo mata cafka, don kada ta kara karya masa guiwa da tata karayar, don hatta yadda yake maganar kadai zaka san ya fi ta shiga damuwa da kewa, ya karaya. Hauwa dai ba tace komai ba, amma a cikin ranta wani irin ‘dakace’ take yi, cewa take inamainama! Inama na ga fuskar sa yau, inama nayi masa kallon karshe yau kafin ya barmu, wanda zai sa kullum nake tuna fuskar sa, in yi ta masa addua!. Don duk tsayin lokacin nan da suka kasance da Sarham a cikin rayuwar su kusan koda yaushe cikin wannan fatan take, ba don komai Hauwa take son ganin fuskar Sarham a rayuwar ta ba, sai don ta yi quenching curiousity dinta a kan kamannin sa ta kuma yi matching din fuskar da kyawawan kalaman bakin sa na kullum a kan su, wadanda a kullu yaumin masu maana ne wadanda suke kara mata son ganin kamannin halittar sa, shi Sarham mutum ne mai fasahar zance na ilmi, da girmamawa ga mutane, ba tare da laakari da matsayi ko ajin rayuwar su ko nasa matsayin ba, kalaman Sarham har kullum masu tausasawa dan adam ne, a duk halin da yake ciki ya san kalaman da ya dace yayi masa, wato koyaushe kalaman sa na tafiya ne da irin yanayin da ya tarar da kai a ciki. Alal misali, in ya lura kana cikin farin ciki zai taya ka da zolaya da tsokana yakara maka farin ciki, haka in bakin ciki kake shima zai taya ka har a murya da zuciyarsa, daga yanayin kalaman sa kadai zaka tabbatar (he feels what you are feeling) kuma yana tayaka. Sarham ta kwana da sanin cewa shi din, wani kyautar Ubangiji ne koko tace (dauki) da Ubangiji ya kawo cikin rayuwar su, ya hada su da shi, a lokacin da suke tsananin bukatar tsayawar namiji a rayuwar su. Ubangiji ya nufe shida shigowa rayuwar su ne don ya zame musu fitila mai haske kuma sanyi daga kuncin da suka samu kan su rana daya na nakasar ta, wanda in ba hadin Allah ba, ba abinda zai sa ya shigo cikin rayuwar su ya tsaya kamar Yayanta na jini. Domin ta kowacce fuska babu ta inda rayuwar su ta zo daya. Yau da yake cewa zai tafi, har tsayin shekaru uku sai taji cewa lallai zasu yi rashin da baa mayarwa, zasu yi kewar da bata karewa, don shekara uku ba kwana uku bace, abu ce ta mai yawan rai. Inna ta cigaba da hana kanta kuka a gaban Sarham, tana gayawa kanta saboda su ba zai fasa gina rayuwar sa ba. Yo fisabilillah don su aka halicce shi? Daga taimako? Kuma dai duk wani abinda ya dace don kyautata rayuwar mutum Sarham ya gama yi musu shi, tunda yayi wa Hauwa sanadin cigaba da karatu bayan iftilain da ya same ta. Sun koyi abubuwa da dama daga gare shi, irin su magungunan da ya dace da taimakon farko na cikin gida (first aid), home hygiene, sanitation duk karshen wata, cin balance diet a gargajiyance da irin abincin da suke da shi, sun koyi abubuwa masu yawan gaske da suka shafi kiwon lafiya a bakin sa a dalilin zamansu tareda shi. Haka kuma ko yau bai yi shiru ba sai da ya ce da Inna ga kudi zai bar musu ta tabbata ta sayawa Hauwa auduga mai yawa a chemist, bai yarda da kunzugun tsumma ba, yace ita ba ido ba, don haka ba iya kula zata yi da kanta ba kada yaje ta dauki kwayoyin cuta. Kunya duk ta kama Inna. Kulu kuwa da ace a da ne Dr. Sarham ya fadi haka da tuni ta hau shan kunu da fushi da bacin rai na cewa an yi mata gorin ido, watakila harda su kuka, amma da yake yau itama zuciyarta ta tabu da zancen tafiyar tasa ba tace ko uffan ba, saima kunya da taji sosai itama kamar Innar. Inna har sai da ta kasa rike hawayen nata a wannan karon, da ya ajiye mata kudi masu dama a gabanta, tace. Dan nan shekara uku ba kwana uku ba. Allah yasa ka same ni a raye, rayuwar nan da bata da tabbas. Allah yasa muna da rabon sake ganawa, Allah ya hada fuskokinmu da alkhairi. Allah ya albarkaci rayuwar ka ya baka ilmin da zaka je nema, ya kuma baka dukkanin abinda kake nema a cikin samunsa, ya huwwace maka saukin sa, ya kuma baka albarkar sa. Amin- amin Inna, nagode kwarai da gaske da wannan addua mai dadi daga bakinki, na ji dadin zama da ke Inna, zan kuma yi kewar ki ba dan kadan ba!. Sai da ya tashi tafiya yaga Hauwa ba tace masa komai ba, koda kuwa adduar fatar baki ce, ta sunkuyar da kai kawai. Wannan karon kam ya kufula da wannan mugun hali nata, ya ce Kuluwa!!!”. (Sunan da ya san ta tsana, kuma yana kular da ita), ta dago manyan idanun nan tayi harrr! Dasu a saitin da ta jiyo tashin muryar sa, ga mamakinsa hawaye ya gani ya kwanta dankam a cikin su, ya basu wata irin kala kamar na mai jin barcin da ke hamma, ya sake cewa, ko ba da Hauwa-Kulu-AKA-Kuluwa nake magana ba?. Hauwa ta tsuke baki, sannan ta sosa hanci cikin jin haushi, bata amsa ba, sai can data mula taga damar magana don kanta sannan tace, amma dai saboda Allah in mutum ya nuna baya son suna, bai kamata a dinga kiran sa da shi ba, har raina bana son suna KULUWA! an ce miki Kuluwar, Kulun Majadun, Hauwa-Kulu, Kululu, da wasu idanuwanki kamar na Kuliya (mage/mussa). Ke kam baki ji dadin halin ki ba, wallahi ba don Inna ta tabbatar min a gida ta haife ki ba, da na yi rantsuwa an canja mata ke a asibiti. Don Inna ba sumumu-kasau bace, bakin ta baya shiru don ya cutar da ita, ki fada kar ta kashe ki, mai yuwuwa kafin shekara ukun na mutu! Ko ke kin mutu! Ko dukkan mu mun mutu! Don haka fadi abinda ke ran ki yau da nazo yi muku sallama, ba tare da mun san ranar sake haduwa da juna ba. Hauwa zan iya rantsuwa kan ban taba jin kin yi min magana da ta wuce sentence biyu ba, a tsayin shekaru biyun da nayi da sanin ki. Ga wani ‘sadness’ da nake gani akan fuskarki a duk lokacin da kika ji sallamata a gidan ku. Me nayi miki haka? Meye dalili? Na rantse gaisuwa ma akan dole kike yi min ita. Kulu baki dauke ni dan uwa kamar yadda na dauke ki ba.. Hauwa-Kulu sai ta fara hawayen babu gaira babu dalili, ko da yake dama sun cika idon tuntuni suna so su zubo ne, tana fin

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});