Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,213 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ni Hauwa da Inna ta muke rayuwa har tsayin shekaru biyu da batan Malam, muna cikin alhinin rashinsa. Duk da cewa ni Hauwa ba wata kyakkyawa bace acan-acan, gani nan dai kalar Kanawan usli, wankan tarwada kuma makimanciya ga kyau, banda idanuna farare manya dasu masu kama da zagayen kwan zabo, ba abinda zaka ce mai bayyannnen kyau ne a halitta ta. Na farko bani da tsayi, kuma bani da rama, amma bazaka kira ni mai kiba ba, gani nan dai yar duma-duma haka, lubu-lubu mai jiki (luscious) tubus-tubus kamar na kulba, na kasance yarinya mai zafin nama tun ina karama da kwazon taya Inna aiki, sannan da tsananin son Uwa-mahaifiya da tausaya mata, musamman dana wayi gari babu Baba tare da ita, na fahimci ita kadai take buga-buga da kulle-kulle don ganin ban rasa komai ba. Hakika na saka son Inna ta da yawa a raina, da tausayinta tun ina kankanuwa mai cikar lafiya, ga Inna da kujuba-kujuba a cikin gida tayi wannna ta koma ta yi wancan, shiyasa nima bana kyuya wajen taya Innata aikin abinci da ayyukan cikin gida tunda na soma kawo karfi, ni dai bar ni da shiru-shiruna na rashin son magana da rashin son hayaniya, sai manyan idanuwa tubarkallah masu yiwa wanda duk na harara barazana, farare kal dasu, masu haske da sheki da wani kwantaccen ruwa a kasan su, inna juya ido sai ka ga kamar hawaye ya kwanta. A kaina akwai tarin sumar hausawa baka mai karfi irin cunkus dinnan, wadda bata taba ganin man shamfo ba (relaxer) ko na Danjangabo da ake amfani da shi a lokacin domin motsa gashi. Ni Hauwa tun ina kwailata akwai son wanka da yawan shafa turaren ‘Binta-Sudan’ ko ‘Dan Duala’ wanda na Inna ta ne da take yawan siya don amfaninta, kullum tayi wanka su take shafawa, sai nima na ara na yafa. Lokaci-lokaci Inna kan sai min maina na shafawa na musamman (Dela-Maigurguwa), can gaba da zamani ya kara sabuntawa wato ‘cream’ ya shigo, sai ta koma saya min ‘TonyMontana’ don nima in jera da yammata, a lokacin a shekaru goma sha biyun da nake dasu sune matakin farko na fara zama budurci, duk da ko kirgen dangi ban fara ba. Komai nawa dai-dai misali ne na asalin hausawa gaba da baya, kuma na halitta wanda babu kirkirarre. Zaku iya kiran ni Hauwa Kulu da (natural black African beauty) ta zamanin da na taso. A wannan shekarar da aka shiga na samu kammala makarantar firamare, na zana jarrabawar kwamen intarans, watakila don na fara karatun da wuri ne na gama firamare da wuri, inda ba da jimawa ba sakamako ya fito, Hauwa sarkin himma (ta bakin Inna), na ci makarantar yammata ta gwamnati ta jeka ka dawo wai ita Shekara (GGSS Shekara). Asalin iyayena kanawa ne na usul, wadanda ake kira Kanawan cikin Badala. Wane tudu wande gangare duk aka bi za a fahimci daga Inna har Malam yan asalin cikin kofofin Kano ne, basu da wani kauye da zaa ce daga can suka fito ban da kwaryar cikin birnin Kanon. Inna iyayen ta sun jima da kwantawa dama yan cikin Kofar Kansakali ne, kusan yanzu ita kadai ta rage a raye cikin jamaar gidan su babu wanda zata kira nata da ya saura, ta haifeni a shekaru na girma tana da kusan shekaru arbain sanda ta haife ni, shi yasa wasu ke dauka Kaka ta ce, babu wanda Inna zata kira nata a halin yanzu duk sun gushe, banda makwabta da abokan arziki da suke rayuwa a lungu guda. Shi kuwa Malam Bilyaminu yana da dan uwan sa na jini Zakari mai wankin hula, yana nan a raye da nasa iyalin a unguwar kofar Dan agundi wadda ke daura da kofar Naisa. Sabanin Malam Bilyaminu shi Zakari Allah ya bashi haihuwa da yawa maza da mata sun kai goma, sabida yana da yawan aure-aure, mata biyar ya aura, uku ne a gidan yanzu, don haka yayan iyaye daban daban suka haife su, sai dai ka samu biyu a daki daya ko uku a daki daya, amma kowa ya san babu jituwa ko kankani tsakanin Malam Bilyaminu da kanin sa malam Zakari sai yan ubanci na gani kashe ni, wanda a kan sa suka rayu tun suna kanana har gashi sun cimma furfurar su basu daina ba. Bayan batan Malam, Inna na yawan korafi gareni, “tun batan dan uwan sa bai taba zuwa ya ga halin da muke ciki ba, bai kuma taba tuna wai dan uwan nasa ya bar diya mace guda daya, yayi tunanin kula da lafiyarmu ko da bai taimaka mana da komai ba”. Sai in ce Inna kenan. Ai bai ma kamata ki damu ba Inna, don dama kin kwana da sanin ba batan sa ba damuwar sa bane, da kin yi shawara da ni ma bazaki je cigiyar Baba gidan sa ba Inna. Amma a cewar Innar Hauwa, lalurar batan mutum ta wuce komai, don gara a ce mutuwa yayi a kan ta, a ganin ta sun cancanci kulawar sa ko yaya ne a bayan ido dan uwan nasa. Wannan shine cikar zumunci. Wani abun mamaki shine bai fi shekaru biyu da batan Malam Bilyaminu ba, aka wayi gari aka ga Baba Zakari ya kudance, ya rushe gidan sa ya zabga ginin katon gida mai dakali biyu irin na masu kudin da, anan kofar dan agundi, ya sayi motar yayi ta zamani da ake kira Marsandi, ya kuma bude katon shagon sayar da atamfofi a Singa. Sunansa ma ya koma Zakari mai atamfa. Ba irin maganganun da mutane basa yi akan arzikin Zakari na rana daya, wanda babu wanda ya san inda ya samo shi. Shikuwa ya kame bakin sa daga tambayoyin jamaa da an yi magana Baba Zakari zai ce DARE DAYA Allah kan yi Bature. Wannan ba shi ne a gaban Innar Hauwa da ni kaina Hauwan ba, sai shirin fara karatuna a makarantar yammata ta Shekara, abinda Zakari bai yarda yaran sa maza da mata ko daya cikin su ya yi ba hana rantsuwa in ka dauke babban cikin su da ya saki uwarsa ta fita dashi shikadai yake yi a boye, wato Jamil Zakari, da kannen sa ke kira “Yaya Jamilu”. **** **** **** APOLO” W ani ciwon ido ne na yayi (eye flu) da aka yi annobar sa a wasu shekarun can baya. Wanda daukacin yara da manya dai-dai ne suka tsallake shi. A wani wata na Junairu da muka shiga, bazan manta ba aka wayi gari da annobar cutar ciwon ido na apolo a garin Kano, yaya aka yi yaya aka yi? Ko wane tudu wane gangare aka bi aka samo? Sai gani nima Hauwa na samo nawa rabon na apolo, daga makarantar bokonmu ta Shekara. Amma Inna ta gagara dauka sabida karfin jinin ta da shaye-shayen magungunan gargajiyanta yana bata immunity iri- iri. Da farko Innar Hauwa bata dauki abun nawa da muhimmanci sosai ba, don haka bata damu ba, duk da idon yayi jajawur ya kuma kankance kamar gauta, abinda yasa bata damu ba shine kusan kowanne yaro ya samu rabon sa na apolo a wancan lokacin, kai har manya ma, don in yaro daya ya samo duk gidan su sai sun raba (dauka). Amma in aka kwana biyu ko uku

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});