Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 28

Chapter 28

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,214 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

na sunsunar takalmi. Wani babban abinda yafi bata mata rai, duk shiru-shirun Hauwa da miskilancinta in da Jamilu suke hira kaji ta har tana kyakyatawa tun daga soro, tana hira rai-rai-rai kamar kanari ita da shi, ta sake da shi sosai abin ki da jini! Asabar da lahadi da baya zuwa aiki a gidan su yake wuni, makale da Hauwa, Inna ta rasa yadda zata yi da Jamilu. Daga baya ya fito fili ya gaya mata shi fa kamun kanwarsa yake yi, da zarar ta kare sakandire zai kawo sadakinsa. Inna kam bata yi kasa a gwiwa ba ta ce Jamilu kana wasa! Kaima ka san wannna abu ne da ba zai taba yuwuwa ba, don haka na roke ka daga yau kada ka kara tada wannan maganar mara yuwuwa. Ni bazan raba ka zumunci da yar uwarka ba, amma bana bayan wannan maganar wai auren zumunci kai da ita. Jikin sa a sanyaye ya koma gida ranar, kuma kai tsaye ya yanke shawarar tunkarar mahaifin sa a kan maganar, a yi ta ta kare. Komai ta fanjama-fanjam. Malam Zakari sai da ya bari Jamilu ya gama bayani kaf cikin kankan da kai, da tsananin ladabi ga mahaifin nasa, sai ya ce masa, kai kai kai! Kai kuma ta nan ka bullo? Auren makauniya? Diyar BILYAMINU jafai a cikin zuria ta? Toh ban shirya haifar jikan da zai zo ya zama dan jagora ba. Ko ya gado makanta ya saka min a cikin zurria, ko babu makanta haihata-haihata jinina ya gogi na Bilya jafai, jinin jaraba jinin masifa jinin tsiya da rashin arziki. Idan ka kuskura ka sake zuwa inda suke, idan na ji labari, sai na tsine maka albarka. A gigice Jamilu ya bar gaban Baban sa, o ganain gabansa baya yi, shi kuma Zakari Jamilu na tafiya ya saka takalman sa ya fito ya rufo shagon atamfofin sa dake cikin Singa. Da ya fafuri mota bai tsaya a koina ba sai a Badalar Kofar Na’isa. Gidan ai ba zai taba bace masa ba, tunda kuwa gidan gadon su ne, Bilyaminu yayi masa karfa-karfa ya raba shi da shi, don haka kai tsaye ya tuna hanya, bayan tsayin shekarun da ba zai iya tuna yawan su ba rabon sa da ko bin hanyar. Zakari ya yi sallama a zauren Inna, da katotuwar murya mai razana wanda ake yimawa. Ta na tsakiyar dabbobin ta tana zuba musu dussa, ta ji muryar sa yana kwada sallama kamar zai tada gidan Safiya, ina Safiyar ne? Diyar masu Danjangabo?. Nan da nan zuciyarta tace mata ZAKARI!. Don shikadai yake kirata diyar masu Danjangabo don sanaar mahaifiyarta kenan. Inna ta dago kai cikin mamaki ta tako ta iso soron ta yi tsaye a gaban sa, bazata iya tuna rana ta farko da ya tako kafar sa gidan su ba tun bayan rigimar mallakar gidan, da a karshe ya sayarwa Malam Bilyaminu. Ai bai kamata kiyi mamakin gani na yau ba, tunda ke kika takalo ni, kuma kin sanni farin sani kamar kashi nake, sai an kula ni nake doyi”. Zakari ya fada cikin gyara murya da gyara tsayuwa. Inna tace, dole in yi mamaki mana tunda dai na san banza bata kai zomo kasuwa yo daman ina kuwa zata kai shi? Sai ya ji wuta! Zuwa nayi in ja kunnen ki, in sake ja, da kwantareriyar murya, in kin ji kin dauka, ki zauna lafiya, in kin ki ji ba kya ki gani ba. Ki saki kurwar Da na Jamilu ta shakata, don shi ba nakasashshe bane, haka kawai kin ga yaro da maikon sa shine zaki bi dare ki bi rana ki lika masa makauniya ko? Yo Allah na tuba ko Kulu idon ta hudu kinga ta dace da Jamilu yaro son kowa dan gata dan asali, mai ilmi, mai nasaba, Uwar Bilya kuwa ki bincika tarihi kiji inda uban mu ya samo ta, can ne cikin zuriar su barbushe da tsimbirbira. Inna Safiya ta yi tsaki ta ce kana tunanin ko Hauwa ta rasa miji saboda makanta, ko tana yawo tsirara saboda talauci, zan dauketa na baiwa dan ka ko shugaban kasa ya zama? Ai ni martabar diyata da kake gani, duk da take marar ido, miskiniya, wallahi tafi karfin gidan ka, wulakantaccen gida na rashin tarbiyyah, gidan da daga yan daba sai yan shaye-shaye, sai sauta ga wawa rututu. Uba daya uwa kowa da tasa, kurwar ya ta kurr da shiga irin wannan laanannen gidan na Allah wadai, in sha Allahu. Zakari ya kyabe baki duk da ya ji mugun ciwon maganganunta, ya ce ni dai na gaya miki, kuma aure-aure ai arziki ne, idan fitsari banza ne kaza tayi mana, shi bai iya ya kara ko daya ba saboda talaucin da yasa shi barin gida, ke da aka gudu aka bari bakin jini yasa ba wanda ya taba zuwa ya sunsuna ki da sunan aure, a haka zaki mutu gwauruwa, da makauniyar ya a gaban ki kina mata tsarkin kashi. Daga yau zan zuba C.I.D a kofar gidan nan, aka kara gaya min an ga Jamilu ya shigo, duk abinda ya same ki ke da makauniyar yar taki ku kuka da kanku, ke kika saya muku da kudin ku, lakadan. Ya juya ya tafi, ya bar Inna tana tsaki. Juyawar nan da zata yi sai taga Kulu a bayan ta curko-curko da ita, manyan idanun ta kamar sa fado kasa don tashin hankali, tayo waje dasu bakidaya. Inna tayi kwafa tace, gara da kika ji da kunnen ki, irin tijarar ubansa, marar lissafi, gobe ki kara tankwashe kafa kina hira da Jamilu da sautin murya kamar na gyare, a zo a ci mutuncina ban ji ba ban gani ba. Jamilun da kin riga kin san waye ubansa, ko wanene Zakari ba bakon ki bane ba. Jamilun bai san an yi haka ba a washegari ya zo wa Hauwa sallama zai wuce wani workshop’ da banki ya tura su na sati daya a jihar Delta. A take kuwa aka kira Alhaji Zakari a waya aka gaya masa, ga Jamilu nan ya sake zuwa. A ranar, duk da Inna na cikin bacin rai, haka ta hadiye shi, ta zaunar da Jamilu a gabanta, cikin lalama ta roke shi Allah Annabi ya rabu da Hauwa-Kulu, kada ya kara zuwa gidan su. Ta warware musu shi da Hauwan irin tsohuwar gabar da ke tsakanin iyayen su maza tun kafin a haife su, a sanadin yan ubanci kawai, ba wani kwakkwaran dalili. Ta kuma gaya masa ita a yanzu girma ya cimmata, bata fama da ciwukan zamani ko guda daya, don haka bata son abinda zai tada hankalin ta. Ta ce masa Hauwa kuma ka gani nakasa ta same ta, wadda tasa bazan iya yi mata aure ba sam-sam, balle na kai ta cikin iyalin Zakari, zai iya hura wuta ya babbaka min ita, a karshe Inna tace. “Jamilu daga ni sai kuma Allah kadai muka ragewa Hauwa-Kulu, ni kadai ce karfin ta a yanzu, don haka ina tattalin rayuwar ta ne bazan iya kaita inda bazata taba samun kwanciyar hankali ba, koda zan mata auren, balle in kaita gidan ku. Balle kuma bazan taba yi mata aure ba in ba idanun ta ne suka dawo ba. Don haka na roke ka Allah da Manzonsa

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});