Chapter 18
Chapter 18
maganar da Inna tayi, kamar ta kara kunna ta, amma duk da haka bata fasa wankin da take faman yi ba kamar na dole, har da kara karfin sheshshekar kukan ta, Sarham ya mike daga kan dardumar da yake zaune ya matsa har inda Hauwa take wankin a gindin famfo ya russunna a gaban ta yace. Maijidda yaya haka zaki tadawa Inna hankali? Kinsan bata son kukan ki. Hauwa tayi sharbe, hannu a bayan ido, ta ce bayan gorin ido tayi min?! Gorin ido kamar yaya? Ta fashe da kuka ta ce cewa fa tayi wai da wanne ido zan san kaya na sun fita ko basu fita ba, menene wannan in ba gorin ido ba? Sarham yayi kokarin danne dariyar sa ya ce easy Maijidda, ko kowa zai miki gorin ido, ai banda Inna. Ke dai kin fassara maganar ta ba daidai ba sabida dama akan tsini kike, amma ba haka Inna take nufi ba, kin ji? Ta gyada kai tana share hawaye. Ya ce to tashi ki bar wankin haka, in ya zo sai ya karasa ai har na gama dauraya nake yi, sai shanya. Yace to dinga daurayewa kina bani ina shanya miki Hauwa ta zaro ido ta ce. Lah! Likita da kai, zan saka ka shanya ka jika jikin ka? Sarham ya ce likita bazai taimaki kanwar sa ba? Shi dama ai mai taimakon alumma ne tun asalin sa da haka ta yarda, ta ke dauraye su daya bayan daya tana miko masa, yana karba yana shanyawa akan igiyar shanyar su, nan da nan suka gama. Dr. Sarham ya ce da Inna zai tafi gida, ba zai jima ba yau, dama ya leko ne kawai ya gansu ya wuce saboda Mama ta aike shi Dakata. Suka yi sallama shi da Inna. Har ya kai bakin kofa ya tuna abinda ya kawo shi yau, kukan Hauwa yasa ya manta, sai ya dawo ya ce “Inna kiyi wa Maijidda shirin tafiya makaranta gobe, amma ba tata ta da zata koma ba. Na nema mata makaranta wadda tayi daidai da masu irin lalurar ta (special school), yadda zaa yi ta dinga zuwa tana dawowa kullum shine ban sani ba, inata tunani a kai har yanzu. Inna taji idon ta har kwalla ta taru, wato shi Da nagari wanda ya samu tarbiyyar iyayen kwarai daban yake, ba sai wanda ka haifa ne kawai zai iya zame maka Da ba, da gaske akwai yayan mutane yan albarka fal a duniya wadanda baku hada kowacce irin alaqa ta jini ba, don dama damuwar ta kenan tun bayan makancewar Hauwa cewa itada karatun sakandire yaya zasu karke? Gashi tun ba’aje koina ba likita Sarhamu yayi musu maganin wannnan damuwar. Ya share musu wannan hawayen. Me zata yiwa wannan bawan Allah banda duk sallahr farillar ta ta roka masa rahmar Ubangiji da gafara ga iyayen sa ba don sun mutu ba? da gamawa dasu lafiya. Godiya sosai Inna tayi masa, ta shi masa albarka iyaka, sannan tace kai ta da daukota wannan ba damuwa bane Salele zata yiwa magana ya dinga kaita kullum yana zuwa ya dawo da ita in sun tashi”. Sarham ya ce shi kuma ya saka masa albashin hakan, don kada yau da gobe ya gaji. A yammacin ranar Sarham ya kawowa Hauwa uniform na Special School ta Kano, littafai, jakar makaranta da takalmi sau ciki da socks. Ita da kanta Hauwa saida ta rasa ta inda zata godewa Dr. Sarham. Mafarin fara karatun Hauwa Bilyaminu a special school kenan, tare da sauran yaran Kano da zagayen ta masu visual impairment’ (lalurar gani.) Dr. Sarham yayiwa Hauwa photochromic glass baki saboda ta dinga sakaya kwayar idanunta cikin hasken rana kada (sun exposure) yayi ma kwayar idon ta lahani wadanda kyawun su mai matukar ban mamaki ne, kamar bayan makancewar tasu an kara musu wani (added beauty) a cikin su, da haske mai daukar idon duk mai kallon ta. Washegari litinin tun kafin ya tafi asibiti ya zo gidan don kai Hauwa makaranta da kansa, ya kuma ce da Inna da Salele duk su tafi tare don su ga makarantar ya kuma gabatar da su ga malaman makarantar. Hakan kuwa a ka yi. **** **** **** Hauwa-Kulu ta soma zuwa makaranta kullum tare da Saleleh da yake yi mata jagora, in lokacin tashi yayi ya je ya taho da ita. Hauwa ta soma karatu tare da sauran yara irin ta ta hanyar ‘Braille reading and writing’. Wanda ake koya musu tun a mataki na farko a matsayin hanyar rubutu da karatun su. Hauwa’u an zama daliba, karatun data ke yi kullum ya dauke mata damuwar rashin idon ta manta da komai, kafin shekara ta zagayo a yi canjin aji na gaba Hauwa tayi na daya har sau uku a kowane zango, ta iya rubutu da braille sosai ta kuma iya karatu da braille din tiryan-tiryan. Sabida har a gida karatun take yi bata hutawa yasa Inna ta dauke mata tayata da ayyukan gida, ko tayi kokarin karba don ta taya ta Inna cewa take koma daki kiyi karatu kin ji Kulu na yafe miki, ba nakasashshe sai kasahshe, nakasa ba kasawa ba, kiyi ta karatu da nakasa domin kubuta daga bara da tozarta, aikin gida ba naki bane. Nawa ne, nida Allah ya baiwa lafiya. Sarham ba sosai yake zuwa gidan su Inna yanzu ba, saboda yanayin ayyukan nasa sun koma safe da yamma. Don haka sai karshen mako yake samun leko su Inna ya ji lafiyar su, ya kawo musu sayayyar da yakan yi musu ta kayan masarufi idan ya dauki albashin sa, yana matukar farin ciki da cigaban Hauwa ta fuskar karatu, da kokarin da take yi a ajin su kullum. Don yakan je wajen malamanta ba tare da su Inna sun sani bama, don bincikar progress din ta, ana kuma tabbatar masa da irin kokarin Hauwa bana wasa bane, gifted ce. Don hatta lissafi (mathematics) da yake baiwa makafi wahala a braille ita Hauwa tsaf take ganewa abinta. A karshen shekarar har kyauta aka bata wato ranar hutun karshen shekara prize giving day kasancewar a shekarar gabadaya ita ke daukar na daya, kuma tafi kowa zuwa makaranta akan lokaci da kasancewa cikin tsaftar jiki data kayan makaranta. Hakan yasa Sarham da kan sa kawowa Hauwa tasa kyautar ta musamman don kara mata karfin gwiwa inda ya dauki Sumayya a motar sa suka je Levintis suka yo mata sayayyar kayan kamun azumi rankatakaf. Kayan dadi na kwali dana gongoni iri-iri. Wannan ne karon Sumayyah na farko da zuwa gidan su Hauwa, tunda jimawa Bhaiyan ta Sarham ke bata labarin su, amma bai taba yarda ta biyo shi ba sai yau, yau din ma don ta taya shi sayayya ne don ta iya provision na kayan kwalama, ta kuma taya shi da daukar kayan zuwa cikin lungun. Suka yi sallama Hauwa na gindin famfo tana alwalah Inna na daga kitchen, Inna ta amsa musu don ta dau muryar Sarham tun daga madafi, amma Hauwa a cikin cikinta ta amsa, zaka ga dai yadda bakin ta ya motsa alamar ta amsa, Sumayya ta tsaya daga nesa ta saka ma Hauwa ido don jikin ta ya gama bata itace Maijiddan, Hauwa Kulun Badalar kofar Naisa da Yayanta yake yawan bata labari kullum, wadda
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31