Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,209 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

zafi, ko cikin watan azumin ramadana da kuma lokacin da rana ta take sosai, to kuwa tsakar gidanmu zai zame maka muhallin hutawa sabida inuwa da duhuwar bishiyoyin. Gidanmu ya kunshi dakunan kwana guda uku kacal, daya a gefe na Babane, biyu na kallon sa, wanda daya ya zama na Inna ne, dayan kuma dakina ne nikadai a kusa da shi. Sai madafinmu mai rufin kwano da akayi da langa-langa, sai bayan gida daga gefe na gargajiya. Duk shaanonin cikin gida na Innar Hauwa a karkashin bishiyun nan take yin su, kamar su daka, gyaran kayan miya, surfe, wankin kayanmu, kai har da yin kuli-kuli da man gyada, don sau tari Inna da kanta take yi wa kanta mankuli, don wani lokacin na sayarwa sai ta ce an yi kazanta mai yawa a cikin sa, haka ta kan yi duk wasu abubuwan da hannunta kan iya sarrafawa da kanta ne don amfanin ta na gida. Hatta markaden kayan miya ita take nika abunta da dutsen nika. Inna bata da ganda (kiwa) ko kadan, akwai kuzari da koshin lafiya irin na matan da, da kashinsu yayi kwari daga shan surfe da dakau da tukin tuwo, sakamakon hakan kasusuwansu suka yi karfi sosai, gashi bata wasa da shan magungunan gargajiya masu kara koshin lafiya da cire kananan cututtuka irin su shawara (jante) dasu basir. Girman tsakar gidan zai isa a gina wani dakin guda, ba tare da daya ya gogi sauran dakunan ba, amma mahaifina wato Malam Bilyaminu ya barwa iyalin sa filin su yi amfani da shi don hidimar gida ta yau da kullum da hutawar su, don ya fahimci yadda rayuwar mu tafi bada karfi a zaman tsakar gidan. Kowa ya san yadda babu wanda ya kai mutanen dake cikin gari da badalolin nan na jihar Kano jin dadin alfarmar dake tattare cikin zaman kwaryar birnin Kano, da kuma jin dadin rayuwar birni gabadayanta. Mutanen cikin Badala, na da rayuwa ta tsaro ga junan su, da hadin kai, da taimakekeniya a tsakani, don suna kaunar juna ne kamar jini guda suka fito, ga kula da hakkin makwabtaka. A irin wadannan unguwannin na cikin Kano, a tsakanin 1970s, 1980s da 1990s zaki samu akwai saukin rayuwa na ban mamaki, misali arhar kayan masarufi dana abinci, makwabci baya iya cin abinci shi kadai a gidan sa ba tare da ya zuba an kaiwa makwabcin sa ba, ko ya fito da shi majalisa ayi ciyayya don inganta hakkin makwabtaka da zaman tare, da karfafa taimakon juna da zumuncin Allah. To a unguwarmu ma, wato Kofar Naisa, irin rayuwar da su Babanmu ke yi kenan kullum, shi da makwabcinsa Malam Isa, kullum bayan sallahr ishaI kowa zai fito da abincin gidan sa su shimfida katuwar tabarmar kaba a kofar gidan Malam Bilyaminu, su sallaci magriba da isha tare, sannan su zauna zaman cin abincin a kwano guda, da hannayen su dana kawo musu ruwa suka wanke. Akwai wadatar shaguna na kayan masarufi da abubuwan bukatar yau da kullum a kowanne lungu da kowanne kwana na unguwannin Badala, babu abinda baa sayarwa. Iyaye na dorawa yaran su talla ba tare da fargabar wani abu ba, akwai abincin sayarwa iri-iri kuma mai arha mai tsabta da a ke yi a gidaje, ga rijiyoyin burtsatse a koina da rijiyoyin amfani a cikin gidaje, don haka babu batun wahalar ruwa a lokacin, kai duk iya talaucin ka zaka rayu ne cikin jin dadi ba tare da ka sayi ruwan amfani ba a unguwannin cikin Badala. A hakikanin gaskiya sai kana zaune a irin gidajen nan namu dake cikin Kofofi da Badalolin Kano, shine kadai kake samun duka wadannan alfarmomin masu tarin yawa, kuma shine zai sa a kira ka da cikakken Ba-Kano, ko ka kira kanka da Bakano, ba dan wajen gari ba ko bakon haure a Kano. **** **** **** KANAWAN DABO A lummar Kano su akewa kirari da laqabi da KANAWAN DABO. Ni Hauwa-Kulu ina alfahari da kasancewata (yar asalin cikin BADALAr Kano), don haka ne na dauko muku labari na tun daga tushe, wato na fara da baku shimfidar labarina daga inda na taso, kuma inda aka haifeni, wato cikin kwaryar BADALA. Garin Kano gari ne da ake ma kirari da Ta-Dabo Tumbin Giwa (Yaro ko da me ka zo an fi ka). Mun samo wannan lakabin ne daga masarautar Kano (Dabon Kano) ta Sarki Abdullahi Bayero, Kano garin Sarki Ado, Kano mai Mata mai Mota, mai Ganuwoyi da Badaloli da wasu irin kofofi wuri-wuri lungu-lungu na tarihi, suna nan birjik bila adadin zagaye damu. A takaice tarihin birnin Kano tarihi ne mai dogon zango kuma mai zaman kansa, wanda in aka ce zaa bada shi saidai a dauko shi tun daga tushe, wato tun daga lokacin zuwan Habe, har zuwa shigowar Turawan mulkin mallaka, da rayuwar Mai-Tatsine a Kano, data sarakunan Kano da suka gabata. Don haka ba zai takaitu a shafi guda na gabatarwar/shimfidar littafi ba, sai dai I can boldly say; Kano ta zarta kowacce jiha a arewa kyakkyawan tarihi na sarauta, da ilmin addini dana boko da rike kasuwanci da muhimmanci. Abinda kowa ya sani ne Ba-kanon mutum bai yarda da zaman banza ko zaman kashe wando ba. Haka kuma bai yarda da zama cikin jahilci ba komai yawan shekarunsa; wato dai Gemu baya hana Ba-Kano neman ilmi. Saboda zaka ga daga yara har manya a Kano kowa dalibi ne, matan aure ma a wancan zamanin duka da suna dakin miji dalibai ne a gidan auren su, da zarar an yi sallahr isha, zaka ga suna firfitowa daga gidajen su cikin lullubi da shigar mutunci don tafiya makarantar dare ta matan aure, haka da safe akwai masu halartar makarantun manya (adult education schools) irin su Gidan Galadima, ko makarantar Gidan Makama, don haka akasari a Kano maza da mata bakidaya kusan kowa yana da abin yinsa daga neman ilmi zuwa sanaar da ta karbe shi, ko kuma wadda ya gada daga iyayensa. Zauna gari banza ga Bakanon mutum mace ko namiji sai mu ce sai dai abinda bazaa rasa ba, don hatta maaikatan gwamnati baka raba su da kodago a kasuwar kantin Kwari, ko Bata (Sabon gari), ko kofar Wambai, kasuwar Singa, ko kasuwar Kurmi, manyan kasuwannin birnin Kano kenan. Mafi yawan jamaar Kanon kuma da kasuwancin kacokam suka dogara, basu damu da aikin gwamnati ba, koda sun dan yi karatun zamani kuwa, balle wadanda basu samu yin mai zurfi ba, kamar mahaifina, wanda akafi sani da suna “Malam Bilyaminu dan Kofar Naisa”. Sanaar Babana Malam Bilyaminu itace sayar da kayan yara na gwanjo a kasuwar kofar Wambai. Da wannan sanaa muke rayuwa kuma da ita ya dogara, sannan kuma ta rufa masa asiri ya rike iyalin sa daidai gwargwado da kulawa irin ta Bakanon mutum, mai zucciyar kula da iyali, wato Mallam mutum ne har mutum wanda ya san ciwon iyalinsa. Malam Bilyamin ya taba yin sakandire ya kuma yi aikin masinja a wata maaikata daga baya ya bari ya kama kasuwar gwanjo sadidan. Duk wanda ya san Malam Bilyaminu, (kafin a neme shi a rasa rana daya), ya san cewa mutum ne da ya dogara da sanaar sa ta gwanjo, ya kuma bata muhimmanci sosai, sannan kuma shi din mai kula da iyali ne fiyeda kima da duk abinda

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});