Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,207 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

mamaki in ka ji cewa kusan duk wannan gulmar tasa da zunden nasa da suke yi, wato shi sabon likitan nasu, yana sauka ne reras, kuma tiryan-tiryan a cikin kunnen sa kamar an kunna radio yana sauraren su. Bai san sanda ya ajiye biron hannun sa ba don ya kasa cigaba da rubutun, ba wai haushi yaji ba don sun aibata halittar sa, aah, kawai abin ya bashi tsoro, cin naman mutum haka a kan kunnen sa da tsakar rana babu ko shakka, ya fiddo ido warwaje ya kuma kara sakin kunnuwa yana sauraren su da alajabi da mamaki. Mata sun kware da gulma ya sani, amma ta wadannan ta bashi mamaki kasancewar su Nosis ne dake karkashin sa. Shima ya yarda kamar yadda mahaifiyar sa ke yawan fada wato shi “SARHAM” mutum ne mai karfin JI. Wato jin sa yana da karfi, kamar yadda ganin sa yake da karfi yadda baa zato. Kusan komai na halittar sa ma mai karfi ne Ubangiji ya yi masa, idanun sa basa bukatar madubin kara karfin gani (medicated glass) da yawancin likitoci ke amfani da shi. Sarham hatta takun tafiyar sa wato (gait) din sa shima mai karfin gaske ne, gab-gab-gab… haka zaka ji takunsa in ya dumfaro ko ya durkako inda kake. Kafin ya iso sautin takunsa zai gaya maka isowar sa. Baban sa kan ce, shi din, wato Sarham, “DAN BAIWA NE KUMA NA MUSAMMAN A CIKIN DUKA YAYAN SA. Komai nisan zance in dai yana gefe aka yi shi, to kuwa tabbas Sarham zai jiyo shi tsaf. Wannan wata baiwa ce da Ubangiji ya yi masa da ba kowa yake yiwa ba, wadda a kullum yake gode masa a kanta, wato baiwar kyakkyawan ji da gamsashshen gani, da suka banbanta dana sauran mutane da yawa, shiyasa a kullum kunnuwan sa suke zuko masa abinda baa zaci ya ji ba. Ga shi dai da gaske siriri din ne shi, kuma dogon mutum a halitta, kamar dai yadda suka gulmanta, shima ya san hakan, don har wasu na yawan fadin wai yana dieting ne saboda sirantar sa mai yawa ce a matsayin sa na namiji, amma kuma a zahiri kakkarfa ne ta cikin kasusuwansa, zaka gane hakan ko daga fadin kirjin sa da kaurin kwanjin sa, wanda ke nuna duk safiya yana motsa jikin shi da kyau da hanyoyin motsa jiki irin na bature, ko daga kaurin tsokar damatsan hannun sa. Kallo daya zaka yi wa Dr. Sarham ka fahimci yana matukar kula da lafiyar sa kwarai da gaske, ta hanyar kula da abinda yake ci, da motsa jini (exercise) bada wasa ba a duk safiyar Ubangiji. Shi yasa yake dan shafal da shi mai dogon hanci. Sannan tsayin sa bai wuce kima ba kamar yadda Nosis dinsa suka kintata shi a gulmar tasu, kuma kaurin jikin sa ya wuce ace masa kamar na karan-raken takanda, kai shi bai taba jin wani ya kushe halittar sa ba banda wadannan magulmatan matan, iyakaci ana cewa yana ‘dieting’ baya cin abinci saboda kwalisa, amma shima ya san shi dogon ne saidai ba kamar karan-rake kamar yadda yaji suna cin naman sa ba. Don haka ba tantama in aka yi laakari da kalaman bakinsu, da bayanin da mai dan hankalin cikin nasu tayi a kan karatun sa, zaa fahimci tabbas sun yi masa farin sani ba kirkirowa suka yi suka fada ba, har da abinda ya bashi mamaki cikin zunden nasu, wai a Baban sa Farfesa ne na tsangayar ido, kasancewar bai dade da zuwa Murtala ba, kuma shi dai ya san bai taba abota da kowa a asibitin nan ba, balle su maaikatan jinya mata wadanda a karkashin sa suke. Sai yayi dan murmushi kawai wanda ya motsa gefen kuncin sa na dama, ya cigaba da rubuce-rubucen da yake yi a cikin wani fayal na mara lafiyar da ya kammala dubawa ya fita, yace a ran sa. A zauna a kafa tebur saboda kai, ana rage maka zunubi haka ai ka isa ne, wanda bai isa ba ko kallon sa ba mai tada kai yayi. Yana cigaba da rubutu yana murmushi cikin mamakin gulma ta rashin aikin yi irin na mata musamman maaikatan jinya. Dr. Sarham Abbas Shanono kenan. Siririn wankan tarwadan matashin likitan da bai fi ace a bana ya gama makarantar sakandire ba, sabida duka-duka bai fi shekaru ashirin da takwas ba. Hayaniyar Malaman jinyar sa, da ta dattijuwa Innar Hauwa data dage bazata tafi ba sai yar ta Hauwau ta ga likita, koda kuwa dukan ta zasu yi karewar rashin kunya, tace ban haife ku ba? ta kuma ce ai asibitin ba nasu bane na gwabnati ne, don haka basu isa ba da zasu hana ta ganin likita, inji dattijuwar, don sun kure hakurin ta, wannan hayaniyar ta hana shi fuskantar rubutun ma da yake yi yadda ya kamata. Gashi kuma a kofar ofishin sa ake ta wannan taqaddamar. Su Nosis din sun dage da rashin mutuncin tunda ta bari sai da ido ya rube zata zo asibiti, to ta je ta nemi sandar yi wa yar ta jagora zuwa bara. Amma bazata batawa likita lokaci ba, a lokacin da ba abunda zai iya tabukawa wadannan idanun da hakiya ta gama canyewa murus. Innar Hauwa har da kukan ta, don taga alamar fada ba zai bi da su ba, tana rokon su da muryar ban tausayi su bar yar ta ta gan shi kada ta makance, ta yarda ta yi laifi amma a taimaka musu su ga likita don Allah, ta tuba. Kuskure ne ta riga ta yi. Nan gaba zata kiyaye. Amma maaikaciyar jinyar nan ko a jikin ta, ta dora kafa daya kan daya akan kujera tana karkadawa ta hana su shiga ta yi rantsuwa da Jesus din ta, ba zata bari su batawa likita lokaci a kan idonnan da sun riga sun kashe shi a banza ba. Me ke faruwa haka? Hayaniyar me kuke yi mata haka? Ke Maria, meye haka kike yi? Wannan ya dace da maaikacin jinya? Sister Saratu wannan matar bata girme ku ba?” Dakusassar muryar DR. SARHAM, irin ta mai fama da sabuwar mura, ta karade wurin, yana maganar yana furzar da dan tari, don sosai yake fama da mura daga jiya zuwa yau da ya dan sha ruwan sanyi, jikin sa baya son sanyi ko kadan. Muryar tasa ta dira a kunnen su da sigar tambaya daga inda yake tsaye a jikin kofar ofishin sa, hannayen sa duka biyu zube cikin aljihun bakar Jacket din sa, yana dan yamutsa fuska cikin gajiya da alamun jin yunwa, don tun safe yake aikin duba marassa lafiya har zuwa yanzu da agogo ya buga karfe biyun rana, wato lokacin cin abincin ranar sa kenan da zuwa yin sallahr azuhur, lokacin tafiyar sa gida yayi kenan. Don haka ya fito ne don tafiya gida. Yana sanye da bakaken ‘suit’ da ya zanzare kugun sa a cikin su, ya dora bakar jacket a kan su, wadda ta sauko har zuwa gwiwar sa, ta bada suurar cikakken dan gayun likita kuma dan kwalisa dashi na wancan zamanin, masu yawan yin zanzaro da belt. Bafullatanin Shanono mai kakkaifar murya, amma a halin yanzu ta dushe, ta dakushe da alama yana fama da ‘Catarrh’. Yanayinsa na Kanawan usli ne, amma yanayin

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});