Chapter 20
Chapter 20
Jikin ta nata bari ta bude kofar motar ta fita daga gaban motar, hawaye ya tsirgo mata, zata cigaba da bashi hakuri ya fizgi motar sa ya bar harabar gidan su. Sumayya ta dade tsaye a wurin, tana nadamar shegen surutun ta, da bata iya gani tayi biris, daga karshe ta share hawayenta ta shiga gida. Yinin ranar zungur, Sumayyah ta kasa sukuni idan ta tuna Bhaiya na fushi da ita, Aunty Surayya na tambayar ta me aka yi mata take kulubi da hade rai? Sai ta ce a fusace ina ruwanki dani? Ko ina shiga harkar ki? Mama tace ke ko! Ina laifin Yayan da ya damu da kai? Nifa rashin kunyar ki ce take hada ni da ke Sumayyah ta tashi fuuu! Tayi dakinta ta bar musu falon. Surayyah na fadin kyaleta Mama ta yi da yar halak. Shikuma tunda ya sauketa asibitin Murtala ya koma. Ya shige ofishin sa ya kulle kan sa a ciki. Maganar da Sumayyah tayi kuskuren furtawa ta tuna masa da shekaru biyar a baya, abinda ya dade da mantawa; ta tuna masa ‘first love affair din sa wato MADINAH ATTAHIRU (MADINAH SORON DINKI), yar ajinsu, wadda bai sha da dadi a hannun ta ba dama iyayen ta da sunan soyayya, shiyasa duk inda aka ambaci yana son mace, sai ran sa ya kai makura wajen baci. Ya so Madinah kamar rai, irin son da ake kira (love at first sight) tun bai gama sanin ciwon kan sa ba, amma Baban ta ya wulakanta shi, don a cewar sa nawa yake a shekaru da matsayi? Sune samarinnan masu hurewa yaran mutane kunne su hana su karatu, bai isa auren diyar sa ba. Sannan Uban sa ma bai isa ba, tunda ba wani bane banda malamin makaranta, ina shi ina auren diyar sa? A lokacin ko part three na karatun sa bai hada ba. Soyayya ta rufe musu ido, soyayya ce irin ta tashen balaga daga shi har Madinan, sun so juna shi da Madinah kamar daya bai iya rayuwa ba tareda dan uwansa ba, sun yi alkawarin aure da zarar sun kammala MBBS sabuda yadda suka zaku ga son mallakar juna, amma Baban ta sai ya canza mata makaranta ma, duk don ya raba su, ya nesanta Madinah daga gareshi kwatakwata, don yace ya fahimci zai hana yar sa karatun da ya kai ta ta yi a Jamiar Sarki Abdul Azeez dake Jeddah ne kawai, shine dalilin da a karshe ma ya dauke yar sa ya maida ita Jamiar Yamboa dake kusa da Madinatul Munawwara, inda acan ne Madinah ta samu ta kammala nata karatun, shikuma ya kammala a King Abdul Aziz University ya dawo kasar sa ta haihuwa, daga lokkacin basu kara haduwa ba shi da Madina ko a hanya ko a waya ko a mafarki. Baya ko son tuna wata kalma wai ita soyayya saboda abinda Baban Madinah yayi masa, shi ya san tsakani da Allah ya so Madinah ya kuma yi niyyar auren ta da zarar sun kammala karatun matakin farko na koyon likitanci, itama kuma sai ta baiwa mahaifin ta goyon baya dari bisa dari, lokacin da ya maidata Yamboa sai bata kara nemansa ba koda kuwa a email, ko a telephone, ko ta wasika da ake aikawa ta post office a lokacin. **** ***** ***** HAUWA-KULU Kusan shakuwar tafi yawa tsakanin Inna da Sarham maimakon Sarham da Hauwa, kasancewar Hauwa bata da magana kuma taki sabawa da Sarham har gobe, duk kuwa da yadda yake kyautata musu, kuma yake jan ta da wasa lokaci-lokaci, iyakaci in ta ji ya zo ta gaida shi, ta shige daki ta bar su, in ya mata tambaya akan karatu ta bashi amsa a gajarce, kuma in an bata sakamakon ta bata kasa a guiwa wajen nuna masa da zarar ya zo gidan. Don ta yarda Dr. Sarham shine ginshikin karatun nata. Kuma ta kwana da sanin taimakon da yake yi musu mai dimbin yawa ne, da yafi karfin a gode masa, don duk da Inna ta cigaba da sanaar ta ta sayar da wake da shinkafa duk wata hidima ta karatun Hauwa shi yake yin ta kamar biyan Salele albashin kaita makaranta da daukota, da basu kudin hawa hayis zuwa da dawowa, sayen littatafai da kananan abubuwan da makaranta ke bukata kasancewar special school makaranta ce ta gwamnati domin yara masu bukata ta musamman yasa babu bukatar biyan kudin makaranta. Daga baya kuma Sarham baya zuwa gidan Inna sosai saboda ayyuka da suka tarar masa amma duk weekend baya fasa lekowa. Ya zama dan Inna, Inna ta zama uwar sa, ya zama dan gidan Bilyaminu kofar Naisa, don ganin sa take ya maye mata gurbin Zulkifilu. A yanzu hatta a weekend dinma Dr. Sarham baya samun zuwa hira wajen Inna kamar da, domin yana shirye-shiryen komawar sa Jiddah, bayan kwashe shekaru biyu yana aikin gwamnati, tun akan abinda ya faru da Hauwa yasa a ran sa zai koma zurfafa karatun sa, domin ya ki yardarwa kansa har zuwa yanzu cewa ba rashin kwarewar sa bane ya janyo wa Hauwa’u cataract blindness, yasa a ran sa yana bukatar kara zurfafa ilmin sa zuwa mataki na gaba. Sai ya ga abinda ya turewa buzu nadi daga ilmin likitancin ido, akan dai specialization din sa na ophthalmology a shirye yake har ya tsufa in dai da rai, bazai gushe ba kuma bazai gaji ba yana karawa kansa kwasa-kwasai na fadada ilmin sa da zurfafa shi, don zama kwararren ophthalmic surgeon din da zai zamowa kasar sa abin alfahari watarana da fiddawa kansa ‘inferiority complex’ din da yake fama da shi tun akan aikin da yayiwa Hauwa-Kulu. Duk da cdewa bayan nan yayi wasu ayyukan fidar da yawa kuma an yi nasara. Abba Prof. kuma ya lamunce masa ya koma din, don a cewar sa gara ya gama karatun duk da zai yi cikin kuruciyar sa, kamar yadda shima ya samu yayi nasa yake cin moriyar sat un da jimawa. **** **** **** Jikin kafatanin mutanen gidan yau a matukar sanyaye yake, wannan ya faru ne kasancewar gobe da asubah ake saka ran in sha Allah, Bhaiya (Dr. Sarham Shanono), zai tashi zuwa kasar da ya baro a can baya a karo na biyu wato kasar Saudi-Arabia don zurfafa karatun sa. Sabo, wani abu ne mai matukar muhimmanci ga rayuwar iyali, musamman irin wannan wadanda suka gina tubalin rayuwar su akan tsari na (nuclear family) wanda akasari yan boko ke yi, wato rayuwa ta daga su sai yayan su, kamar yadda yake a gidan Prof. Abbas Shanono. Don haka ficewar daya daga cikin su rana daya zai haifar da wawakeken gibi ne a gidan, musamman shi Sarham da yake jigon gidansu, sannan ‘personality’ din shi ya banbanta dana kowa cikin gidan, shi mutum ne na kowa! Likita mai farin jini da sakewa da mutane wanda kowa nasa ne, mai faram-faram da hidima da kowa nasa, shi kadai ne Da namiji a cikin su, in ka cire mahaifin nasu. Don haka shi din, tamkar wani bango ne a gidan su abin jingina. Gabakidayan su jamaar gidan, in ka dubesu yau zaka fahimci tsantsar damuwar da suke ciki, kowa fuska ba annuri, banda Abba Prof. da ke shi babba ne, ya boye tasa damuwar, maimakon hakan, sai ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31