Chapter 29
Chapter 29
kan a bar zancen nan daga yau, anan inda zamu ajiye shi. Jamilu na yarda kai mutumin kirki ne, zuciyarka ba irin ta mahaifinka bace, kai daya ne cikin dubu a gidanku, kuma kai mai nufin Hauwa da alheri da soyayya ne, duk da lalurarta ka amince ta zamo maka uwar iyali a haka, babu wata kauna da taimako da soyayya da wani dan adam zai nuna ma Hauwa a duniya da ya wuce wannan a doron kasa. Hakika mun yaba maka, mun kuma gode maka, domin ka so kayi jihadi ne kuma Allah zai baka ladan niyya. Amma komai zamuyi sai da yardar iyaye zai yi albarka Jamilu ka sani, ina kuma tabbatar maka ba zaka taba samun albarkar mahaifin ka ba in kana tare da Hauwa-Kulu”. Jamilu Zakari, yasa hankaci yana tsane tulin hawayen idon sa, ya fahimci Inna sosai, yau kam ya fahimci bata kinsa da Hauwa kamar yadda yake zato a baya, ya fahimci abinda ada ya kasa fahimta, wato su iyayen Hauwa da nasa mahaifin, bazasu taba zama a inuwa guda ba, a sanyaye Jamilu yace. “Inna na ji ki, na kuma fahimce ki, amma ku sani daga ke har Babana; Hauwa yar uwa ta ce ta jini, baa raba hanta da jini, ni kadai na rage mata matsayin Uba kuma dan uwa a yanzu. Maganar aure tsakanin mu na bar ta har abada! Amma ni Jamilu daga yau nine Yayan HAUWA-KULU na halali kuma Uban ta na jini, daga nan har karshen rayuwar ta, ko kuma ranar da mahaifin ta ya dawo na damka masa yar sa a hannunsa. Kiyi min alfarmar cigaba da zumunci da ita, da kula da ita, tunda na hakura da maganar aurenta, ba don komai ba sai don samar muku kwanciyar hankali amma ba don na daina sonta ba, don ni da kaina na san Babana hatsabibi ne”. Inna ta rasa kuma me zata ce. Ta rasa Jamilu kowanne irin mutum ne da baya gane abinda zaa shekara ana ganar da shi. Da zai tafi ya kawo kudi masu yawa ya baiwa Inna, shi kan sa baisan adadin su ba, yace su yi amfani da su kafin Allah yayi masa dawowa daga tafiyar da ta same shi zuwa Delta. Jamilu ya tafi Delta da kwana biyu aka yi sallama da Inna a zaure, maza ne magidanta su uku, nan suka gaya mata yaya har yanzu bata tashi daga gidan ba? Inna ta ce wane gidan? Sai suka hau mata bayanin wannan data ke ciki yanzu, saboda mai gidan yana so zai rushe shi, zai mayar da wajen kamfanin buga ruwan leda, ko ba a gaya mata an bata notice din tashi na kwana uku ba? Inna tayi musu kallon banza ta ce ban gane ba? Anya nan gidan kuke nema? Nan dai gidan Malam Bilyaminu Kofar Na’isa ne, wanda ya gada daga tsohon sa. Ya gada ko suka gada?. Mutumin ya gyara mata zance cikin gatse. Kafin ta bashi amsa yace to ai shi Zakari ya riga ya sayar mai da gidan a gaban wadannan shaidun”, ya nuna mutanen da suke tare, wadan da yan unguwar ne abokan Zakari, sannan ya fiddo ainahin takardun gidan ya nuna mata, wadanda Innar bata san ina aka je aka samo su ba. Suka ce lallai suna son gidan su zuwa gobe, don zaa zo a rushe shi goben, da sauran gidajen da aka saya na makwabtan su. Da fadin haka Inna ta rasa abinda zata yi, sai kawai ta saka kuka tana cewa su koma su gaya wa Zakari ta sallami dan sa Jamilu in dai a kan sa ne zai mata wannan tozarcin. Ko sauraron ta basu yi ba suka tafi. Har washegari Inna ta kasa gayawa Hauwa maganar nan, tana ta fama da ita a kirjin ta dake faman zabalbala, zuwa yamma kuwa wasu tsagerun samari suka shigo suka soma fatali da kayan Inna suna jefo komai waje. Suka ce suma saka su aka yi. Ga masu rusau nan zuwa, in sun ki fita ta arziki zaa rushe har da su suna ciki. Yadda ake jifa da kayan Inna a unguwar ya janyo hankalin daukacin jamaar unguwa, suka taru don neman baasi, amma ba wani bayani sai na maigidan ya sayar da shi, ita kuma Inna an ce ta fita ta laluma taki fita. Inna na kuka, Hauwa kuwa don taurin da zuciyar ta tayi idon ta ko kyallin hawaye babu, amma ya kada ya yi jajir, jakar makarantar ta lalubo da gilashin ta da Sarham yayi mata ta sakaya idanunta, ta goya jakar ta mai dauke da komai nata na makaranta ta kama hannun Inna, kamar itace mai idon ba Inna ba, Hauwa tace. Kada ki damu Inna muje, Baba Zakari ya kara arziki da gidannan don Allah, in don ni ko a tashar mota da karkashin gada zan iya kwana, in dai idan gari ya waye zan je makaranta, ba kuma zaki bar ni in yi “bara” don bana gani ba. Inna ta kasa magana sai kuka, a haka ta yafa mayafin ta ta kulle kayan ta da zata iya dauka a bakko, ta kama hannun Hauwa suka fice daga gidan. Gidan su mai tsohon tarihi! Gidan da tayi dukkan rayuwarta da yaya da mijinta, sama da shekaru talatin. Gidan da ba abinda take so a rayuwarta sama da shi. Ga Hauwa kuwa wannan gidan na bayan Badala shine farin cikin ta, da shi kadai take tuna ta rayu tare da mahaifinta. Ko minti goma basu yi da fita ba, masu rusau din suka iso, cikin dan lokaci suka hau rushe gidan Malam Bilyaminu. Kafin dare sai kasar gidan da duwarwatsu, Dabbobin Inna kam tuni sun yo waje da suka ji su a bude babu turke. Sai Malam Isa da ya dawo kasuwa ya ga dabbobin a kofar gidansa aka kuma gaya masa abinda ke faruwa wato Zakari ya kwace gidan ya sayar su kuma wadanda suka saya sun rusa, Hauwa da Inna suna tsaye a kofar gidan sa ake ta rushe gidansu akan idon su, sai ya tattara dabbobin ya kora su wani kango na gidan sa ya rufe su. Jamaar unguwa suka yi dafifi suka hana Inna barin unguwar suka ce tunda dare yayi ta shiga gidan Malam Isa zuwa gobe, dattijan unguwa sun ce ta zauna gobe a shigar da karar Zakari a kotu. Don mai unguwa ya dade da rasuwa. Saidai cikin daren, a gidan Malam Isa, inda aka baiwa su Inna mafaka, Inna ta canza shawara, ba ita ba shiga kotu a rayuwarta saboda abun duniya, a wurin mutanen da shiga kotu na nufin karshen tozarci ga mutuncin su kenan, meye abun duniya wanda duka mutuwa zaayi a bar shi a inda yake? A gidan Malam Isa suka kwana dakin matar sa Mai kosai, da asubahi ta kama hannun Hauwa ta dora kayan su a kanta, suka faki idon kowa suka bar gidan Malam Isa. A lokacin shi yana masallaci sallahr asubahi, matar sa kuma tana daka tana jan rago (munshari). Kai tsaye Inna da Hauwa suka naushi hanyar fita daga BADALAR Kofar Naisa, ba don sun san inda suke nausa kafafun su ba, ko suna da wurin zuwa, burin Inna kawai su yi nisa da kusa da duk wata Badala ko Kofa
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31