Chapter 26
Chapter 26
na kirki ne sai bai gudu ba, ya taimaka aka saka Hauwa a motarsa, tareda wani dattijo da Salele da ya ce ai Yayar sa ce, suka nufi asibiti da ita jini nata disa a motar, amma mai motar nan bai damu ba ta ran Hauwa yake, yana rokon Allah yasa abun ya zo da sauki kada diyya ta hau kansa. Hauwa bata san inda kanta yake ba har suka shiga babban asibiti. Asibitin Malam suka kai Hauwa, a ka karbe ta a imajensi likitoci uku suka rufu akan ta suna kokarin ceto ranta. Sai bayan an samu an yi treating raunukan da ta ji, an kuma daure karayar da ta samu a hannu sannan aka basu daki kwanciya. Wanda ya kade ta duk shi ya biya komai, kuma ya tsaya har aka kai su dakin kwanciya din na mata inda aka basu gado. A lokacin ne ma ya samu damar da ya kalli Hauwa tana barci, duk da ta kara girma sosai, ta zama budurwa sai yaga kamar ya santa. Ya tambayi Salele gidan su, don aje azo da iyayen ta, Salele ya ce zai je shi kadai ya zo da Innar ta. Don haka saurayin ya ja kujera gaban gadon Hauwa ya zauna bayan fitar Salele, ya dau wata jarida a kan lokar gadon ta asibitin yana dubawa yana satar kallon Hauwa yana fadi a ransa yau tsautsayi ne ya fito da shi daga wajen aikinsa ba tare da lokacin tashin sa yayi ba, tsautsayi da baya wuce ranar sa, banda haka shi baya wani fita cin abinci har cikin bankin a ke kai musu su biya, daga yaje ya ci abincin rana a restaurant ya koma office zuwa lokacin tashi tsautsayin nan ya ritsa da shi? Ya sake kai duban sa ga Hauwa a karo na sau ba adadi, sosai take masa kama da wata fuska da ya jima da sani, amma ya kasa tuna inda ya san fuskar ba. Har saida Inna tayi sallama a gigice ta fado dakin asibitin kamar an turo ta, Salele ya biyo ta a baya da buta da bokiti da tabarma da bargo, nan ne mutumin ya gane ta sarai. A tsorace ya mike tsaye, ita kuwa Inna bata ma lura da shi ba kan Hauwa tayi tana salati tana godewa Ubangiji. Bayan ta dan nutsu ne Jamilu ya matsa gaban ta ya tsugunna, ya sadda kan sa kasa cikin kaduwa da mamaki da tsoron kada Inna tace da gayya ya kade Hauwa, yace Inna Safiya kiyi hakuri, ni na kade ta ban sani ba, ashe Hauwa-Kulu ce ma, kanwata. Wallahi ina cikin tafiya kawai na ganta a gabana a tsakiyar titi, nayi kokari in kauce ta sake dawowa daya barin da ba yadda zan iya kauce mata. Inna ta kai duban ta ga saurayin, nan da nan ta gane shi duk da girma da cika idon da yayi, Jamilu ne dan wajen Zakari, Inna ta ce. Jamilu dan wajen Rumanatu? Yace ni ne Inna Inna tayi kwafa ta ce to babu komai, kana iya tafiya, mun gode. Jamilu ya ji babu dadi a ransa, yace Inna Safiya wallahi tsautsayi ne, ba inda zani sai taji sauki, zan kasance tare da ku har Allah ya bata lafiya. Inna bata sake komawa ta kansa ba, ta maida hankali kan gyarawa Hauwa kwanciya, har ya karaci durkuson sa ya tashi, ya tafi cikin damuwa. Bayan fitarsa Inna ta tambayi Salele yadda aka yi ma ya rabu da Hauwa har ta hau titi bisa ita kadai, cikin kokarin boye bacin ran ta, Salele duk rashin gaskiya ya bayyana a fuskar sa ya ce Inna daga nace ta tsaya in je ni tsallake in dawo Inna tace ka dai fadi gaskiya, kai dai wallahi a kan kalle-kalle ko bakauye nan ya ganka ya barka. Allah ya kiyaye gaba”. Can kuma tace. “Oh ni Safiya, Hauwa-Kulu harda karaya? Idon ta ya kawo ruwa, tasa habar zaninta ta share tana sake gyarawa Hauwa kwanciya, an sakale hannun da aka gyara a jikin karfen gadon. Ba jimawa da fitarsa Jamilu ya sake dawowa niki-niki da ledoji a hannayensa, yayi sallama akan su, dakin irin dogon dakin nan ne na kwantar da marasa lafiya mata zallah, suna daga gadon tsakiya da wasu a gefeda gefen su, Inna ta juya ta dube shi ta amsa sallamar sa, fuska kadaran-kadahan ta ce wani abu ka manta ne kuma? Ya ce aah Inna, ai na dinga zuwa kenan har sai an sallame ku, in sha Allah. Ya ajiye mata ledojin da ya shigo dasu a gaban ta cikin matsanancin ladabi, sai Inna ta rasa me zata ce, yaushe yayan Zakari suke da hankali balle su yi halin da yake yi a gabanta yanzu? Koda yake ko dama can shi daban yake a cikin su ta san wannan, saboda uwarsa ta masa tarbiyya daidai gwargwado, bayan Zakari ya saketa da shi ta tafi tayi aure a wani gidan, ba laifi yana gaida mutane duk inda ya gan su ba kamar kannen sa ba da sau dubu zasu wuce ta ko kallo bata ishe su ba. In zata iya tunawa rabon ta da Zakari da wani da ya shafe shi tun batan Malam Bilyaminu, shekaru hudu baya da ta je neman sa yayi mata korar kare. Wani cikin su shi ko yayan sa bai kara neman su ba, yau kuma sai ga Jamilu ya kade Hauwa. Inna ta nisa, ta kasa ce masa ya kwashe tsiyar sa, don sosai taga damuwa a tare da shi na irin karbar da take masa. Haka suka zauna shi da ita zugum-zugum, ba mai iya ce da kowa uffan, daga baya yayi mata sallama ya tafi. Yace sai gobe in sha Allah kafin ya tafi wajen aiki zai leko ya ga jikin Kulun. Inna tayi masa godiya, amma sai ta ce “don Allah ba sai ka dawo ba Jamilu, taimakon da kayi mata ma an gode sosai, madallah. Allah yayi albarka. Jamilu bai ce komai ba ya juya ya fita don ya san tabbas Inna ta kullace su duka ahalin gidansu daga su har mahaifin su, don ma dai tana da kai zuciya nesa. To bayan fitar sa kuma ta samu kanta da bude ledojin da ya aje musu, ta farko kayan shayi ne a ciki, da katon biredi (Laziz) sabon gashi, sai kayan marmari shake a daya ledar harda Tuffa da Inabi, daya ledar kuma gasashshen naman rago ne mai zafi sosai a ciki. A lokacin Hauwa ta farka tun bayan kawo ta asibitin da kyar ta iya ta dan motsa, sai ta ji ta kamar a daddaure, koina na jikin ta ciwo, bata san me ya faru da ita ba, ta kai hannun ta da baa daure ba kan goshin ta tace wash! Inna tace sannu Kulu kin ji, tsautsayi ne da baya wuce ranar sa, mota ta buge ki, Allah dai ya dada kiyaye gaba. Nosis suka zo suka bata magungunan ta, suka ce a bata shayi mai zafi ta sha, kuma zata iya cin wani abu, Inna tace basu zo da ruwan zafi ba, sai suka bata aron karamar heater ta jona ta hada mata shayi mai kauri da kayan shayin da Jamilu ya kawo. Ta taimaka mata ta zauna a jikin filo tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31