Chapter 12
Chapter 12
Hauwa Bilyaminu zata makance a hannun sa. But this written destiny really touched and tormented his heart. Ace ka zama sanadin nakasar idanun wani dan adam kwata-kwata, duk da cewa dai aikin likita irin wannan (a mutu ko a rayu) ne, sannan ba zaa tuhume shi ba, tunda ya tafiyar da komai a kan kaidar aikin sa ne, amma IDO fa ake zance, wannan kwayar tsokar guda biyu mafi amfani da muhimmanci ga halittar dan adam, sannaan in har kana da zuciyar yan adamtaka a cikin kirjin ka da humanity a tare da kai, dole zuciyar ka ta tabu, da ganin yadda fuskar Innar Hauwa ta shiga tashin hankali a lokacin da Hauwa tace, bata ganin komai a gabanta sai duhu. Wanda tayi ta kokarin danne tashin hankalin data shiga din saboda shi. To shi tashi zuciyar ba tabuwa kawai ta yi ba da tausayin su da disappointment akan aikinsa, ta kekkece ne, sannan ta tsatstsage ta yayyage ta yagalgale (into pieces at the same time). Ta yadda a gaban Innar Hauwa duk dauriyar da yake yi sa sai da idonsa ya kada, kwalla ta cika idonnasa, a fakaice ya yi kokari maida kwallar, ta hanyar juya musu baya ya zuba dukkan hannayen shi cikin aljihu yana maida kwallar sa, bai san Innar ta gane halin da yake ciki ba. Hakan ya faru ne lokacin da ya ji Hauwa tana cewa. Shike nan yanzu Inna sunana Makauniya? Ba zan sake ganin fuskar ki data Baban mu ranar da ya dawo gare mu ba? Kema na daina ganin ki kenan daga yanzu?” Yana iya tuno kalaman Innar Hauwa gare shi, da ta ga yasa hankici yana tsane kwallar da yake ta hadidiyewa cikin idanun sa a wayance, yanzu kam tafi karfin sa, ta baiwa kanta yanci ta digo, a lokacin yana rubutu cikin fayil din Hauwa sai hawaye ya diga a kai, wannan ya faru a kan idon Innar Hauwa. Sai Innar Hauwa ta bagarar da tasirin maganganun Hauwa suka yi mata a ranta, ta maida kulawarta a kan shi inda ta dube shi cikin lallashi tace Haba likita? Kaida zaka bata karfin guiwa? Shi Dan adam ai baya tsallake kaddarar sa. Ita Hauwa-Kulu kaddarar ta kenan. Abin yi a yanzu gaba dayanmu shine mu yi mata fatan Allah yasa makanta ta zamo kaffara a gare ta. Idan makantar nan jarrabawarta ce ta dan wani lokaci Allah ya yaye mata ya bata ikon cinye wannan babbar jarrabawa, idan kuma ta har abada ce Allah yasa ta zamo silar shigarta aljannah. Nakasa ai ibadah ce ga wasu kebabbub bayin Allah!. Amma duk da tawakkali irin wannan wanda Innar Hauwa ta nuna, Dr. Sarham ji yake yana blaming kan sa, kamar rashin kwarewar sa ce ta saka Hauwa a wannan halin na rasa abinda yafi komai dadi ga rayuwar mutum, wato idanun ta. Zai fi yarda idan aka ce sakacin sa ne, laifin sa ne, rashin kwarewar sa ko iyawarsa ce. To ko dai gaskiyar mutane ne da suke cewa yayi kankanta da zama mai ceton rayuwar idanun alummah? Yaushe tasirin maganganun jahilan matan nan magulmata zai bar ransa ya sake ne? meyasa ma kunnen sa sarkin ji, ya zuko masa abinda ba alkhairi bane a gareshi kuma wanda zai dame shi? Don haka koda ya baro su a asibitin ya dawo gidan su a ranar, wato gidan mahaifin sa, da matsanancin duhun zuciya ya shigo, mahaifiyarsa kanta ta fahimci cikin matsananciyar damuwa Lelen Abba yake. Tun daga bakin kofa kanwar sa Sumayya ta soma tarar sa da zance yadda suka saba saboda shim aba laifi akwai hira musamman da kannen sa, Sumayya tana gaya masa ta yi (passing exams) din ta, kawai ya zo ya bata kyautar da yayi mata alkawari bata son a bata lokaci har kyautar tabi ruwa tunda shi yayi alkawari. Amma ga mamakin Sumayya yau Lelen na Abba ko kulata bai yi ba, yayi fuska kamar ba shi ba, don ko kallon ta bai tsaya ya yi ba, balle ya bata lokaci wajen taya ta murna yadda ya saba in taci na daya a kowanne zangon karatu, balle har ya ce su fita kingsway ta zabi ‘gift’ din da ya yi mata alkawarin. Kawai sai yasa kai ya wuce zuwa dakin sa abinsa, yana cewa a ransa baki da matsala, ko sannu da gida yau bai iya ya yi mata ba itada sauran jamaar gidan bakidaya. Sumayyah bata daddara ba, ta sake kwasar faranti data shake da abinci ta biyo shi da abincin rana har dakin sa. Da yake ta gan shi cikin damuwa sai tayi tunanin yi masa abincin da ta san ya fi so, wanda dole zai kula yayi godiya, wato tuwon alkama miyar kubewa busassa. Miyar ta ji busashshen kifin banda da cryfish, ga lafiyayyen farfesun kayan ciki ta hado masa da shi da yaji kayan kamshi da attarugu, komai zai ci sai ansa tarugu da tafarnuwa, sune abinda ke sawa yaci abinci sosai ta sani, duk ta jera a kan tray ta biyo shi da shi har daki. Sai ta samu kofar tasa ma a kulle da mukulli, wato ya kulle kan sa, don baya son kowa ya dame shi. Musamman ita Sumayya sarkin naci da zuba zance, ya san saita biyo shi, saboda da shi kadai take shiri ta kuma fi sabawa cikin gidan, bata iya zama idan ba kusa da shi ba. Wannan kulle kan sa da yayi a daki tun dawowar sa gida da hantsi har bayan laasar ya dami mahaifiyar sa Barr. Mai shariah Haj. Maimuna (Mama inji yaranta). Har bayan laasar suna zuba idon ganin fitowar sa shiru suke ji, ta tambayi Sumayyah ko ya ci abincin ranar data kai masa? Nan take gaya mata cikin tata damuwar, ai Mama ko bude dakin bai yi ya dauka ba, dazu na kara dubawa na ga abincin yana nan a bakin kofa inda na ajiye masa”. A lokacin Yayar Sumayyah mai bin Dr. Sarham a haihuwa wato Aunty Surayyah ta dawo gidan, daga gidan Kakar su Hajiya Kulu. Ba jimawa mahaifin su ma ya dawo daga cikin makaranta inda yake koyarwa wato Prof. Abbas Shanono, nan gidan ya idasa cika ya zama full-house yadda yake a kowanne yammaci in sun dawo daga sabgogin su. Prof. Abbas ya tadda su jigum jigum a falo wato dai damuwar Lelen Abba (Sarhamu) ta taba kowa. Don an yi bugun duniya bai bude ba, da Sumayyah ta dame shi da nacin rokon ya bude kofa ya dau abinci, a fusace yace mata in bata bar masa bakin kofar dakinsa ba zai fito ya yi kasa-kasa da ita a wurinnan. Yau ban ga Sarham a masallaci ba ko bai dawo bane? In ji Abba Prof. ya fada yana nazarin yayan nasa mata guda biyu da mahaifiyar su wadanda duk suke cikin damuwar abinda ke faruwa da babban Yaya. A kaidar Abba Prof. idan ya dawo gida daga cikin Jamia kullum, kasancewar suna zaune ne a cikin rukunin gidajen manyan malamai na sabuwar Jamiar Bayero, kafin ya shiga gida masallaci yake fara zarcewa wanda ke kofar gidan sa, mafi yawancin lokuta a can zai tadda Sarham ya riga shi isa, sabida baya wasa da bin jamI, kuma sautari ya kan riga shi dawowa, zasu hadu a can,
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31