Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Hauwa Kulu Book 1 Complete Hausa Novel 1,208 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

lokon su tana rike da Hannun Hauwau yana dauke da kunshin kayan su. Sarham yayi ta mamakin sanayyar jamaar unguwar da Innar Hauwa yadda duk inda suka bulla jamaar unguwar ke gaida Innar Hauwa cikin girmamawa suna kuma tambayar ta yaya Hauwa da ido? Inna sai ta ce sauki na wajen Allah tunda yanzu Hauwa ido babu! Kamar yaya ido babu? Anan kam saidai tayi murmushi ta sa kai ta wuce su tana mai cewa “da sauki dai”. Ta kasa bayani don kada ta karasa Sarham a blame. Sosai kowa ya kasa ganewa haka dai ake ta jajantawa ana wucewa har suka shiga gidan su. Dabbobin Inna duk sun bata gidan da kashin su da fitsarin su yayi daka-daka, kasancewar ta kwana biyu bata nan ba wanda ke sharewa, duk sun cakalkala gidan, ga ganyayyaki sun zubo a kaina irin busassun ganyen bishiyoyin su na darbejiya da umbrella duk gidan ya yi kaca-kaca. Inna ta shiga dakin ta ta dauko ma Sarham kujera yar tsugunno tana cewa cikin takaicin yadda ya tadda gidan nasu daka-daka, kayi hakuri Likita, gidan namu yayi datti, tumaki sun bata shi kwana biyu da bama nan, sun yi abunda suka ga dama a tsakar gidan nan. Ka ga nan shine gidan namu, ana cewa gidan gidan Malam Bilyaminu Kofar Naisa”, ko da nan gaba ka zo ka bata ko ka kasa ganewa, haka zaka ce, ko gidan su Hauwa-Kulu. Sarham yayi murmushi yana jinjina surutu irin na Inna, duk surutun sa ya samu Inna ta fi shi iyawa, don haka da alama tasu zata zo daya kamar Kakar sa Haj. Kulu yake jin maganganun nata, ya zauna a kujerar da Inna ta aje masa yana walainiya da kayatattun idanun sa a gidan, sosai yake shaawar rayuwa irin ta cikin Badala irin wannan, don suma da can a bayan Badalar suke ta kofar Gadon kaya, amma tun sanda aka bude sabuwar Jamiar Bayero aka maida mahaifin sa gidajen malamai na ‘New Site’, kasancewar a lokacin yana daya daga daidakun tsafaffin malamai masu matsayin Farfesa a tsangayar magani (medicine). A can baya kafin a gina ‘New Site’ din iyayensa suna zauna ne a unguwar Kofar Gadon Kaya. Suka sake sosai a tsakar gida suna cafkar hira shi da Inna, (they are all talkatives) kamar wasu yara. Hauwa na daga can cikin dakinta a kwance, kan siririyar katifar audugar ta, tana jin su da rabin hankalin ta, amma rabi baya tare da su sam. Ita kadai ta san me take (going through) wato me take fama da shi a zuciyar ta, wadda ke cike taf da rauni da karaya da rayuwa, idan ta shafa idanun ta taga duhu didim! Idan ta kyafta su taga babu komai a gabanta sai duhu! Shin wai shikenan haka zata dauwama har abada cikin duhun idanuwa bazata kara ganin fuskar kowa da komai ba, har kuwa fuskar Innar ta? Har kuma tata fuskar a mudubi idan ta kalla bazata gani ba? Ko kuwa rashin ganin nata na dan lokaci ne watarana zai dawo? Ko kuwa tafiyar idon kenan? Duka wadannan tambayoyin da take yiwa kanta bata da amsar ko daya. Allah shine masani, amma hakika tana cikin matsanancin tashin hankali da dimuwa da wannan jarrabawa, wanda sai wanda ya taba rasa wata gaba ko wani sashe na jikin sa ne kawai zai iya relating. Imanin ta yau ya karu akan mutane masu nakasar ido (visual impairment) da ta dade tana ganin su a hanya ko suna bara. Yau ta yarda makanta ba abu ne mai sauki ba. Tana jin yadda hira tayi dadi tsakanin Sarham da Inna, kamar su kam ba abinda ya dame su da abinda ya same ta. Sai labarin halin baban ta wato Malam Bilyaminu da Yayan ta Zulkifl Inna take bashi a sanda suke tare dasu, da irin rashin jin Zulkifilu a sanda yake yarintarsa, tace kullum sai yayo tsokana ya dauko mata Magana shi haka Allah yayi shi ba kamar Hauwa ba da ko naman jikin ta zaka yanka sai ta ga dama zata daga ido ta dube ka. Can ajima sai kaji Inna ta gangaro kanta ita Hauwan, tana gaya masa irin halin ta na kirki da yasa take tausaya mata wannan lalura data sameta yanzu, yadda Hauwa ke taimaka mata da ayyukan gida bata da kiwa (bata da ganda), ga son karatu kamar tsuntsun alhuda-huda. Inna ta ce cikin mutuwar jiki da yanke tsammani, babbar damuwar ta a yanzu da makancewar Hauwa-Kulun ta, ba makantar bane ba kai tsaye, ko kiranta makauniya da mutane zaa ke yi, damuwar tata shine; ta yaya Hauwa zata yi ta cigaba da karatu? Wannan magana da Inna ta yi, ba Hauwa kadai ta saka a tunani da damuwa ba har da shi kan sa Dr. Sarham. Kamar wani assignment na lissafi (mathematics) mai wuya yaji Innar Hauwa ta bashi shima. Wanda zai tafi gida dashi domin yayi solving ta hanyar tunani. Don haka koda suka yi sallama da Inna jikin sa duk a sanyaye yake shima, ya fito lokon ya shiga motar sa ya tayar, amma sai ya kasa tafiya, sai ya kifa kansa a kan sityarin motar na tsayin lokaci yana tunanin ta inda zai iya taimaka musu da rage musu. Ya shiga cikin tunanin ta wace hanya zai bi ya taimaki rayuwar wadannan bayin Allah da yarinyar su tilo, ta nakasa a hannun sa? Yo a hannun sa mana! Da yayi aikin nan da kula yadda ya dace da Hauwa bata makance ba (a tunanin sa). Iyaka tunanin sa bai ga da me zai iya taimaka musu ba banda a kan shaanin karatun Hauwa din, don haka ya yanke shawarar baiwa Abban sa labarin su, da neman shawarar sa da karin haske akan ilmin da bai sani ba wato special education. Kasancewar Abban sa mutum mai hangen nesa da yalwar ilmi a bangare daban-daban fiye da shi, ya san a nan ma bazai rasa sani ba. Shi da Abban sa (are more than father and Son, they are very close and best friends) na junan su tun yana karami. Haka kanwar sa Sumayyah ita ce babbar abokiyar sa a rayuwa, Sumayyah is nice and easy going sannan (talkative like her Bhaiya) yadda take kiran sa kenan, shiyasa tasu ta zo matukar daya, su yi hira suyi dariya kasancewar sa very jovial likita abokin kowa, ba kamar sakuwarsa ba wato Surayyah, wadda ta dauki rayuwar sababbin yan jamia (JJC) mai tsauri ta sanyawa kanta. Duk da kasancewar Sumayyah mai karancin shekaru to fa ya shaida ta fi Surayya hankali da hangen nesa, kai dai bar Surayya wajen iya ado, da iya daukar wanka da kuma son kyale-kyalen da zaa ce tafi kowa cikin tsararrakin ta aji. Halayen da ke hadata fada da Bhaiya din kenan a matsayin ta na sakuwarsa a haihuwa, kusan kullum sai an ji kansu, don shi ta rage wuni a gidan su sai gidan Hajiya Kulu kakar su. Dr. Sarham, in ka cire abokan karatun sa da har gobe in an hadu akan gaisa, bashi da wani shaqiqin aboki da zaa kira aminin sa, duk da surutun sa da sakin fuskar sa to fa ya san a inda yake yin su, baida abokai sam saboda training din da mahaifin sa yayi masa kenan na ya

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});