Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 8

Chapter 8

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,067 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ina ya tafi ? oho bakin shi da sallama cen kassan makoshi ya shigo parlourn MALIKAT HOUDA kamar aljana ta na zaune ita kadai cikin parlourn , ta na kallon waje guda a hankali ya karaso geffen ta ya zauna ya na fadin " me ki ke yi a nan ke daya ? " ba tare da ta kalle shi ba ta ce " nothing , kawai na kassa barci ne " " Da gaske , me ya faru ? tunanin me ki ke ? ko cikinki ke ciwo ? " a hankali ta girgiza mishi kai ta na dan karamin murmushi ta ce " uncle ne ya tsayar da ni , wai ya na son magana da kai " cikin rudu ya ce mata " ban gane ba ? " a hankali ta sauke nunfashi , ta lumshe idanunta kafin ta sake bude su , sun koma farare kal a hankali ta juyo ta kalle shi cikin a hankali ta bude baki ta ce " wai kai komai sai an kwatanta maka ne ? " ta fada da murya tak tak irin ta Malik HICHAM ba karamar razana Malik ya yi ba har sai da ya yi baya ya na zaro idanu ya na karanto kalmar shahada cikin zuciyar shi bushewa da dariya ta yi ta na fadin " wlh kai da momyn ka duk matsorata ne , dubi kamar ka ga wani aljani , ko da ya ke na mutu ashe dole ka ji tsoro , ba ni da isashen lokaci , kawai na zo na fada maka a kan ka yi hankali lokacin duel din ku , Aymane ba abun da ka ke tunani ba ne , ya ma wuce tunanin mutum , ba za ka iya kashe shi ba kai tsaye , dole ka fara kawo karshen sihirin shi , Idan ba haka ba ba zai mutu ba , ni kai na ban san inda ya boye karfin sihirin shi ba , da na je na kawo karshen shi , zabi guda gare ka , da ka samu dama ka cire mishi kai kawai ta haka ne kawai zai mutu idan ba haka ba tashin hankali da za ka gani da ga baya ya karfin tunanin mai tunani " ta na gama fadar haka ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya , ta ja wani dogon nunfashi kafin ta lumshe idanunta , ta sake bude su a hankali ya ga sun koma dai² a hankali ta juyo ta kalle shi ta ce " baby me ya faru ? " wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke kafin ya ce " ba komai " wani dan karamin murmushi ta saki sai kuma ta tsuke fuska lokaci guda ta na fadin " sai yanzu ka dawo , ni na yi fushi ma da kai " ta kai karshen ta na kauda kai " sorry Cutie , na tafi yin wani aiki ne " ya fada cikin sanyin murya turo dan bakin nan nata ta yi ta na fadin " baby yunwa na ke ji , tun tafiyar ka ban ci komai ba " " shikenan , me ki ke ki ci ? " da sauri ta ce mishi " irin abincin da ka ke min a US " ta fada ta na sakin wani dan karamin murmushi gyada mata kai ya yi kafin ya ce " okay , jira ni ina zuwa " da to kawai ta amsa mishi , da ga haka ya tashi ya nufi kitchen ya shiga da kallo ta raka shi har sai da ya shiga sannan ta saki wani dan karamin murmushi sai da ya dauki one hour a cikin kitchen din kafin ya fito ya na rike da wani tray kai tsaye gabanta ya karaso ya zauna a kassa saman carpet , sannan ya ajiye tray din a gaban shi ya na ce mata ta sauko ba musu ta sauko kassa su na fuskantar juna , ya fara ba ta abincin da kan shi sai da ta kammala sannan ya dauki tray din ya mayar da su kitchen sannan ya dawo parlourn ta na zaune saman sofa ya tardo ta , ta shafar cikin ta a hankali ya karaso wajen ta ya zauna ya na fadin " yanzu tashi ki je ki konta " shagwabe mishi fuska ta yi ta na fadin " ba tare za mu kwana ba ? " a hankali ya girgiza mata kai allamun a'a shiru ta yi ta na kallon shi babu ko kiftawa sai da ta dauki lokaci kafin ta ce " baby , amma akwai abun da ke damun ka ko ? " " me ki ka gani ? " ya fada a sanyaye " kawai na ga yanayin face din ka ya sauya ne " " ba zan miki karya ba , ina cikin damuwa , ba kadan ba , amma duk lokacin da na tare da ke na kan ji damuwata ta tafi , please don't leave me , kar ki tafi ki bar ni " wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta rungume shi ta na fadin " mutuwa ce kadai za ta raba ni da kai " a hankali ya zagayo da hannayanshi a bayanta ya rungume ya na sauke ajiyar zuciya a hankali ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ ( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊 【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】 【 BOOK ________ 4 📚✍💌 】 _______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________ { P A G E ________ 7 & 8 ✍💕🔥} Sai da ya dauki lokaci rungume da ita a haka kafin ya raba jikinsa da nata ya na ce mata " yanzu tashi ki je ki konta dare ya yi " marairaice mishi fuska ta yi ta na turo dan bakin nan nata ta ce mishi " please baby tashi mu je ni ba zan iya kwana ni kadai ba " ta kai karshen idanun ta na cikowa da ruwa kamar za ta yi mishi kuka a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " shikenan , tashi mu je " ya fada dan ya san halin ta yanzu za ta yi zaune ta aza mishi kuka duk sai mutanan part din sun fito , gwara ya yi abun da ta ke so ko ya samu ya rabu da ita cikin lalama wani kyawatencen murmushi ta sakin mishi kafin ta mike tsaye ta na turo katon cikinta a hankali shi ma ya mike ya riko hannunta su ka shiga corridor , ya shiga bedroom din ta cikin sa'a ko babu kowa su na shiga ya saki hannunta ya juya ya rufe kofar ya saka mata security kafin ya juyo gare ta ya ce mata " let's go sleeping , i'm very tired " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce mishi " baby , mu je na yi maka tausa mana " " uhm , da ni da ke wa ya fi bukatar tausa da wannan katon cikin naki " turo mishi dan bakin nan nata ta yi kafin ta nufi gadon ta Haye ta zauna a tsakiya ta yi irin zaman nan na bokaye shi dai bawan Allah ya na shan rigima

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});