Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 20

Chapter 20

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,077 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

konce , ki na tunanin da a ce uku ne ba zai fi ki farin ciki ba , amma kin gani baby biyu ne , kawai tunanin ki ne ya ba ki hakan " cikin kukan nata ta katse mama da cewa " amma mama ina jin kukan shi , ina jin shi ya na kira na " a hankali mama ta girgiza mata kai ta kai hannu ta fara goge mata hawayenta ta na fadin " tunanin ki ne kawai , please ki kontar da hankalin ki kin ji auta ? wannan su kadai ne babyn ku a yanzu sai wanda za ku samu a nan gaba , ai ki na so ko ? " wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " mama da gaske biyu ne ba ? ba uku ba ? " " no biyu ne Allah ya Albarkaci auren ku da su , ko ba ki son su ? " da sauri ta ce " mama ina son babyna mana , fiye da komai " " har ni ? " su ka tsinci Muryar Malik ya na fada a tare su ka juya su na kallon shi , ya tsare su da ido wata yar karamar dariya ta yi kafin ta ce " ina son ka fiye da tawa rayuwar " gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya mike ya kontar da babyn saman gadon shi dan ya yi barci , sannan ya dago ya ce musu " yanzu na dawo " ya kai karshen ya na juyawa zai fita har ya kai bakin kofar mama ta ce mishi " tsaya don Allah ina son na yi magana da kai , auta yanzu na dawo " ta kai karshen ta na sakin Inaya ta mike ta bi bayan Malik su ka fita ita kuma Inaya ta koma ta konta sai da su ka yi dan nisa da dakin sannan su ka tsaya mama ta ce mishi " na sani Triplets ne ta haifa , ban ga laifin ka ba dan ka boye mata dan kar ta cutu , amma ina jin wani abu wanda ba zan iya fada maka ba " cikin rudu ya ce mata " ta ya a ka yi ku ka san uku ne bayan ni da doctor da nurse biyu ne kawai mu ka san triplets ta haifa , ko ita na yi mamakin yadda a ka yi ta san Triplets ne " " Muryar shi ta jiyo , haka ni ma na jiyo Muryar shi ta haka ne na gane su uku ne ta haifa , but zan so ka koma wajen doctor ka tambaye ta ina babyn ka ya ke in ba ta gan shi ba za ta iya samun sukuni ba , haka za ta yi ta jin Muryar shi " wani dogon nunfashi ya ja ya na saukewa a hankali kafin ya ce " ki yi hakuri mama , ba zan iya ba , na san in ta ji labarin shi ba za ta iya jurewa ba , shi ya sa na boye wannan maganar , ke ma ina rokon ki don Allah kar ki fada mata " " amma ya ka ke so ta yi Muryar shi da ta ke ji ? " " zan san yadda zan yi " ya na gama fadar haka bai jira amsar ta ba ya raba ta geffen ta ya wuce a hankali ta juya ta bi shi da kallo na dan lokaci kafin ta juya ta sauke wata yar karamar ajiyar zuciya sannan ta koma dakin Inaya ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ ( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊 【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】 【 BOOK ________ 4 📚✍💌 】 _______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________ { P A G E ________ 17 & 18 ✍💕🔥} ▪AFTER TWO DAYS wani katon waje ne cike da chairs red color dukkan su , su na kallon wani hall a saman hall din akwai wata doguwar table shinfide da wani tissu white color , an jera drinks kala² a sama da Mic guda 11 a gaban kowace kujera , amma na gaban farar chair din nan ya fi kawatuwa , bayan table din akwai wasu chair guda biyar a geffen , biyar a geffen hagu sai wata babba fara kal ta alfarma a tsakiyar su wajen duk zagaye ya ke da Sojoji , kowane rike da gun ya daure fuska , ga wasu yan JARIDA zazzaune saman chairs din nan , sai wasu manyan cameras wajen hall din nan cen na hango Diya zaune saman kujerun da ke saman Hall , da Rafik , da General Abdallah , Idris da Hussein a geffen dama , a geffen Hagu ma akwai wasu biyar zaune saman chair din da allamun wadanan su kuma ministers ne wajen ya yi tsit ba ka jin komai su na a haka Malik ya shigo wajen ya na sanye da wasu suit Farare kal ma su mugun kyau , ya saka wasu sneakers farare kal a kafafun shi , ya daure wanan smooth hair din nashi a baya , ya na taku cike da Izza wasu sojoji guda uku na biye da bayan shi ya na shigowa wajen kowa ya mike tsaye , har su Diya , nan take kowa ya shiga yin tapi , dan duk mutanan wajen ba karamin dadi su ka ji ba ganin shi a haka har ya karaso saman hall din nan , ya nufi chair din Fara , da sauri wani soja da ke tsaye baya ya karaso zai janyo mishi chair a hankali Malik ya daga mishi hannu , ba musu ya koma ya tsaya hannu ya sa janyo chair ya zauna , sai da ya zauna sannan kowane ya koma ya zauna su na kallon shi cike da nitsuwa ya fara magana cikin wata zazzakar murya ya na fadin " Assalamualaikum wa rahmatullah wa barkatuhu , My name is Nawfel Hicham Bin Jaabar , na ji dadin ganin yadda ku ka hallaci wannan zaman , kafin mu fara abun da ya kawo mu , zan so mu bude taron nan da addu'a , mai girma Rafik , bismillah " ya fada ya na dan kallon Rafik ba musu Rafik ya mike tsaye ya fara jero musu addu'o'i su na amsa mishi da Ameen , sai da ya kammala sannan ya koma ya zauna saman chair din shi ya na zama Malik ya ce " Alhamdoulilah , na san kowa a wajen nan ya san matsayina a cikin kassar nan tamu mai albarka , na san kuma kowa ya san abun da ya faru last seven months da ba nan , bayan hawan Aymane Bin Abdoul Mujeeb kujerar Malik , da farko zan so na gabatar da sakon ta'aziyata ga ahalin da su ka rasa 'ya'yansu , ina me kara ba ku hakuri , in sha Allah wannan shi ne na karshe da izinin ubangiji , Tabbas ni na hakura na sauka da ga kujerar Malik , amma ba wanda ya yi tunanin Abun da Malik Aymane zai aikata , a lokacin da na samu labarin abun da ke faruwa a cikin masarautar na yanke shawarar

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});