Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 13

Chapter 13

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,114 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

dari ya sa wutsiyar shi ya buge ta , wata yar karamar kara ta saki ta na yin cen gefe ta fadi " Cutie ! " Malik ya fada da karfi ya na zaro idanu lokacin da macijin nan ya buge ta , sa karfi ya shiga kai wa hayakin nan bugu amma ina , ba kuma zai iya zagaye shi ba dan hayakin ya raba masarautar biyu , babu ta hanyar wucewa lokaci guda Abyad ta bace , sai ga ta tsugune geffen Aswad ta na fadin " ba ki ji ciwo ba ? " " a'a " Aswad ta fada ta na kokarin tashi da sauri Abyad ta mike tsaye , ta na kallon macijin nan ya na kokarin cire sword din Aswad da ke bayan shi a hankali ta mika hannunta , kamar da ga sama wata farar bow ta fito cikin hannunta a hankali ta kai dayan hannunta , ta fara jan zaren bow din nan kamar ta na shirin tilla kibiya sai da ta ja shi har karshe kafin ta saki , kawai sai na ga wata farar Arrow ta fito ta nufi macijin nan da mugun gudu ta soke shi a jiki wani marayen kuka macijin nan ya saki dan ba karya ya ji zafin hakan lokaci guda Abyad ta bace bat , ta koma gaban macijin , ta kara jan bow din nan ta harba mishi kibiya , ta sake bacewa ta koma bayan shi , ta harba mishi wata arrow a baya , yanzu ma ta sake bacewa ta koma dayan geffen ta sake harba mishi arrow , sai da ta harba mishi har guda hudu kafin bow din hannunta ta bace wani marayen kuka macijin nan ya saki , kafin ya nufe ta gudu , duk da ya galabaita dan har idanun shi sun fara rufewa , jikin shi ya yi sanyi ya na isa ya sa wutsiya , kafin ta bace , ya matse ta a cikin wutsiyar shi ya daga ta sama , ya buga ga kassa da mugun karfi har kura na tashi da mugun gudu Aswad ta tasso , ta nufi Abyad ta Zube saman guyiwowin ta , ta talabo ta , ta na fadin " Abyad , Abyad , ki na ji na ? " murya a disashe ta ce " ina jin ki , ba abun da ya same ni " da sauri Aswad ta mike tsaye , cike da bacin rai , ta bude baki ta yi wata razananiyar kara ta na kallon macijin nan nan take wata bakar guguwa ta tashi da karfi ta fara mamaye macijin nan , a hankali Aswad ta daga kafa ta shiga cikin guguwar nan , ta tsaya cak waje guda a hankali ta mika hannunta , da sauri Sword din ta da ta caka mishi a baya ta fito ta koma cikin hannun ta wata razananiyar kara macijin nan ya saki lokacin da sword din ta fita da ga jikin shi da sauri ya nufi Aswad cike da bacin rai , sai dai kafin ya iso gare ta , ta bace bat cikin guguwar nan cak ya tsaya ya na juyi ya na kuka ya na neman Aswad sai da ya share one minute a haka , babu Aswad ya na a haka ya ga kawai ta fito da ga cikin guguwar nan cen sama dai'dai tsawon shi , kamar an tillo ta , ta daga sword din ta sama ta raba macijin nan gida biyu har jininshi ya watsun mata a fuska nan take ya fadi kassa rabi ya yi gefe , rabi ya yi dayan gefe non take gudun guguwar nan ya kara , sai kururuwa ta ke yi wani razanannan sauti na fitowa da ga ciki sai da ta yi wajen good one minute ta na wannan sautin kafin ta bace bat tare da macijin baki daya wata nanauyar ajiyar zuciya Abyad ta sauke ita da Aswad a tare , ta tashi da gudu ta nufi Aswad wani dan karamin murmushi Aswad ta saki kafin ta bude mata hannayan ta , ta na isa ta shige jikin ta a hankali farin hayakin nan da ta tare su Malik da shi ya fara yin kassa har ya bace shi ma ya na bacewa ko sai ga Inaya tsaye a wajen , ta na sanye da kayan ta na farko , idanun ta sun komo dai'dai har wannan katon cikin nata a hankali ta fara bin wajen da kallo ta na tambayar kanta me ta ke yi a nan cen ta hango su Malik tsaye , sun yi cirko² su na kallon ta babu ko kiftawa sun ma rasa abun da za su ce , da a ce wani ne ya ba su labarin abun su ka gani yau , da wlh sai su ce mishi ba shi da hankali , amma da idanunsu su ka gani , kowa ya shiga yi wa Inaya ayar tambaya ban da Malik ta na ganin shi ta saki wani cool murmushi ta fara takawa a hankali ta nufe shi ya na ganin ta fara takowa ya sauke wata nanauyar ajiyar zuciya har zai daga kafa kawai ya ga ta tsaya cak , kawai sai ya ga wajen da ta ke tsaye ya jiqe kamar an watsa mishi ruwa wata irin muguwar murdawa cikin ta , ya yi mata har sai da ta saki wata razananiyar kara ta na dafe shi da hannayan ta a dubu dari Malik ya yi kanta ya na fadin " Cutie , me ya faru ? " amma ko jin shi ba ta yi sai kara ta saki , ta nunfashi sama sama da sauri su MALIKAT INAS su ka nufe su dan sun ga allamun kamar naquda ce ta ke , ga shi kuma ta zubar da ruwa hakan na nufin haihuwa za ta yi MALIKAT INAS na karasowa wajen Malik ta ce mishi " mu kai word room , haifuwa za ta yi " dum ya ji gaban shi ya fadi , tun kafin wani ya yi magana , ya sa hannayan shi biyu ya dauke ta cak sai kara ta ke saki ya nufi word room da ita sai cije lips din shi ya ke dan ba karamin zafi hannun shi na dama ya ke yi mishi ba , ga shi ko sai zubar da jini ya ke amma a haka ya daure ya nufi word room da ita , tun a reception ya shiga kwallawa su doctor kira dama cikin word room din akwai mace likita me karbar haihuwar matan masarautar da gudu wata nurse ta tafi office din ta , ta kira ta ta na fitowa ta cewa Malik " yi sauri ka shiga da ita dakin cen " ta fada ta na nuna mishi wani daki da sauri ya nufi dakin , har su MALIKAT INAS sun bi bayan shi , doctor ta ce musu " a'a ku tsaya a nan , shi ma yanzu zai fito " ta kai karshen ta na nufar dakin da Malik ya shiga ba musu kowane ya zauna saman waiting chair , kowane da addu'ar da ya ke yi cikin zuciyar shi bangaran Malik kuwa , ya na isa cikin dakin kawai ya

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});