Chapter 11
Chapter 11
namun daji , har kukan tiger na ke jiyo wa amma shi ko tsoro babu ya ratsa ta dajin nan cikin motar shi ya yi ten minutes a haka kafin na ga ya tsayar da motar bakin wani katon dutsi a hankali ya bude kofar motar ya fito , kai tsaye dutsin nan ya nufa , nan na ga wata yar karamar kofa kamar cellar da ga kasan dutsin ko digon haske ba ya fitowa babu ko tsoro ya nufi kofar ya shiga babu ko sallama kamar da wassa kawai sai na ga wajen da mugun haske kamar safiya , wajen zallar dutse ne an yi zanen macizai a sama da mutane , ga wata wuta na tashi tsakiyar dutsen da wasu kwalabe zagaye da wutar hayaki na tashi da ga cikin su kai wajen ba zai iya kwatantuwa ba dan bai yi kama waje holy ba , da ga gani wajen tsafi ne in ba haka ba ya za a ce da ga waje na ga wajen duhu babu digon hasken da ke fitowa ta kofar ga shi kuma cikin da mugun haske kamar da safe , kai ni dai zuciya ta ba ta amince da wajen nan ba a hankali Aymane ya karaso gaban wutar nan ya sa hannu daya bayan daya ya fara cire kayan jikin shi ya na ajiye wa gefe sai da ya rage da ga shi sai short sannan ya zauna gaban wutar nan , ya yi irin zaman cin tuwo ya kai hannu ya dauki gudar kwalba ya sa yatsun shi biyu a ciki kafin ya fiddo su da wani abu ja a sama kamar jini , kai tsaye saman forehead din shi ya shafa wannan abun ya na shafawa ko ya shanye kamar bai shafa komai ba , a hankali ya meda kwalbar ya ajiye ya lumshe idanunshi ya fara karanto wani karatun mara dadin ji , a hankali wani dan karamin iska ya fara tashi a wajen a dubu dari ya ware idanunshi , ba karamar razana na yi ba ganin yadda idanun shi su ka koma na maciji , ma su ban tsoro ya tsare waje guda da ido kamar a film haka na fara ganin zanen macizan nan da ke saman dutsen nan sun fara fitowa kamar na gaske , daya bayan daya su ka nufi Aymane kawai sai su shige jikinsa su bace bat su na bacewa ko zanen ke fitowa saman fatar jikin shi , sannu sannu har sai da jikin sa ya cika da wadanan zanen sannan na ga ya ja wani dogon nunfashi ya lumshe idanunshi kafin ya sulale a wajen ko motsi ba ya yi ya na faduwa ko wutar nan ta gaban shi ta mutu ita kan ta , wajen ya koma duhu kamar ba a taba yin haske a wajen ba 🤧🤧🤧 NI DAI BA ABUN DA ZAN CE SAI DAI ALLAH YA KARE MANA MALIK , AYMANE YA WUEC ABUN DA YA KE TUNANI , MUGU NE NA GIDAN GABA , YANZU NI WANNAN ABUN DA YA YI BAN MA SAN KO MINENE BA , SAI DAI RANAR DUEL DIN MU GANI AMMA NA SAN BA AL'HERI NE BA , SAI DAI KAWAI NA CE MALIK ALLAH YA KARE KA DA GA SHARIN AYMANE DA MACIZAN SHI ▪AFTER TWO DAYS 🤧🔥 yau ta kama ranar Friday , tun karfe 6 a ka fara shirye²n duel din Malik da Aymane misalin karfe 8 kowa ya hallaci wajen da za a gabatar da duel din , a cikin garden a ka shirya yin duel din kowa na cikin masarautar sai da ya hallaci wajen , da mutanan fadar Malik , da kuma na fadar Aymane , har da su MALIKAT INAS , da Inaya ba rokon da su mama ba su yi mata ba a kan ta zauna , amma fir ta ki ta ce sai ta je a tsaye Malik da Aymane su ke tsakiyar garden din , su na fuskantar juna , Rafik na tsaye da ga tsakiyar su a gefe cikin nitsuwa ya fara magana ya na fadin " kun san yadda tsarin fada da takobi ya ke , ban da zalinci " cikin nitsuwa Aymane ya katse shi da cewa " ka ga don Allah ka ba mu waje mu yi mu wuce wajen , a sani na ka kashe ko a kashe ka shi ne tsarin wannan fadan , dan haka ka wuce ka ba mu waje " " za ka iya tafiya Rafik " Malik ya fada cikin sanyin murya gyada mishi kai Rafik ya yi kafin ya juya ya karbi Sword din da ke hannayan Azim da ke tsaye bayan shi ya mikawa Aymane guda , sannan ya mikawa Malik guda ya na fadin " Allah ya ba mai rabo sa'a " amma cikin zuciyar shi Malik kawai ya ke yi wa addu'ar samun nassara , da ga haka ya bar wajen ya koma wajen da a ka shiryawa ma su kallo ya zauna saman chair din shi geffen MALIKAT AL'UMU , ya na zama ko Aymane da Malik su ka fara fadan su a hankali MALIKAT AL'UMU ta juyo ta kalli Rafik ta ce " Rafik , wai fadan minene su ke yi ? " wani dan karamin murmushi Rafik ya yi ya na fadin " ranki shi dade , wanda ya yi nassara shi zai hau kujerar Malik " " Wanda bai yi nassara kuma fa ? " MALIKAT INAS ta fada dan jinkirtawa Rafik ya yi kafin ya ce " mutuwa zai yi " a tare su ka ce " inallillahi wa'ina illaihi raji'un , ka na nufin idan Malik bai yi nassara ba kashe shi Aymane zai yi ? " a hankali ya gyada mishi kai ya na fadin " ina jin tsoron hakan ranki shi dade , addu'a kawai za ku yi Allah ya ba shi sa'a , idan Aymane ya yi nassara za mu shiga babban tashin hankali dan babu wanda zai iya yin jayaya da shi a kan kujerar Malik " kalmar shahada MALIKAT AL'UMU da INAS su ka shiga jerowa , kenan kashe musu yaron su za a yi in dai bai yi nassara ba , nan take zuciyoyinsu su ka fara bugawa da karfi a hankali MALIKAT INAS ta juya ta kalli su Malik dai'dai lokacin da Aymane ya samu Malik a damtsen shi na dama ya yanke shi nan take ya fara zubar da jini har ya gangaro saman takobin hannunshi da sauri Inaya ta rumtse idanunta , ta na kauda kai gefe a hankali RIANNA ta riko ta , ta na fadin " ko mu koma ciki ? " girgiza mata kai Inaya ta yi ta na fadin " a'a Aunty RIANNA " da to kawai RIANNA ta amsa mata kafin su ci gaba da kallon su Malik wata yar karamar dariya Aymane ya yi lokacin da ya ji wa Malik ciwo a hannu ya na fadin " ya ,har ka gaji ? still yanzu ma mu ka fara " a hankali ya kai hannun shi na hagu ya riko sword din , dan ba karamin rauni ya samu ba , ba zai iya ci gaba da fadan da hannun damar ba wata yar karamar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31