Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 24

Chapter 24

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,087 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

cream na ke so , mu tafi mu sayo ice cream " har da wasu hawayen iskanci ya ke kamar da gaske sarai Malik ke jin shi amma ya share shi , dan ya saba da rigimar Prince , da ya tashi dauko momyn shi sai da ya wuce , gwara ya share shi , dan in ya ce zai biye mishi yanzu zai yi frog jump , ya san ba karamin aikin Prince ba ne ya ce sai ya yi frog jump sannan zai hakura da ice cream din , dama dama Princess ita ta dauko miskilancinsa , shiru da ita in har ba tabo ta ka yi ba , sai ka rantse ba ta cikin wajen akwai wata rana da su ka taba fita da PRINCE su ka manta da ita cikin bedroom din ta , amma a haka su ka je su ka dawo ta na cikin bedroom din ta , ta na konce ta na barci ya na a haka kawai ya ga Prince ya sa hannu ya ture laptop din shi har sai da ta fadi kassa ba tare da ya bar kukan shagwabar shi ba cak Malik ya tsaya ya na zaro idanu , kamar ya tashi ya yi kuka shi ma ya ke ji dan jarabar Prince wani dan karamin kukan kura ya yi kafin ya tashi a zafafe , ya dauki Prince ya juya ya na kallon kofar Kitchen ya na fadin " Cutie ! Cutie ! Cutie ! " ya ke kwalla mata kira da karfi cikin nitsuwa na ga Inaya ta fito da ga kitchen din Masha Allah , Gaskiya ba karamin kyau ta kara ba ta cika ta yi bul bul abunta , da ga gani ta samu hutu , har wani haske ta yi kumatu sun fito , gaskiya US ta zauna mata ta na sanye da wando palazzo pink colour , da wata t-shirt blue , amma da ga gani ta Malik ce dan ta so ta yi mata yawa a haka har ta karaso cikin parlourn , a sanyaye ta ke fadin " baby , lafiya ka ke min irin wannan kiran ? " mika mata Prince ya yi ya na fadin " rike yaron ki ! " cikin rudu Inaya ta kai hannu ta karbi Prince da ke ta faman turo dan bakin nan nashi irin nata ta na karbar shi ta juya ya dauki laptop din shi da ta fadi , da wayoyin shi , sannan ya juyo ya kalle ta ya ce " na bar muku gidan , na san sai kun kashe ni za ku huta , da ke da yaron ki ku na neman ku saka min hawan jini wlh , da daddare ban huta ba , da safe ban huta ba , gwara na tafi tun kafin ku kashe ni " ya na gama fadar haka ya juya ya nufi kofar fita parlourn ya fice wata yar karamar dariya Inaya ta yi dan ta san yaron nata ya tsula tsiyar tashi , sai da ya fita sannan ta dawo da kallon ta saman shi ta na fadin " me kuma ka yi wa Daddyn naka ? " cike da shagwaba Prince ya ce mata " Cutie , ni fa kawai na ce mishi ina son ice cream ne , shi ne ya yi fushi ya tafi , ni ke ce mishi ya dawo , na bar ice cream din , ina son zama tare da Daddyna " ya kai karshen ya na sakin kukan gaske wannan karan ita dai ta tsaya ta zuba mishi ido ya na hawaye bibiyu , kamar ba shi ya tukarawa baban nashi ba har ya tafi , yanzu kuma ya na kuka dan ya tafi , ta tafi duniyar tunanin ta kawai ta jiyo Muryar Malik ya na fadin " wa kuma ya taba min babyna ? " a tare ita da Prince su ka juya su ka kalli saitin kofar parlourn ya na tsaye ya na sakin wani dan karamin murmushi , dama ba tafiya ya yi ba , laptop din shi ne ya kai cikin motar ya runo ashe ya manta file din shi , shi ne ya dawo zai dauka , ya jiyo Prince na kuka da sauri Prince ya diro da ga jikin Inaya ya nufi Malik ya na sa isa ko Malik ya sa hannayan shi biyu ya dauke shi , cikin sanyin murya ya ce " I'm sorry my Prince , bari mun tafi sayan ice cream din , now stop crying please , kai ma ka san ba na son ganin kukan ka " wani dan karamin murmushi Prince ya saki kafin ya kai hannu ya fara goge hawayen shi , ya kontar da kan shi saman shoulder din Malik , ya lumshe idanunshi , da alamun barci ya ke ji , Inaya na ganin ya lumshe idanunshi ta san to na barcin ne su ka sauko mishi , " baby , ina ga barci ya ke ji , ka kai shi bedroom din shi yanzu ina zuwa " ta fada ta na juyawa ta koma kitchen ba musu ya nufi stair ya Haye , kai tsaye bedroom din Prince ya shiga bedroom din ta hadu gaskiya , komai na cikin ta blue ne , har gadon , da carpet , ga ta ko cike da kayan wassa , har da su play station , dan wani lokaci tare su ke game din su shi da Malik kai tsaye saman gadon shi Malik ya kontar da shi , sannan ya zame jacket din shi , ya ajiye gefe , ya sauko ya manna mishi kiss saman forehead , kassa kassa ya ce " i love you my baby " cikin magagin barcin nashi ya ce " i love you too my Daddy " wani cool murmushi Malik ya saki kafin ya sake ce mishi " konta ka huta , in ka tashi sai mu tafi sayan ice cream , mu biya park , okay ? " wani dan karamin murmushi Prince ya saki kafin ya gyada mishi kai , ya juya mishi baya ya kai hannu ya janyo Teddy din shi , ya rungume janyo duvet Malik ya yi ya rufe shi har zuwa kirji , sannan ya sauko da ga saman gadon , ya kashe lamps din dakin , Sannan ya fito ya na fitowa ya ci karo da Inaya taa shirin shiga dakin da sauri ya sa hannu ya toshe mata baki ya yi baya da ita , su ka shiga nasu bedroom din , sannan ya meda kofar ya rufe ya sa mata security cikin rudu ta ce mishi " lafiya ka min irin wannan janyowar ? " a hankali ya tako ya tsaya gaban ta , sai dai ya kare mata kallo da kyau sannan ya kai hannu ya ja mata hanci ya na fadin " dubi don Allah yanzu kin bata min yaro da wannan rigimar taki " hmmm , kamar dama jira ta ke kawai sai ta sakin mishi kukan shagwaba har da bubuga kafafu a kassa bai ce mata komai ba kawai ya sa hannu ya yi sama da rigar ta ya fidda mata ita , ya hade bakin su waje

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});