Chapter 19
Chapter 19
abun da na fada maka " a hankali Malik ya janye hannayan shi , kamar wanda bai san komai ba ya ce " me ka fada min , ni ban ni abun da ka fada ba " ya kai karshen ya na nufar kofar fita dakin da sauri Diya ya riko hannunshi ya na fadin " kar ka tafi ba ka ce min komai ba don Allah " a hankali Malik ya juyo ya ce mishi " don Allah malam tun dazu ka kawo ni nan ka tsaya ka na min kuka kamar wani karamin yaro , ni fa ina son na je na ga babys di na " " ka na nufin ba ka ji abun da na fada maka ba ? " Diya ya fada cikin rudu " yeah ban ji ba , ban kuma gani ba , zan iya tafiya yanzu ? " wani cool murmushi Diya ya saki dan ya gano abun da Malik ke kokarin yi a hankali ya saki hannunshi ya na fadin " shikenan tafiyar ka , ni barci ma na ke ji " " na gode " Malik ya fada a takaice kafin ya juya ya cire security din kofar ya fice ya bar Diya nan tsaye ya na sakin murmushi dama ya jima ya na son ya fadawa Malik wannan maganar amma ya rasa ta ina zai fara , amma yau ya samu kwarin guyiwar fada mishi , kuma ya ji dadi da Malik bai dauki abun wani iri ba , ya san da wani ne zai yi mishi wani kallon daban har ya yi kokarin kashe shi , amma Malik ko ajikinshi , shi ya sa ya ke Alfahari kasancewar shi dan uwa kuma amini ga Malik ▪MALIK bakinshi da Sallama ya shigo room din da Inaya ke konce , nan ya tardo ta zaune saman gadon , ta na rike Nayel wata nurse na gwada mata yadda za ta ba shi nono , Nailah kuma har yanzu ta na barci da allamun ita ma ta gaji har ya karaso wajen ba su lura ba , a hankali ya yi musu gyaran murya ya na fadin " za ki iya tafiya " ba musu nurse din nan ta fice ta ba su waje ta na fita ya janyo chair ya zauna bakin gadon ya na kallon Inaya ta na ganin ya zauna ta turo mishi dan bakin nan nata ta na shirin magana ya riga ta cewa " no please kar ki min wannan shagwabar taki a gaban babyn mu " ai ko sai da ta yi mishi shagwabar ta na fadin " ka ce mishi ya sake ni , zafi na ke ji " " ki bari idan ya ishe shi zai saki " ya na gama fadar haka ko babyn ya sake mata nipple wani dan karamin murmushi ta saki ta na kallon shi a hankali Malik ya kai hannu ya dauki babynshi , wani dan karamin murmushin geffen fuska ya saki lokacin da idanunshi su ka sauka cikin na babyn shi ya na a haka ya jiyo Muryar Inaya ta na fadin " la baby , da gaske murmushi ne ka ke ? " ta fada ta na dan leko face din shi a hankali ya dago babyn ya kai bakinshi wajen kunnen babyn ni dai ban ji abun da ya ke fada ba sai da ya gama sannan ya sauko babyn ya kalle ta ya ce " ba za ki gane ba , i'm just Happy to day , specially da ba abun da ya same ki " marairaice mishi fuska ta yi ta na fadin " amma yaya Zayd ba za mu sake samun wani babyn ba ko ? wlh sai da na ji kamar zan mutu sai da na dinga ganin wutar lahira " maganar ta ba karamar dariya ta so ta bashi ba amma ya danne kayanshi ya saki wani dan karamin murmushin geffen fuska ya na fadin " don't worry , Nayel & Nailah sun ishe mu , bayan su ba kari " wani cool murmushi ta sakin mishi kafin ta ce " ta gaske Nayel ka saka mishi ? " a hankali ya gyada mata kai allamun Eh wani kyawatencen murmushi ta saki har da dariya , ta na kallon shi rike babynsu " dubi har ya yi barci " ya fada ya na nuna mata Nayel da ya yi barci a cikin hannunshi murmushi mai dan sauti ta yi kafin ta ce " ba dole ba , ya na cikin hannun Daddyn shi dole barci ya dauke shi " bai ce mata komai ba ya ci gaba da kallon Nayel , sai zuba mishi surutu ta ke amma ba ya ma jin ta tuni ya tafi duniyar tunanin shi ya na a haka ya jiyo Muryar ta ta na fadin " baby , ina gudan babyn mu , ban gan shi ba " Dum ya ji zuciyar shi ta buga har dan zaro idanu ya yi da sauri ya dago kai ya na kallon ta , sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " wane baby kuma bayan Nayel ? " a hankali ta girgiza mishi kai ta na fadin " baby , ni Nayab na ke cewa " wannan karan har wani dishi dishi ya gani , ya a ka yi ta san sunan da ya yi mishi huduba da shi , dan tabbas sunnan Nayab ya saka mishi a hankali ya bude baki Muryar shi har kerma ta ke ya ce " Cutie , Nayel ne ba Nayab ba " da sauri ta katse shi da ta na girgiza kai kamar za ta yi kuka ta ce " baby , ni baby uku ne a cikina , ina gudan babyn , ina jin Muryar shi ya na kira na , in wassa ka ke ka bari please , ni ka kawo min baby na " duk inda hankalin Malik ya ke sai da ya bi ya tashi ya ma rasa ya zai yi , ya a ka yi ta san da Nayab , bayan ya na da tabbacin ba ta cikin hayacinta lokacin da ya shigo duniya , in ma doctor ce ta fada mata ya a ka yi ta san sunan shi Nayab bayan shi bai fada mata ba ya yi nisa duniyar tunanin shi kawai ya jiyo Muryar mama ta shigo dakin ya na sallama a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya juya ya na amsa mata sallamar ta Inaya na ganin ta ta saki kuka ta na fadin " mama , ki ce mishi ya fiddo min babyna , ina jin shi ya na kira na , amma wai ya ce shi bai san maganar me na ke ba , ni baby uku na haifa ba guda ba , ku medo min da babyna " a hankali Mama ta rungume ta ta na fadin " Auta , duba ki gani " ta fada ta na nuna mata Malik da ke rike da Nayel cikin rudu Inaya ta kalle su kafin ta juyo da kallon ta kan mama cikin sanyin murya mama ta ce mata " kin dai gani , mijin ki ne kuma ya na rike babyn ku , ga guda kuma a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31