Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 26

Chapter 26

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,055 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

da a ka fi bukatar ka , a ranar da mu ka hadu na ga damuwa sosai a tattare da kai , ga kuma halin da familyn ka ke ciki , ba zan so na kara maka wata damuwar ba , that's why na yanke shawarar yin shiru , na fara tambayar ka abun da ke damun ka , na ga in zan iya taimaka maka , na san indan ka samu nitsuwa kai da kanka za ka nemi sanin halin da familyn ka ke ciki " wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke , sai da ya dauki lokaci kafin ya ce " na gode , i don't know how zan yi maka godiya " cikin nitsuwa Aylan ya katse shi da cewa " please , ba sai ka yi min godiya .... " " no , in ban yi maka godiya ba na san sai Allah ya kama ni , ko ba komai kai ka kawo nitsuwa cikin rayuwa ta " ya kai karshen ya na rungume Aylan ba shiri wani dan karamin murmushi Aylan ya yi kafin ya rungume shi shi ma , ya na dan bubuga bayan shi a hankali sun dauki lokaci a haka kafin su raba jiki da murmushi a face din shi Malik ya ce " please , mu je na gabatar maka da familyna " " ka ce ba kai kadai ba ka zo wannan karan ? " wata yar karamar dariya Malik ya yi ya na gyada mishi kai ya ce " yeah , ni da Cutie da Prince , my son " gyada mishi kai Aylan ya yi kafin ya ce " okay , ina jiran ku " gyada mishi kai shi ma Malik ya yi kafin ya juya da sauri ya koma wajen da ya baro su Inaya ya janyo su su ka dawo wajen da su ka bar Aylan sai dai ya na dawo ya neme shi sama da kassa ya rasa , ya kalli hagu , ya kalli dama babu Aylan babu mai kama da shi wani dan murmushi Malik ya saki kafin ya cewa Inaya " ina ya tafiyar shi , mu tafi kawai " da to kawai ta amsa mishi , shi dama PRINCE bai san abun da ke faruwa ba ya na ta shan halawar shi , sai wajajen Magriba sannan su ka baro park din , shi ma sai da su ka biya pastery su ka sayo cake da ice cream sannan su ka koma gida ko da su ka koma , Malik ya yi sauri ya yi wanka ya yi alwala ya fice ya tafi mosque Inaya kuma ta ja Prince ta yi mishi wanka , kafin Malik ya fito ita ma ta shirya shi dan kullum tare su ke tafiya mosque haka su ka tafi su ka bar ta ita kadai cikin gidan , ita ma wanka ta yi ta yi alwala sannan ta fito ta gabatar da sallar ta , sai bayan sallar isha Malik da Prince su ka dawo cikin gidan ▪WASHE GARI ⛅⛅ ▪PRINCE 👑❤ a hankali ya ke sauko stair , ya na tsalle , ya na sanye da wani Trouser black color , da wata sweater Red color , da sneakers farare a kafafun shi , duk in ya yi tsalle sai gashin kan shi ya yi sama ya na gama sauko stair din Malik ya shigo parlourn ya na sallama Prince na ganin shi ya nufe shi da gudu ya na fadin " Daddy , tun dazu fa na ke jiran ka , har na yi fushi " ya fada cike da shagwaba a hankali Malik ya sa hannu ya dauke shi ya na fadin " I'm sorry my Prince , tell me kun gama shiryawa mu tafi ? " da sauri Prince ya ce " yeah , kai kadai mu ke jira , na matsu na ga Ammie , da mamie , da mama , da Uncle " ya fada cike da shagwaba ( hmmm , ko da ga ina ya dauko wannan shagwabar ? 🤔🤔 ) " okay , where is your mom ? " Malik ya fada " wait " Prince ya fada kafin ya juya ya kalli Stair ya ce " Momyyyyyyyyy ! " ya fada da mugun karfi sai da Malik ya lumshe idanunshi ya na fadin " Prince slowly mana , ka fasa min kunne " ya na gama fadar haka Inaya ta fara sauko stair ta na sanye da wata Abaya fara kal mai mugun kyau an yi mata zanen flower kamar rainbow , ta yafa veil din ta fari shi ma , ta na sanye da wasu sneakers pink color a kafa , ta na rataye da wata yar bag pink color ita ma ta na rike da hannun Princess , gaskiya babyn ta hadu kamar na sace ta na gudu , fara kal da ita har ma ta so ta fi Prince haske , sak balarabiya , ta na kama da Malik kamar an tsaga kara , har idanunsa Hazel , kamar dai Prince ta na sanye da wata gown pink color har kassa , sai wata yar jacket white color , mai mugun kyau , fuskarta a daure kamar dai ta Malik a baya , sai ka ce ba ta iya dariya ba tun da ta fara sauko stair Malik ya tsare ta da ido babu ko kiftawa , sai magana prince ke yi mishi amma ba ya jin shi a hankali Prince ya kai hannu saitin fuskar Malik ya kyasta mishi yatsu ya na fadin " Daddy , tun dazu ina maka magana ka kyale ni , sai kallon momy ka ke kamar ba ka san ta ba " a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya dai'dai lokacin da Inaya ta karaso gaban shi ta na fadin " mu tafi ko ? " gyada mata kai Malik ya yi a hankali ya na murmushi kafin ya riko hannun Inaya , ya juya su ka fita parlourn , su ka fito harabar gidan , su na fitowa sai saman motar Malik , kai tsaye ya budewa Inaya wajen mai zaman banza , ta shiga sannan ya daura Princess saman kafafunta , ya rufe motar ya zagayo ya bude wajen driver ya shiga tare da Prince ya zaunar da shi saman cinyoyinshi ya yi tukin a haka har su ka bar gidan su ka nufi hanyar Airport ❤⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❤ 🔥👑 ( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 🕊💕 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) 💕🕊 STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊 【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】 【 BOOK ________ 4 📚✍💌 】 _______________________🕊✍💕🕊✍💕🕊✍💕🕊✍💕______________________ { P A G E ________ 23 & 24 ✍💕🕊} 【 THE LAST PAGE 🤧❤🕊 】 ▪DAULAR SAUDIYA 👑🔥 zaune MALIKAT AL'UMU ta ke cikin parlourn tare da MALIKAT INAS sai murmushi su ke saki su na a haka RIANNA ta shigo ta na sallama ta na fadin " Ammie , momy mu tafi sauran ten minutes jirgin su ya sauka " ba ta jira amsar su ba ta juya ta fice da sauri ta na sakin murmushi a tare MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});