Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,074 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke ya na lumshe idanunshi a hankali kafin ya sake bude su , ya dago kai nan ya ga Doctor rike da wani babyn , sai wuntsila kafafu ya ke , ido a rufe ya na kuka da karfi bai san lokacin da ya lumshe idanunshi ya na yi wa Allah godiya cikin zuciyar shi a hankali doctor ta matso rike da babyn ta ce mishi " congratulation it's a girl , ranka shi dade Triplets ne ta samu " sai da ya sunkuyar da kai ya mannawa babyn hannunshi kiss saman forehead sannan ya dago ya kalli Doctor ya ce " ba na son maganar nan ta fita da ga dakin nan , kar Wanda ya san MALIKAT Triplets ne ta haifa , ko ita kanta kar ku fada mata , ki dauki babyn cikin sirri ki bizine shi " dan zaro idanu ta yi ta na fadin " ran ka shi dade , ba za a yi mishi jana'iza ba ? " bai ce mata komai ba ya juya a hankali ya kontar da babyn saman gadon da ke bayan shi sannan ya juyo ya kali doctor ya ce " zan yi mishi jana'iza , amma ba na son kowa ya san da maganar nan , da ga ni sai ku ukun nan , na roke ku don Allah , dan son annabi kar ku fitar da maganar nan , na san ba za ta iya jure wa ba idan ta ji wannan maganar , ni na godewa Allah ma da ba ta cikin hayacin ta ya shigo duniya , na roke ku don Allah kar ku bari wani ya san wannan maganar , ya zama sirrin mu na mudu hudun nan sai Allah " a hankali Doctor ta gyada mishi kai kafin ta juya ta karbi dayan babyn ta ce " in sha Allah , Twins ne MALIKAT ta haifa , nurse ? " a tare su ka ce " twins ne ta haifa " wata boyayyar ajiyar zuciya Malik ya sauke , ya na shirin magana Doctor ta riga shi cewa " za ka rike shi , ko mu tafi ? " bai ce mata komai ba ya dago hannayan shi a hankali ya mika mata ba musu ta daura mishi babyn a sama nan take ya kara sautin kukan shi ya na wuntsila Kafafu kadan ya kubcewa Malik da sauri Doctor ta karbe shi ta na fadin " Nurse , ku je a yi wa mai martaba dress , ya samu rauni a jikin shi , ku kontar Da hankalin ku , zan kula da komai " ta fada ta na juyawa da babyn hannunta , gudar nurse din ta na rike da namijin sai da ya sunkuyo ya mannawa Inaya kiss a saman forehead din ta , sannan ya kai bakin shi saitin kunnen ta ya yi mata rada kafin ya mike ya juya ya bi bayan nurse din nan su ka baro dakin , ya ma kassa kallon dayan babyn nashi dan ya na jin zafi cikin zuciyar shi ba kadan ba , amma ba komai haka Allah ya so kuma duk abun da ya yi dai'dai ne ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ ( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊 【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】 【 BOOK ________ 4 📚✍💌 】 _______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________ { P A G E ________ 13 & 14 ✍💕🔥} su na fitowa kawai ta ga Malik ya yi gaba abun shi , ya nufi su MALIKAT AL'UMU da ke zazzaune sun yi zugum su na ganin shi su ka mike a tare su na tambayar ta sauka lafiya gyada musu kai kawai ya yi kafin ya ce " za ku iya komawa part din ku , doctor ta ce ta na bukatar hutu " ya kai karshen ya na shirin takawa da sauri MALIKAT AL'UMU ta taro shi ta na fadin " me ta samu ? mace ko namiji ? " slowly ya juya ya kalli MALIKAT INAS , cikin sanyin murya ya ce " Nayel & Nailah " wani kyawatencen murmushi MALIKAT INAS ta saki har hawaye na zubo mata da sauri RIANNA ta ce " Akhie Twins ne ta samu ? " gyada mata kai ya yi a hankali kafin ya juya ya fice word room din ran shi fari tas kamar an yi mishi albishir da gidan Aljanna a haka su ma su MALIKAT INAS su ka baro Word room din , kowace ta nufi part din ta na asali shi ma Diya da Nesrine su ka koma part din su , haka Abdoul da Tesnim Rafik kuma ya nufi fada ya bude ta , ya kira duk wani na fadar ya fada mishi ya dawo Ranar Friday za a sake nada Malik Nawfel Hicham Bin Jaabar bangaran Malik kuwa kai tsaye part din MALIKAT HOUDA ya koma , babu ko sallama ya shigo parlourn , nan ya tardo ta zaune , sai faman addu'a ta ke yi ta na ganin shi ta sauke ajiyar zuciya ta tashi da sauri ta nufe shi ta na fadin " masoyina , ba abun da ya same ka dai ko ? Allah na gode maka " wani dan karamin murmushin geffen fuska ya sakin mata kafin ya ce " kin ga , ki daina kira na da masoyinki , so ki ke papi ya tardo ni , ya ce na kwace mishi matar shi " wata yar karamar dariya ta saki ta na fadin " kai dai ka sani , mara kunya kawai " " shikenan , bari na yi wanka , zan yi miki albishir me dadi " " shikenan , ina jiran ka , mai martaba " ta fada cikin zolaya bai ce mata komai ba ya nufi corridor ya shige bedroom din Inaya ke ciki , kai tsaye toilet ya wuce bai ce mata komai ba ya nufi corridor ya shige bedroom din Inaya ke ciki , kai tsaye toilet ya wuce dan ya yi wanka jim kadan ya fito sanye da bathrobe bed din ya nufo ya zauna , ya zauna a baki ya kai hannu ya bude bedside drawer ya fido A box sannan ya ajiye a sama , sannan ya bude ya fiddo wata yar takarda hannu ya sa ya rabata gida biyu , ya fido wata yar karamar allura irin ta dinki ta na da wani siririn zare blue a hankali ya kai allurar nan wajen yankar da Aymane ya yi mishi , ya fara yi wa kanshi dinki , ya na lumshe idanunshi , ya na cije lips din shi na kassa dan ba karamin zafi a dakwai ba amma a haka ya yi wa kan shi dinki , ya yi dressing wajen , sannan ya tashi ya nufi dressing room jim kadan ya fito sanye da Trouser black color , da T-shirt sky blue , sai wasu sneakers farare a kafafun shi , ya daure wanan smooth hai din nashi a baya , sai tashin qamshi ya ke , sannan ya nufi kofar fita bedroom din ya fito kai tsaye part din ya baki daya ya baro , ya

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});