Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 27

Chapter 27

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,117 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

su ka fito part din , su na fitowa sai saman wasu motoci a jere bakin part din , a tare su ka shiga motar da ke gaban su , su na shiga motocin su ka tada su ka bar masarautar da mugun gudu su ka nufi airport a jere motocin su ka shiga airport , kai tsaye wajen saukar jirgi su ka nufa , sannan su ka yi parking , daya bayan daya su ka fara sauko motocin , Diya da Nesrine su ka fito da ga cikin motar su tare da Junior din su RIANNA kuma ta fito da ga cikin motarta tare da mama da MALIKAT HOUDA MALIKAT AL'UMU da MALIKAT INAS kuma cikin mota guda sannan Abdoul da Tesnim su ka fito cikin mota guda tare da wata kyakyawar yarinya a shekaru ba za ta wuce 3 or 4 years ba , kyakyawa ce gaskiya kamar an tsaga kara da Abdoul dan ta na kama tak da shi , sai dai ta dauko farin Tesnim dan kamar ka taba jini ya fito ta ke har wani ja ta yi ta na ganin MALIKAT AL'UMU ta nufe ta da gudu wani cool murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta durkusa ta dauki yarinyar nan , a hankali duk su ka karaso wajen motar su MALIKAT AL'UMU su ka tsaya da sauri MALIKAT HOUDA ta ce " wai har yanzu ba su iso ba ? " wata yar karamar dariya duk mutanan wajen su ka yi kafin Diya ya ce " mamie , mu ma duk mun matsu mu gan su " har ta bude baki za ta yi magana su ka jiyo karar jirgi a tare su ka kai kallon su wajen da su ka jiyo sautin su na fadin Alhamdoulilah cikin zuciyoyinsu a hankali jirgin nan ya sauka , ya tsaya ya na fuskantar motocin su sai da ya yi two minutes a haka kafin kofar jirgin ta bude a hankali a tare Malik da Inaya su ka fito da ga cikin jirgin Malik ya na dauke da Prince duk jikin shi ya yi sanyi allamun barci ya ke a tare duk su ka nufe su su na yi musu barka da zuwa , da sauri MALIKAT INAS ta kai hannu ta karbe shi nan ta ga ashe barci ya ke , amma duk da haka sai da ta karbe shi , MALIKAT AL'UMU kuma ta karbi Princess hannu Inaya da ga haka su ka shiga rungumar juna , specially Diya , da ya rike Malik sai da RIANNA ta shiga ce mishi ya sake mata dan uwa ita ma ta rungume shi , ita dai Inaya tun da ta rungume mama ba ta sake ta ba har kowa ya hakura ya bar ta dan sun San yadda kewar uwa ta ke da ga su ka shiga motocinsu su ka bar airport din su ka kama hanyar Daular Saudiya ko da su ka isa kai tsaye Diya ya wuce da Malik building din shi tare da Abdoul MALIKAT INAS kuma ta tafi part din su da Prince tare da MALIKAT AL'UMU da RIANNA da Tesnim Inaya kuma ta bi mama tare da Nesrine su ka nufi part din MALIKAT HOUDA tare da Junior ▪MALIK tsaye ya ke a cikin parlourn part din shi a floor na uku sai bin wajen ya ke da kallo kamar bakwon shi ya na a haka ya jiyo Muryar Diya a bayan shi ya na fadin " mu tafi ka yi wanka , ka huta , amma gaskiya abokina US ta zauna maka , ka na cen ka na shan dadinka ka kyale ni nan da aiki " wani dan karamin murmushi Malik ya yi ya na fadin " ai ni zuwan tsaye na muku , dan gobe zan yi gaba da Cutie " ya kai karshen ya na fara takawa ya nufi corridor cikin rudu Diya ke ce mishi " ban gane ? " ko sannu Malik bai ce mishi ba ya shige corridor sai da ya shiga sannan Diya ya juyo ya kalli Abdoul da ke tsaye gefe ya ce " har yanzu dai na miskilancin nan su na nan " wata yar karamar dariya Abdoul ya yi ya na fadin " ai miskilanci a jininshi ya ke , ba zai taba fita ba , ba banza Allah ya hada shi da wadda ba ta iya rufe bakin ta ba " " hmmmm , mu tafi mu ba shi wuri " Diya ya fada ya na nufar lift ba musu Abdoul ya bi bayan shi su ka baro part din , dan Diya nashi part din daban ya ke , ko so guda bayan tafiyar Malik bai taba shiga building din ba , saboda wannan building musaman na Malik nz , shi ya sa ya yi nashi part din daban , amma mai floor biyu , sai in Malik na shirin zuwa sannan ya ke sa a bude shi a gyara part din , amma floor na hudu sai Malik ya zo da kan shi ya bude shi dan babu wanda ya san ya ma a ka rufe shi bare a bude sai Malik , dan a ganin shi sirrin da ke cikin wannan floor na nashi ne shi kadai , saboda a nan ne ya ga dare mafi mahimanci a rayuwar shi , a nan ne ya zama cikaken mutum dan haka ba wanda ke da damar shiga floor din , idan kuma za su koma US ya sake rufe shi , bayan shi da Inaya ba wanda ya taba hayo shi , har prince kai tsaye Malik kuwa bedroom din shi ya nufa , ya na isa ya wuce kai tsaye Toilet sai da ya share good one hour a ciki kafin ya fito daure da towel a kugunshi ya na fitowa idanun shi su ka sauka saman ta , ta na zaune tsakiyar gado , ta jingina bayan ta a forehead din gadon ta na rike da wayar shi ta na latsawa wani cool murmushi ya saki kafin ya karaso wajen gadon , ya zauna a baki ya kai hannu ya kwace wayar shi ya na fadin " ta ya a ka yi ki ka san ina nan ? " ya kai karshen ya na ajiye wayar shi saman bedside drawer wani kyawatencen murmushi ta sakin mishi ta na fadin " tracker na saka maka a jiki, ba ka sani ba ? " daga mata gera guda ya yi ya na fadin " Oh , da gaske ? " " sosai ma kuwa " ta fada ta na kauda kai gefe a hankali ya matso , ya kai hannu ya janyo ta a hankali jikinshi , murya kassa kassa ya ce mata " kin zo ko a dai'dai lokacin da ya dace " " wane lokaci kuma ? " ta fada cike da shagwaba har da turo dan bakin nan nata a hankali ya kai bakin shi saitin kunnen ta ya yi mata rada wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta zagayo da hannayan ta a kugunshi ta kara shigewa jikinshi ta na fadin " kai dai ba ka gajiya baby , yanzu fa mu ka zo ka bari mu huta mana " " idan

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});