Chapter 12
Chapter 12
ajiyar zuciya ya sauke kafin ya nufi Aymane , shi ma Aymane da gudu ya nufo Malik sai dai kafin ya kai ga daga takobin shi , Malik ya juya ya ba shi baya ya caka mishi sword din shi a ciki har sai da ta fito mishi ta baya da sauri Malik ya juyo ya yi baya ya na kallon Aymane da ke zubar da jini ta bakinshi wata nanauyar ajiyar zuciya duk mutanan Malik su ka sauke MALIKAT AL'UMU da INAS su na yi wa Allah godiya cikin zuciyoyinsu da sauri Inaya ta mike tsaye ta na kallon Malik ta ce " ka cire mishi kai ! " ta fada da karfi har sai da hankalin kowa ya dawo gare ta Malik na jin hakan ya tuno abun da ta tabba fada mishi lokacin da ya ce wa Aymane su yi duel din na ya cire mishi kai ta haka ne kawai zai mutu tuno hakan ne ya sa shi nufar Aymane da sauri zai zame takobin shi sai dai kafin ya karaso ya ga Aymane ya zare takobin da kan shi ya tilla gefe ya na sakin murmushi " ka kashe ni , amma ba za ka iya ja da shi ba " Aymane ya fada jini na fitowa da ga bakin shi kafin Malik ya yi taku biyu , kawai ya ga skin din Aymane ta koma green scales na fito mishi kamar irin na maciji , idanunshi su ka koma irin na maciji bayan kalmar shahada ba abun da mutanan wajen da Malik su ke yi su na kallon Aymane da ya fara girma , ya na girma , ya na girma , ya koma dankareren maciji tsanwa shar , girman shi ya yi biyun macijin da Rouksar ta zama a word room wani irin razanannan kuka macijin nan ya yi tongue din shi na fitowa waje duk mutanan wajen sai da su ka saki kara , ma su tserewa na yi , ma su suma na yi MALIKAT INAS , MALIKAT AL'UMU da Rafik , RIANNA , Diya , bayan kalmar shahada ba abun da su ke yi da sauri General Abdallah ya kalli Sojojin shi da ke tsaye cen a geffen ya daga musu murya ya na fadin " Fire ! " da sauri Su ka fiddo gun su ka fara harbin macijin nan , amma ko ajikin shi , bullet din sai faduwa kassa su ke yi wutsiyar shi kawai ya sa ya buge duk sojojin da ke wajen su ka yi cen gefe su ka fadi shi dai Malik ya yi sumar tsaye bayan kallon macijin nan ba abun da ya ke yi , sai kalmar shahada da ya ke karantawa cikin zuciyar shi , ya na kallon macijin nan cikin ido dan shi ma macijin Malik ya ke kallon ya na tsaye a haka kawai ya ga........ ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ ( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : MEERAH ⚘🕊 【THE ROYALTY LOVE ❤🌹】 【 BOOK ________ 4 ❤✍💌 】 _______________________♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡♡______________________ { P A G E ________ 11 & 12 ✍💕🔥} ya na tsaye a haka kawai ya ga Inaya kamar ta fado da ga sama tsaye a gaban shi , kayan jikin ta duk sun koma baki kirin , gashin ta ya yi black sosai , ga shi kuma ya yi kwari kamar an yi kitso , idanunta sun koma bakake kirin ko digon fari babu , har wani bakin hayaki ke tashi da ga saman rigar ta da gashin ta , wani abun mamaki kuma cikin jikinta ya bace bat kamar ba ta taba yi ba a hankali Malik ya bude baki ya na shirin magana ya ga wani haske ya fito da ga jikin ta ya yi cen gefe dan nesa kadan wata irin muguwar bugawa zuciyar shi ta yi wata Inayar ce kuma daban , amma wannan kayan jikin ta duk farare ne , har gashin kan ta fari ne kal , idanunta sun koma farare kal har wani haske su ke yi kamar torch , ita ma dai cikin ta a shafe ya ke babu allamun pregnancy a tattare da ita cikin wani harshe da ban san irin shi ba mai sanye da bakaken kaya ta cewa dayar " Abyad ki koma , idan wani abu ya same ki dukka mu uku ba za mu rayu ba " girgiza mata kai Abyad ta yi ta na fadin " Aswad , ba za ki iya yin fada da shi ba ke kadai , ki bari na taimaka miki " " Ki fara fitar da Malik da ga wajen nan " Aswad ta fada gyada mata kai kawai Abyad ta yi , kafin ta tako da gudu ta nufo Malik da ya yi sumar tsaye , ta riko hannunshi ta bace bat tare da shi sai ga ta tsaya gaban su MALIKAT AL'UMU rike da Malik sakin hannunshi ta yi , ta na shirin juyawa ya riko hannunta ya na fadin " Cutie , kar ki tafi " a hankali Abyad ta juyo , ta kwace hannunta a hankali , wannan karan da harshen Hausa ta ce " kar ka damu ba abun da zai same ta , ka zauna a nan , idan wani abu ya same ka , ita ma za ta cutu " ta na gama fadar haka , ta yi taku uku baya , ta na fuskantar su , ta fara motsa lips din ta a hankali a hankali wani farin hayaki ya fara tashi tsakanin su , ta dago hannun ta , ta fara yin sama da shi , shi ma hayakin nan ya fara yin sama sannan ta daina motsa lips din ta , ta sauko hannun ta kafin ta juya da gudu ta na juyawa Malik ya tako da sauri ya na fadin " Cutie ! " , sai dai ya na iso wajen hayakin nan ya yi baya da sauri ya ji kamar ya bugi bango a rude ya tsaya ya na kallon hayakin nan , ya mika hannun shi , kawai sai ya ga ya tabo abu kamar ya taba bango cikin fitar hayaci ya fara kai wa hayakin nan bugu , ya na fadin " Cutie ! Cutie ! " da sauri Diya ya riko shi ya na fadin " Ka kontar da hankalin ka , ba abun da zai faru da ita bangaran Abyad kuwa , kai tsaye geffen Aswad ta dawo ta tsaya ta na fadin " ya za mu yi da shi ? " a hankali Aswad ta yi sama da hannu ta , sai ga wata katuwar Sword baka kirin ta fito a ciki , ba tare da ta kalli Abyad ba ta ce mata " kar ki damu , zan yi maganin shi " ta na gama fadar haka ta nufi macijin nan da gudu da sauri ya juyo da wutsiyar shi zai kai mata bugu , kawai sai ta bace bat sai ga ta tsaya a bayan shi , ba tsaya bata lokaci kawai ta caka mishi sword din hannun ta a baya wani irin razanannan kuka macijin nan ya yi , a dubu
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31