Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 18

Chapter 18

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,091 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

: MEERAH βš˜πŸ•Š 【THE ROYALTY LOVE β€πŸŒΉγ€‘ 【 BOOK ________ 4 πŸ“šβœπŸ’Œ 】 _______________________β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘______________________ ο½› P A G E ________ 15 & 16 βœπŸ’•πŸ”₯} dan jinkirtawa Diya ya yi kafin ya ce " tsinuwar macijiya ce a kan ahalin Abdoul Mujeeb , lokacin da mahaifin mu ya hau mulkin masarautar Ottoman ya yi kokarin kara fadada girman masarautar , akwai wani fili da ga bayan masarautar , kawai sai ya ce a sanyo shi cikin Daular , a yi sabin gineΒ² a cen , ashe wajen snake's nest ne , lokacin da ya samu labarin wajen gidan macizai ne kawai sai ya tura a kashe duk macizan , haka ko a ka yi , amma abun da ba su sani ba , sarauniyar macizan mayya ce , kafin ta mutu sai da ta tsinewa Ahalin Abdoul Mujeeb , duk yaran da zai haifa za su zo rabi maciji , rabi mutum , kuma haka a ka yi , ba Aymane kadai ba , duk yaran Abdoul Mujeeb mu na iya komawa wannan macijin da ka gani na koma yanzu , amma na Rouksar daban ne , dan duk lokacin da idanunta su ka koma na maciji a ka yi katari wani ya kalli cikin su , to sai ya koma status har sai ta yi mishi kiss sannan ya dawo dai'dai , shi ya sa ma mu ke kiran ta da Medusa , ina da shekara 17 na fara komawa wannan macijin , abun ya yi matukar ban tsoro , da na fadawa Daddy shi ne ya ke ban labarin yadda a ka yi na zama macijin , da na ji hakan kawai na ji na tsani masarautar , shi ya sa ma na daina zama cikin Saudiya baki daya , na koma UK da zama , idan na gaji na tafi DubaΓ― ko Jordan ko Asia , tsakanin wadanan gariruwan hudu na kammala karatu na , shi kuma Aymane nashi macijin daban ya ke shi ma , saboda shan jinin mutum ya ke , mutanan ma sai mata , ba yin da Daddy bai yi ba dan ganin Aymane ya daina shan jini amma ya kassa , har ya kai ya gogawa Rouksar shan jini , ba tare da sanin shi ba , ga shi kuma ya koyo yin tsafi , da ya ga abun ya fara gagara shi ne ya tura shi kassar Rouma wajen wani babban masanin tsafi dan ya cire wannan macijin da ke jikin Aymane , amma ya kassa asali ma tsafin shi sai karuwa ya yi , babu yadda ya iya ya sa mishi ido har ya girma a haka , ba zan maka karya ba , lokacin da Aymane ya yi kokarin kashe ka shekara bakwai baya , ina sane , saboda na zo wucewa na ji ya na maganar , dalilin da ya sa ma na shigo masarautar Saudiya a ranar dan na cece ka , amma ina shigar ta kai ne mutum na farko da na ci karo da shi , ba karamin sanyi na ji ba ganin ka a raye , shi ya sa ma na hakura na bi ka Nigeria , saboda ina tsoron Aymane ya cutar da kai idan ya samu labarin ka na raye , na san ka manta amma ni na sani , duk lokacin da ka je kai wa papi Ziyara a Daular Ottoman kai da Tesnim , sai Aymane ya yi kokarin kashe ka , amma bai taba yin nassara ba , akasin da a ka samu , duk lokacin da ka ke zuwa Daular ni ba na nan , shi ya sa ba ka san ko ni wanene ba ranar da mu ka hadu , tun lokacin da na sauke idanu saman Baby na san ta na da aljanu , na san kuma Malik ya shiga jikinta ya ce maka dole sai ka fara karaya tsafin Aymane sannan za ka iya kashe shi , ko kuma ka cire mishi kai , ni na san inda Aymane ya boye sihirin shi , amma ba zan iya fada maka ba , saboda a jikin RIANNA ya boye shi a ranar da a ka yi auren su , hakan na nufin sai ka kashe RIANNA , shi ya sa na ja bakina na yi shiru , bare kuma ba ni da tabbacin za ka yarda da ni , mistake daya a ka samu Aymane ya koma maciji a gaban ka , da ni ma ba zan fada maka ba saboda ya na daya da ga cikin abun da ba na son tunawa a cikin rayuwa , dalilin da ya sa ma na yi bincike a kan yadda zan cire macijin da ke jikina , kuma Alhamdoulilah ya na fita a hankali ta hanyar karatun kur'ani da sallar dare dan macijin ba ya son adini , da farko girman shi ya kai irin na Aymane , ka yi hakuri na boye maka wannan abun tsawon shekaru but i don't know how to explain you , i'm just afraid idan na fada maka ka ji ka tsane ni ba zan iya jure hakan ba , I'm so sorry " ya fadi na karshen kamar zai yi kuka sai da ya dan jinkirta kafin ya ci gaba da fadin " lokacin da a ce ka sha poison , lokaci guda na san da Rouksar ce , dan ita kadai ke da poison , ba rokon da ban yi mata ba a kan ta ba ni antidote , ka yi hakuri har alkawari na yi mata idan ka tashi za ka aure ta , amma fir ta ki , ta na cewa idan ta ba ni kashe ta zai yi , na tambaye ta wa amma ta kassa fada min saboda ya rufe bakin ta da tsafin shi , sa'ar mu guda aljanun Baby sun tashi , ba dan haka sai dai ka mutu dan antidote din poison din ta , yawunta ne that's why ma ka ga mahaifinmu bai wani damu da mutuwarta ba saboda ya san wacece ita , haka ma Aymane ya yi kokarin ya ja mishi birki lokacin da ya hau kujerar amma ya yi kokarin kashe shi , shi ya sa ya ja bakinshi ya yi shiru dan ba abun da zai iya yi , ka yi hakuri ahalina ya cutar da kai dayawa , please ka samu wani gurbin a zuciyar ka ka yahe min , na san ko na mutu ruhi na ba zai samu salama ba idan ban fada maka gaskiya ba " wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya mike tsaye , ya na kallon Diya da ya tsare shi da ido ya na hawaye a hankali ya tako gaban shi ya tsaya , sannan ya mika mishi hannu wani cool murmushi Diya ya saki kafin ya dago hannun shi a hankali ya daura saman na Malik kafin ya mike tsaye ya na mikewa tsaye Malik ya kai hannu ya goge mishi hawayen shi ya na fadin " ni wlh na zata wata babbar magana ce za ka min , kawai dan ka yi zaune ka min kuka ne , ko dadi ya yi maka yawa ne ? " " ta ya za ka min irin wannan maganar bayan

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});