Chapter 17
Chapter 17
da Allah Nawfel komawa za ka yi , tun da komai ya wuce ka zauna cikin familyn ka mana " a hankali ya tako wajen sofar ya zauna geffen ta murya a sanyaye ya ce " momy , ba zan yi miki karya ba , these months that I spent there were the best of my entire life, I felt free, without any pressure, just her and me , na ji dadin zamana a cen fiye da komai , please kar ki ce za ki tsayar da ni , i promise duk bayan sallar Azumi za mu dinga dawowa mu yi babbar sallat a nan , just let me go please " shiru MALIKAT AL'UMU ta yi ta rasa abun da za ta ce mishi , ita ta na farin cikin komai zai dawo dai'dai , amma ya ce zai koma , zai sake barin su a hankali ta sauke ajiyar zuciya kafin ta ce " kujerar Malik kuma fa ? wa zai hau ta yanzu ? " " Diya " ya fada a takaice " ka sani Diya ba zai iya hawa kujerar nan ba , in da ma a ce Abdoul ne da zai iya hawa " " na sani momy , amma shi za a nada , dan na san Bayan shi babu wanda zai iya rike min ahalina , na san zai kula da masarautar nan kamar yadda ni zan kula da ita , na yarda da Diya fiye da rayuwata , ba dan shi ba da yanzu ban san inda zan tsinci kai na ba , ba dan shi ba da ba zan taba haduwa uncle bare har ya ba ni auren Cutie , duk wani abun al'heri da ya same ni cikin rayuwata shi ne sila , shi ya sa na yarda da shi fiye da rayuwata , he is my best and ONLY friend's , He is my Brother not my Cousin , dan haka ya na da ikon hawa kujerar Malik " wani dan karamin murmushi MALIKAT AL'UMU ta saki kafin ta ce " ka tabbatar shi ne abun da ka ke so ? " " na tabbatar momy " ya fada kai tsaye " shikenan , amma kar ka fadawa kowa maganar nan , har ranar nadin " " okay momy " ya fada ya na mikewa tsaye da sauri MALIKAT AL'UMU ta ce mishi " ina kuma za ka tafi ? " " ina son na ga babyna kafin mu tafi mosque lokacin sallat ya yi " da to kawai ta amsa , da ga haka ya sa kafa ya fice part din har ya nufi hanyar word room a ka fara kiran sallat , kawai sai ya juya ya nufi mosque dan ya yi sallat bayan sun yi sallat , Diya ya ja hannunshi ya nufi part din shi da shi , sai tambayar shi Malik ya ke me ya faru , ya sake shi amma ko sauraron shi Diya ba ya yi , su ka shiga part din shi sai da su ka shiga cikin dayar bedroom sannan ya saki hannunshi , ya meda kofar ya rufe , ya saka mata security Malik na ganin haka ya ce mishi " wai lafiya ka kawo ni nan , ina son na je na ga babys di na , ka wani kawo ni nan har da rufe kofa " cikin sanyin murya Diya ya ce mishi " please , ka tsaya akwai wata magana da na ke son mu yi " wani dan karamin tsaki Malik ya yi ya na fadin " magana ba za ka iya yi min ita ba a mosque sai ka kawo ni har nan ? , wlh ba ka da hankali , ban hanya na wuce " ya fada ya na nufar kofar dakin da sauri Diya ya riko hannunshi ya janyo shi bayan da karfi ya na fadin " please Nawfel , ka tsaya wlh maganar mai mahimanci ce , don girman Allah ka tsaya " ya fada ya na marairaice fuska wani dan karamin tsaki Malik ya yi ya na fadin " okay , ina jin ka , amma yi sauri " wani dan karamin murmushi Diya ya yi kafin ya gyada mishi kai a hankali ya lumshe idanunshi a fara motsa lips din shi kamar ya na karanto wani abu a hankali skin din shi ta fara sauya launi , ta koma wani launi shi ba green ba shi ba yellow ba , scales su ka fara fito mishi , nan take skin din shi ta koma irin ta maciji , a dubu dari Diya ya bude idanun shi dai'dai lokacin da ya koma wani babban maciji , amma yanayin jikin shi da tsawon shi duk dai'dai yanayin jikin shi Diya ne da tsayin shi , sai wutsiyarshi a baya ta na motsi " inallillahi wa'ina illaihi raji'un " Malik ya fada da karfi har ya na yin baya ya fadi , ya na zaro idanu ya na kallon macijin da Diya ya koma zuciyar shi na duka uku uku , ganin abun ya ke kamar a mafarki a hankali ya bude baki lips din shi har kerma su ke ya na fadin " Diya ! " ya furta lokaci guda ya na gama fadar haka ya ga A hankali skin din macijin nan ta sauyawa , sannu sannu har ya bace Diya ya dawo tsaye a hankali ya zauna a kassa ya yi irin zaman cin tuwo ya sunkuyar da kai murya a sanyaye ya ce " na je na kira ka mu tafi mosque dan lokacin sallat ya yi , amma ban gan ka ba a part din MALIKAT HOUDA , shi ne da na tambaya , a ka ce min ka na part din MALIKAT AL'UMU , na je part din zan shiga na jiyo Muryarka ku na magana da MALIKAT AL'UMU , na ji abun da ka fada mata , ka yi hakuri na boye maka wannan sirrin tsawan shekaru , just na rasa yadda zan iya fada maka ne , na san duk lokacin da ka san ya na ke ba za ka taba ci gaba da yarda da ni ba , that's why ya bunne abu na , amma bayan na ji abun da ka fadawa MALIKAT AL'UMU shi ne na yanke shawarar fada maka " " ya Salam " Malik ya fada cikin zuciyar shi , ka fin ya bude baki ya ce " kai , kai ma tsafi ka ke yi ? kamar Aymane ? " da sauri Diya ya dago kai , nan Malik ya ga hawayen da ya ke zubar wa da sauri ya ce mishi " No , ba na tsafi , duk zaman da mu ka yi da kai ka taba gani na na yi wani abu mai kama da tsafi ? " a hankali Malik ya girgiza mishi kai allamun a'a kafin ya ce " ta ya a ka yi ka ke zama wannan abun kai ma , kenan ka na sane da Aymane shi ma ya na zama hakan ? " ❤⚘ EXILED PRINCE ⚘❤ ( LOVE MEETS POWER ) 👑🔥 ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31