Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,096 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

kontar da ita saman gadon jinya dai'dai lokacin da doctor ta shigo ta na fadin " za ka iya fita " ta fada dai'dai lokacin da wasu nurse guda biyu su ka shiga da gudu har ya juya zai fita ya ji ta riko hannunshi da sauri ya juya ya na kallon ta , a hankali ta girgiza mishi kai hawaye na zubo mata ya na shirin yi mata magana doctor ta ce " please ranka shi dade ka fita " ko sauraron ta ba ya yi ya dawo wajen Inayar shi ya sunkuyo ya ce mata " ki kontar da hankalin ki ba abun da zai faru , kin ji ? " ya na gama fadar haka ya jiyo Muryar doctor ta na fadin " ka fita don Allah " cikin bacin rai ya dago ya ce mata " babu inda zan je , ku yi aikin ku kawai , idan ba za ki iya ba ki fice min da ga nan " ba dan ta so ba ta ja bakin ta ta yi shiru wata yar karamar kara Inaya ta saki , ta na kuka ta ce " kar ka saki hannuna don Allah " a hankali ya dago hannunta da ke cikin nashi ya manna mishi kiss ya na fadin " ba abun da zai faru , ina tare da ke " ba ta amsa mishi ba kawai ta saki kara ta na lumshe idanun ta har wani dago kai ta yi kafin ta koma , ga wata uwar zufa da ta karayo mata , kamar an watsa mata ruwa cikin sanyin murya doctor ta ce mata " ki kontar da hankalin ki , ki dinga jan nunfashi a hankali , ki na saukewa " ba musu Inaya ta ja wani dogon nunfashi har kirjin ta na yin sama sai dai maimakon ta sauke kawai sai ta saki kara ta na kara matse hannun Malik a cikin nata da sauri ya daura dayan hannun nashi saman kumatun ta ya na fadin " Cutie , Dube ni kin ji ? " ba musu ta juyo ta kalle shi idanun ta duk sun yi ja sai hawaye ta ke ta marairaice fuska da sauri ya sauke forehead din shi saman nata ya na kallon cikin idanunta , murya cen kassan makoshi ya ce mata " ba abun da zai faru da ke okay ? " da sauri ta katse shi da cewa " yaya Zayd mutuwa zan yi , da zafi " ta kai karshen ta na kara sautin kukan ta cikin sanyin murya ya ce mata " ba abun da zai same ki , ki daina cewa mutuwa za ki " ya fada kamar zai yi kuka har wasu hawaye ke zubo mishi wanda shi kan shi bai San da su ba karan farko da na ga hawayen Malik , ko a lokacin da Daddyn shi ya mutu bai yi hawaye ba wata yar karamar kara Inaya ta saki ta na janye forehead din ta , ta kauda kai gefe , da karfi ta cije lips din ta kamar za ta fashe su da sauri Malik ya kalli doctor ya ce " wai har yanzu ba ku fiddo mata wannan abun ba ? " " don't worry , ga kanshi nan na fitowa , ranki shi dade , last working , ki turo da karfi " doctor ta fada ta na kallon Inaya da sauri Inaya ta shiga girgiza mata kai idanunta a lumshe da sauri Malik ya daura hannunshi saman kumatunta , ya juyo da face din ta , ya sauke forehead din shi saman nata murya kassa kassa ya ce " okay , zan kirga zuwa uku , da ga nan ki ka dogon nunfashi ki sauke , kin ji ko ? " a hankali ta gyada mishi kai allamun Eh " Okay , one , two , three let's go " wani dogon nunfashi ta na sakin wata siririyar kara karfin ta sauke wata nanauyar ajiyar dai'dai lokacin da kukan baby ya gauraye wajen wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke ya na fadin " Alhamdoulilah " cikin zuciyar shi har lumshe idanunshi ya yi ya na sakin murmushi kamar shi ya yi aikin ya na bude idanunshi ya ga Inaya ta yi tsit kamar an yi ruwa an dauke Dum ya ji zuciyar shi ta buga da karfi , a dubu dari ya kai hannu ya fara jijiga ta ya na fadin " Cuti , Cutie , please ki bude idanunki , Cutie , please ki bude kar ki min haka mana " da sauri Doctor da ke rike da babynsu ta karaso wajen ta na fadin " ka kontar da hankalinka , ba mutuwa ta yi ba , suma ce ta yi " ta na gama fadar haka ya ga ta sauke babyn hannun ta saman kirjin Inaya ta kontar da kan shi saitin zuciyarta wani irin sanyi ne ya ji lokacin da idanunshi su ka sauka saman babyn , kyakyawa da shi fari kal kamar ka taba jini ya fito har wani ja ya yi , ya na kama tak da Malik kamar an tsaga kara , sai dai idanun shi a rufe su ke sai in ya bude mu ga kalar su da sauri Nurse din da ke tsaye a baya ta ce " Doctor , ina ga Twins ne " cikin rudu Doctor ta ce " Twins kuma ? " ta na gama fadar haka ta dauke babyn ta juya ta mikawa nurse din ai ko da gaske Twins ne dan ga kafafun shi nan su na son fitowa , ya kuma a ka yi haka bayan baby ta kai ya ke fara fitowa da sauri Malik ya ce mata " Doctor me ya faru ? Twins ne ? " Doctor ba ta ce mishi komai ba ta na aikin ta kawai sai ganin ya yi ta na rike wani babyn a hannun ta amma ko motsi ba ya yi Dum ya ji zuciyar shi ta buga , kenan da gaske Twins ne ? ga shi shi ma namiji ne slowly Doctor ta dago ta kalli Malik , cikin raunin murya ta ce " i'm sorry bai zo da rai ba " ta fada dan ta san ba karamin abu zai sa baby ya fito ta kafafu ga shi ko motsi ba ya yi hakan na nufin ya jima da ya mutu a cikin ta ba ta sani ba Dum Malik ya ji zuciyar shi ta buga har wani lumshe idanu ya yi ya na fadin " inallillahi wa'ina illaihi raji'un " kassa kassa ta daya bangaran ya ji dadi da ba ta cikin hayacinta ta haihu da yanzu in ta ji babyn ta guda ya mutu zuciyar ta bugawa kawai za ta yi , a hankali ya sauke ajiyar zuciya kafin ya dago ya mikawa Doctor hannayan shi a kan ta ba shi babyn ba musu ta daura mishi babyn a hankali ya dago shi , ya yi mishi addu'a sannan ya yi mishi kiss saman forehead din shi ya na a haka kawai ya jiyo sautin kukan wani babyn , cak ya tsaya ya na zaro idanu , ga shi dai sautin ba ya kama da na farko

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});