Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 5

Chapter 5

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,105 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

sai Rafik su na fita Shi ma Malik ya juya ya fice fadar , ya na tafiya kamar zai tashi sama hannun shi na zubar da jini , ga idanun shi duk sun yi ja da allamun ya na cikin bacin rai kai tsaye part MALIKAT HOUDA ya nufa , babu ko sallama a bakin shi ya shigo parlourn nan ya tardo su duk su na zaune ban da Inaya da mama da su ka shiga Bedroom duk su na ganin shi kowane ya saki wani kyawatencen murmushi , MALIKAT INAS har da hawaye har sun tashi za su nufe shi , su ka ga Diya ya fado mishi a baya ya rungume shi ya na fadin " ni dama na san za ka dawo , tabbas za ka dawo , ai dama damuna a lokacin da a ka fi bukatar ta ta ke samuwa , kamar wata ka ke a sararin samaniya haskenka ya na mamaye duk duniya , na ji dadin ganin ka abokina , I have really missed you " ya na gama rufe bakin shi , Malik ya kai hannu cikin zafin nama ya medo Diya gaban shi , ya dunkule hannu ya kai mishi wani mugun bugu a face har sai da ya fadi kassa a tare duk mutanan wajen su ka razana , Nesrine har da sakin kara , lokaci guda babyn ta ya saki kuka kamar ya san abun da ke faruwa cike da bacin rai Malik ya ce mishi " ka na sane da abun da ke faruwa amma ka ki fada min , why ba za ka kire ni ka fada min halin da ahalina su ke cike tun kafin abun ya tsananta ? why Diya ? da yanzu RIANNA ba ta kire ta fada min ba shikenan haka Saudiya za ta dongwama hannun wacen azzalumin dan uwan naka " a hankali Diya ya dago kai ya mike tsaye , ya na fadin " lokacin da na samu labarin abun da ke faruwa , sai da na kira ka , amma ba ka dauki wayata ba , na tura maka text a na bukatar ka a Saudiya , amma ba ka min reply ba , asali ma blocked di na ka yi , shi ya sa na ja bakina , na yi shiru ba kyale ka , na tattare familyn ka na tafi da su Qatar , duk abun da ya faru laifin ka ne , da tun farko ba ka tafi ba da duk wannan ba ta faru ba " ya fada cikin bacin rai shi ma gaskiya Diya ya fada , duk abun da ya faru laifinshi ne , da tun farko ya tsaya , ya yaki Aymane da duk wannan abun ba ta faru ba ya na gama fadar haka ya fara jiyo kukan baby wani dan karamin tsaki Diya ya ja ya na fadin " dubi don Allah ka saka shi kuka " ya kai karshen ya na juyawa ya nufi Nesrine , ya kai hannu ya karbi babynshi , sannan ya juyo ya dawo gaban Malik ya shiga jijiga shi ya na fadin " Shiiiiiiiiii , calm down my baby ba abun da ya faru " a hankali ya dago kai ya kalli Malik ya na murmushi ya ce " tun kafin a rigani , bari na gabatar maka da Nawfel bin Abdoul Mujeeb , my baby " lokaci guda idanun Malik su ka ciko da ruwa , har wata nanauyar ajiyar zuciya ya sauke ya na kallon babyn babu ko kiftawa Diya na jin yadda ya sauke ajiyar zuciya , ya saki wani kyawatencen murmushi ya ce " ba za ka rike shi ba ? " ya fada ya na mika mishi babyn a hankali Malik ya dago hannayanshi har kerma su ke yi ya kai zai karbi babyn kamar wanda ya tuno wani abu , lokaci guda ya juya ya fita da gudu a tare su ka kalle shi har ya fita sannan Diya ya kalli babyn hannun shi ya ce " Oh sorry my baby , yanzu ya dawo kai da takwaran ka guda , duk gudun ruwanshi sai ya dawo ya dauke ka " sa ga haka ya juya ya koma geffen Nesrine ya zauna su ka shiga rarrashin babyn su haka kowa ma ya koma ya zauna , ya yi zugum sun rasa abun yi , wannan tashin hankali da me ya yi kama , su dan ba su ma ji abun da Aymane ya fada da sai sun dinga sumewa ▪AYMANE cike da bacin rai ya nufi part din Malik , kai tsaye a floor na biyu ya nufa dan a nan RIANNA ta ke , shi kuma tare da Hafsat a floor na uku , dan tun zuwan shi part din bai taba hawa floor na hudu ba , dan ya na rufe kuma babu wanda ya San ta yadda a ka rufe shi bare a bude shi babu ko sallama ya shigo parlourn ya kwallawa RIANNA kira kamar murya shi za ta fado da gudu RIANNA ta fito da ga Corridor , ta na tafe ta na ingishi da allamun kafar ta na ciwo , ga fuskar ta duk ta yi ja , ta na sanye da wata gown pink color ko veil ba ta da a kanta kai tsaye gabanshi ta karaso murya har kerma ta ke ta ce " ga ni , ka na bukatar wani abu ? " tsaya wa ya yi ya na kallon ta babu ko kiftawa sai da ya dauki one minute ya na kallon ta kafin ya daga hannu ya wanke ta da wani gigitacen mari har sai da ta saki kara ta fadi kassa cikin bacin rai ya tsuguna ya kai hannu ya shako wuyan ta ya na fadin " bayan ke na san babu wanda zai yi wannan aikin , why ? azabar da na ke miki ba ta ishe ki ba sai da ki ka yi abun da zai sani na kashe ki ? why za ki sa dan banzan dan uwanki ya dawo , har ya yi kokarin kwace min kujerar Malik ? " tattara duk karfin ta RIANNA ta yi , ta sa hannayan ta dukka biyu ta ture shi ya fadi baya da sauri ta mike tsaye ta na sakin murmushi ta na fadin " Akhie ya dawo ? " ta kai karshen hawaye na zubo mata ta na gama fadar haka ta ji hannun Aymane ya damko wuyanta ya na fadin " ya dawo , amma ba za ki samu ganin shi ba , da ga nan gawar ki ce za ta fita da ga part din nan , duk wanda ya yi kokarin shiga tsakanina da kujerar Malik , sai na ga bayan shi , ki jira shi ma dan uwan naki , zai tarda ki ranar Friday " " ka sake ni " ta fada murya a disashe dan a rarrabe ma ta fiddo hariffan ya na shirin magana ya ga an riko hannun shi a hankali ya juya ya ga ko wanene , kai tsaye cikin idanun Malik nashi su ka sauka ba karamar razana ya yi ba ganin wadanan hazel eyes din nashi , ga shi sun yi jazir dan

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});