Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,062 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

" ta fada cike da shagwaba har da turo baki " karbi , ba za mu iya rigimar ki ba , ai dama dole ta ce sai ta rike shi , ba mijin ta ba ne " MALIKAT HOUDA ta fada ta na daura Baby saman hannayan Inaya da sauri Nesrine ta ce mata " yi a hankali kar ki murde min kan baby " hararrar ta Inaya ta yi ta na fadin " to ina ruwan ki , ai ni ma na kusa samun nawa babyn " ta kai karshen ta na murguna mata baki a hankali Nesrine ta karaso wajen ta , ta na fadin " ban babyna tun da haka ne " ta kai karshen ta na mika mata hannu da sauri Mama ta ce mata " Nesrine wai biye mata za ki yi , kin fi san halin ta " hararrar Inaya Nesrine ta yi kafin ta koma gefe ta zauna ta na tsuke fuska a tare kowa ya koma ya zauna kafin MALIKAT INAS ta ce " baby , ina mijinki ya yi ? ba tare ku ka zo ba ? " a hankali Inaya ta dago kai ta kalli MALIKAT INAS ta ce " a tare muku Ammie , ya ce akwai inda zai je yanzu ya dawo " a tare duk su ka yi hamdallah , sannan MALIKAT AL'UMU ta ce " baby , ya kamata ki je ki huta ko ? " noke mata kafada ta yi ta na fadin " ni tare da babyna zan tafi " da sauri Nesrine ta ce mata " wane babyn ? kam , wlh tun wuri ki sauke idanun ki da ga saman babyna , in ba haka ba na yi miki duka kawo ruwa " cikin nitsuwa Tesnim ta ce mata " Malik ko ya cire miki kai , gwara ki bi ta cikin ruwan sanyi ku rabu lafiya , dan in ta ce ta na son babyn nan ko mutuwa za ki ba abun da zai raba ta da shi " marairaice fuska Nesrine ta yi ta na shirin magana , ta ga Inaya ta miko mata babyn ta na fadin " amshi , barci na ke ji " da sauri Nesrine ta kai hannu ta karbi babynta ta na karba Inaya ta mike tsaye a hankali , ta na dafe da cikinta , ta ce " mama , barci na ke ji " ta kai karshen cike da shagwaba wani dan karamin murmushi ta saki ta na kallon ta , yau dai ga autar ta da ciki har ya kai watan haihuwa , ga kuma Nesrine da babynta , saura na Abdoul kadai ta ga burin ta ya cika , ga shi ko ta fara jiyo qamshin kamar Tesnim na da ciki a hankali ta mike ta nufi Inaya ta riko hannunta , ta na fadin " mu je ki yi wanka ki konta ki huta , Nesrine kawo kayanta bedroom di na " " bari zan kai " Tesnim ta fada , ta na mikewa ta nufi trolley din da Azim ya ajiye a wajen ta bi bayan su mama da su ka shiga corridor ( πŸ€”πŸ€” mama ba ki yi karya ba fa , ko ni na ga allamun ciki a jikin Tesnim , 🀣🀣🀣 ) ❀⚘ E X I L E D P R I N C E ⚘❀ πŸ”₯πŸ‘‘ ( LOVE MEETS POWER ) πŸ‘‘πŸ”₯ ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : MEERAH βš˜πŸ•Š 【THE ROYALTY LOVE β€πŸŒΉγ€‘ 【 BOOK ________4 πŸ“šβœβ€ 】 _______________________β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘β™‘______________________ ο½› P A G E ________ 3 & 4 βœπŸ’•πŸ”₯} β–ͺMALIK AYMANE zaune ya ke saman kujerar shi ta Gold ya na rike da wayar shi ya na latsa , haka zalika duk mutanan wajen kowa na harkar gaban shi , sai hira su ke yi su na dariya su na a haka Meli ya shigo da gudu babu ko sallama ya nufi Aymane da gudu , kai tsaye wajen kunnen Aymane ya nufa ya yi mishi rada a dubu dari Aymane ya mike tsaye har sai da ya saki wayar shi ta fadi kassa a tare duk kowa ya juyo ya na kallon Aymane da ke faman zaro idanu baki sake har su na hada baki su na tambayar shi lafiya ba su kai ga gama rufe bakunansu ba , su ka ga Aymane ya kai hannu ya damko wuyan Meli ya na fadin " karya ka ke , ba zai taba dawowa ba " murya a disashe Meli ya ke fadin " ranka shi dade , ba karya na ke ba , da ido na na gan shi zai shiga part din MALIKAT HOUDA " cikin bacin rai Aymane ya tura Meli baya har sai da ya fadi ya na shirin magana idanun shi su ka sauka cikin na Malik , ya na tsaye bakin kofar shigowa Fadar ya rike hannayan shi a baya a tare kowa ya mike tsaye ya na kallon Malik baki sake , wasu zuciyoyin su na bugawa cikin bacin rai Aymane ya ce mishi " me ka ke yi a nan ? " a hankali Malik ya daga kafa ya fara takawa ya karaso tsakiyar fadar ya na fadin " na zo karbar abu na , dama aro ne na ba ka " wata shegiyar dariya Aymane ya yi kafin ya koma saman kujerar Malik ya zauna , irin zaman nan na qasaita ya ce " ko da HICHAM BIN JAABAR ne zai fito da ga cikin kassa , ba isa ya sauke ni da ga saman kujerar nan ba , bare kai ragon banza " cikin bacin rai Malik ya ce mishi " kar ka kuskura ka kira sunan mahaifina " " na kira , na kira me za ka yi ? ,ko ba ka son na fadi sunan wanda ya haifi lusarin namiji kamar ka ? tun kafin na sa a cire maka kai , ka fice min da ga fada " a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya kafin ya ce " Aymane , tun ina yi maka cikin ruwan sanyi , ka sauka da ga kujerar nan " wani makirin murmushin geffen fuska Aymane ya saki , kafin ya juya ya kalli wani dogari da ke tsaye bakin kofar fadar , da hannu ya mishi allamun ya cirewa Malik kai ba musu dogarin nan ya tako gadanΒ² ya na zaro takobi wai cire kan Malik lokaci guda Malik ya kai hannu baya ya fido gun ya juya ya harbe dogarin nan tsakiyar kai , nan take ya fadi kassa matace ba karamar razana Aymane da mutanan fadar su ka yi ba a hankali Malik ya juyo , ya saita kan Aymane ya na fadin " idan na ga dama , move guda zan yi na aika inda ka aika mahaifina , amma zan ba ka damar ci gaba da rayuwa , ka sauka da ga kujerar nan " cikin bacin rai Aymane ya mike tsaye ya na fadin " ba ka da ikon ce min na sauka da ga saman kujerar nan , kai da kanka ka bar ta , kowa ya na shaidar ka hakura da kujerar nan a bisa tsarin

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});