Chapter 10
Chapter 10
da na ce " a dan razane Ya ce mata " mama , ni wlh wannan abun duk ya fi karfin tunani na kawai ina shanye wa ne " a hankali ta gyada mishi kai kafin ta ce " na sani kar ka damu za ka iya tafiyar ka " ba musu ya fara takawa ya nufi kofar fita part din ya yi dan nisa ya jiyo Muryar mama ta na kiran shi cak ya tsaya ya juyo a hankali ya na tambayar me ya faru sai da ta saki wani dan karamin murmushi kafin ta ce " akwai sakon da malam ya ba ni na fada maka amma kullum sai na manta " " wani sako kuma mama ? " " ya ce ya gode da amanar shi da ka rike , ya na matukar alfahari da kai kuma ya na rokon Allah ya sa ka samu abun da ka ke so tare da matar ka ya na fatan za ku samu zuri'ar da za ku yi alfahari da ita kamar yadda ya ke alfahari da ku " shi dai kawai ya tsaya ya na kallon ta ya ma rasa me zai ce mata , kawai ya gyada mata kai kafin ya juya ya fice parlourn ya na juya abun da ta fada mishi cikin kwakwolwar shi ya na fitowa kai tsaye hanyar garden ya nufa , ya na zuwa ya tardo Diya zaune shi kadai kamar aljani babu ko tsoro Malik ya karaso wajen shi ya zauna ya na fadin " me ka ke yi a nan ? ina ka baro babys din ka ? " wani dan karamin murmushi Diya ya saki kafin ya ce " sun yi barci shi ya sa na fito na dan huta , takwaran naka mugun jaraba ce da shi sai mutane sun yi kwana ya tashe su da kuka " " uhm " Malik ya fada kafin ya lumshe idanunshi ya tafi duniyar tunanin shi kallon shi Diya ya tsaya ya na yi ya na sakin wani dan murmushi cen kuma sai ya ce " ka sani na yi kewar ka sosai , kullum in na yi sallat sai na saka ku kai da baby cikin addu'a , na godewa Allah da babu abun da ya same ka " ba tare da ya bude idanun shi ba ya ce " ni ma na gode da ka ceci ahalina a lokacin da su ka fi bukata ta , na san da ban tafi ba da duk wannan abun bai faru ba , wlh na yi nadamar tafiya " " no , kar ka yi nadamar lokacin da ku ka samu na farin ciki kai da ita , na san da ka san hakan za ta faru ba za ka tafi ba , amma tsotsayi ne , in ya wuni ba zai kwana ba , haka Allah ya rubuta za ta faru , kuma ta farun ni dai kawai fata na Allah ya sa ka yi nassara " " ko ban yi nassara ba don Allah ina son ka koma Qatar da family na , specially Cutie da Babyn mu , na bar maka amanar su don Allah kar ka bari wani abu ya same su ko da ba na raye " da sauri Diya ya ce mishi " in sha Allah kai za ka yi nassara , Allah ya na tare da ma su gaskiya , ba zai bari zalunci ya yi nassara ba " shi da Malik ya yi shiru bai ce komai ba amma har cikin zuciyar shi ya na fargaba a je bai yi nassara ba , shi ba ta saudiyar ya ke ba ta Cutie din shi ya ke , yanzu a ka je ya mutu ya za ta yi , babu wanda zai kula da ita da babyn su ya yi nisa duniyar tunanin shi ya jiyo Muryar Diya ya na fadin " ka san General Abdallah har US ya je neman ka ? " slowly ya bude idanun shi ya kalli Diya ya na daga gera ya ce " ya a ka yi ya san ina US ? " " ni na fada mishi , har General din US army General Aylan Jalaludeen su ka hada kai dan neman ka , musaman General Aylan ya ba da tukuyicin one million of American dollars ga duk wanda ya gan ka , amma shiru " cikin nitsuwa Malik ya katse shi da cewa " wait , General Aylan fa ka ce ? ina General Abdallah ya san shi ? " " ni ma ban sani ba , but ya ce mahaifin shi ya sani a DubaΓ― shi ya sa ya yarda ya taimaka wajen neman ka " " Diya , na hadu da General Aylan , har mu ka yi hira da shi " dan zaro idanu Diya ya yi ya na fadin " ban gane ba , ka hadu da shi kuma bai fada maka a na neman ka ba ? " shiru Malik ya yi dan ba shi da amsar da zai ba shi , kenan Aylan ya na sane a neman shi a Saudiya amma bai ce mishi komai ba , ta wani bangaran ta sanadiyar Aylan ne ya samu ya rage zafin da ya ke ji cikin zuciyar shi har ya karbi babyn shi , to why bai fada mishi abun da ke faruwa ba ? π€π€ NI MA ABUN NAN YA DAURE MIN KAI , YA NA SANE KUMA YA YI SHIRU BAI CE KOMAI BA ? π€π€ su na zaune a haka kawai su ka ga wata mota baka kirin ta nufi hanyar fita masarautar a tare duk su ka tsare motar da ido har sai da ta fita sannan Diya ya kalli Malik ya ce " Malik , Aymane ne fa , ina za shi je cikin wannan daren ? " cikin ko in kula Malik ya ce " shi ya sani " " a ka je wani abu kuma ya ke shirya wa ? please tashi mu bi bayan shi " " no , kyale shi , duk abun da ya shirya shi dan cutar da ni Allah ba zai bari ya yi nassara ba , kyale shi kawai " " amma M...... " bai kai karshen maganar shi ba Malik ya katse shi ya na daga mishi hannu allamun ya yi shiru ba musu Diya ya ja bakin shi ya yi shiru amma cikin zuciyar shi ya na jin ba abun kirki ba ne Aymane ke shirin yi ba , in abun kirki ne why zai fita a irin wannan lokacin ? sai dai kawai na ce Allah ya tsare Malik da ga sharin Aymane β€β EXILED PRINCE ββ€ ( LOVE MEETS POWER ) ππ₯ ( A heart touching love story , Romance , injustice & destiny ) STORY & WRITTEN BY : MEERAH βπ γTHE ROYALTY LOVE β€πΉγ γ BOOK ________ 4 πβπ γ _______________________β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘β‘______________________ ο½ P A G E ________ 9 & 10 βππ₯ο½ βͺAYMANE πΊ Tuki ta ke yi cikin nitsuwa da ga gani akwai abun da ya shirya ya yi wajen one hour ya na wannan tafiyar kafin ya iso wajen wani kasurgumin Daji , babu motsin mutum bai rai sam sai dai tsintsaye da
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31