Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 2

Chapter 2

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,114 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

ya yi wa gateman magana kafin ya juya ya nufi wajen driver ya shiga ya tada motar kai tsaye ya nufi airport su na isa , su ka shiga private jet din shi , lokaci guda Jet din ya daga ya nufi kassar Saudiya ▪AFTER SOME HOURS ▪MASARAUTAR SAUDIYA ❤ Misalin karfe 9 na safe , jirgin su ya sauka a kassar Saudiya tun da ya shigo kassar ya ga komai ya sauya mishi kamar ba Saudiyar da ya sani ba bai gama shan mamaki ba sai da ya isa bakin kofar Daular Saudiya a nan ya ga wasu status guda biyu na lions sun bude bakunansu , ga wasu Sword biyu gaban kawuna su , a takaice tambarin Daular Ottoman ne a kafe bakin kofar Daular Saudiya da ga gani kuma na zallar gold a haka Malik ya danne abun cikin zuciyar shi ya shiga Daular nan ya tabbatar da cewa Eh Aymane ba Al'heri ya ke shukawa ba , dan duk Daular ta ruguje garden din ta ya bushe kamar ba a taba yin ciyayi a wajen ba , duk ginin sun kwararabe da ga gani ba a kula da su a hankali Inaya ta tabo hannun shi ta na cewa " yaya Zayd , an ya nan gidan mu ne ? ba ka yi batan kai ba ? " murya a sanyaye ya ce mata " No my Cutie , ban yi batan kai ba , in sha Allah komai zai koma kamar da farko " ba ta ce mishi komai ba ta tsaya ta bin wajen da kallo ga jikin ta ya yi mugun sanyi duk inda motar su ta wuce sai an tsaya a na bin ta da kallo Malik kuwa kai tsaye part din MALIKAT HOUDA ya nufa ya yi parking din motar bakin kofar shiga part din ya na yin parking ya kashe motar ya kalli ta cikin glass din motar ya ga kowa ya tsaya waje guda su na kallon motar allamun su na jiran su ga wanda zai fito da ga ciki a hankali ya sauke ajiyar zuciya , kafin ya kai hannu ya bude kofar motar ya sauko da kafar shi guda , sai da ya dan jinkirta kafin ya fiddo gudar kafar ya fito da ga cikin motar duk wanda ke wajen sai da ya saki kuka lokaci guda ganin Malik ya dawo cikin masarautar shi kan shi sai da idanunshi su ka ciko da ruwa a hankali ya fara bin wajen da kallo , cen ya hango Azim ya tunkaro shi da mugun gudu ya na daga mishi hannu , ga idanun shi nan cike da ruwa haka Malik ya tsaya ya na kallon shi , har sai da ya kusa kawowa wajen motar ya yi tuntunbe ya fadi da gudu Malik ya nufe shi , ya na zuwa ya Zube saman guyiwowinshi ya tallabo Azim ya na fadin " Azim , ba ka ji ciwo ba ? " ina ko amsa mishi tambayar shi Azim bai yi ba , ya rungume shi ya na sakin kuka kamar karamin yaro a hankali shi ma Malik ya zagayo da hannayanshi a baya a Azim ya rungumeshi , da a ce zai iya yin kuka da ya yi shima sai da Azim ya gaji da kukan nashi sannan ya dago da ga jikin Malik ya na fadin " Ina ka shiga ranka shi dade ? ina ka tafi ka bar mu ? kai da kanka ka ce mu ne ahalinka amma shi ne ka tafi ka bar mu ? ba ka san irin kangin da mu ka shiga bayan tafiyar ka ba , na godewa Allah da ba abun da ya same ka , don Allah kar ka tafi ka sake barin mu a hannun wacen azzalumin mutum " ya fada ya na hawaye bibiyu a hankali Malik ya mike tsaye , sannan ya taimakawa Azim ya mike tsaye shi ma hannu ya kai ya fara gogewa Azim hawayen shi ya na fadin " kar ka damu Azim , in sha Allah babu inda zan je , ko zan tafi sai na cire ku da ga hannun wacen azzalumin " a hankali Azim ya gyada mishi kai ya na sakin wani dan karamin murmushin da har ya manta rabon shi da ya yi murmushi a hankali Malik ya juya ya nufi motar shi da sauri Azim ya mara mishi baya , su na isa ya bude gidan baya ya fiddo trolley din su Malik kuwa ya nufi geffen Inaya , ya bude mata kofar , sannan ya mika mata hannu ba musu ta daura hannun ta saman nashi , sannan ta sauko a hankali Azim na ganin cikin Inaya ya saki wani kyawatencen murmushi ya na yi wa Allah godiya cikin zuciyar cikin sanyin murya ya ce mata " ki shiga ina zuwa , su Ammie duk su na ciki " gyada mishi kai kawai ta yi , da ga haka ya manna mata kiss saman forehead ya raba ta geffen ta ya shiga cikin motar shi A hankali ta daga kafa ta fara takawa ta shiga part din MALIKAT HOUDA , Azim na biye da bayan ta janye da trolley bakin ta da Sallama ta shigo parlourn MALIKAT HOUDA , nan ta tardo MALIKAT INAS , MALIKAT AL'UMU , mama , Tesnim , Nesrine , har ita kan ta MALIKAT HOUDA Nesrine da mama na ganin ta su ka tashi da gudu su ka nufe ta , su ka rungume , su na sakin kuka wata yar karamar dariya Inaya ta yi ta na fadin " Ashhhhhh , kar ka ku ji wa babyna , ciwo " a tare mama da Nesrine su ka daga da ga jikin Inaya su na kallon katon cikinta Godiya mama ta shiga yi wa Allah cikin zuciyar ta , Nesrine ma haka sai sakin murmushi ta ke wani kyawatencen murmushi Inaya ta saki , ta nufi MALIKAT INAS da sauri ta na fadin " Ammie " da sauri MALIKAT INAS da MALIKAT AL'UMU su ka mike su na fadin " yi a hankali baby " cak ta tsaya ta na murmushi har su ka karaso wajen ta , su ka rungume ta sannan su ka shiga tambayar ta ya jiki , ya hanya gyada musu kai kawai ta ke ta na murmushi cen cikin hannun MALIKAT HOUDA ta hango wani baby , ya na barci sai jijiga shi ta ki washe baki Inaya ta yi ta nufi MALIKAT HOUDA ta na fadin " la mamie , baby ki ka samu ? " a tare duk su ka yi wata yar karamar dariya sannan MALIKAT HOUDA ta ce mata " ba na son shirme , na Nesrine ne " dan zaro idanu Ta yi kafin ta juya ta kali Nesrine , da ke tsaye ta na hawaye , irin kallon nan na tambaya a hankali Nesrine ta gyada mata kai ta na murmushi allamun Eh zama geffen MALIKAT HOUDA ta yi ta na fadin " mamie ba ni shi na rike " ta fada na mika mata hannu cikin zolaya Tesnim ta ce mata " wannan katon cikin naki zai bari ki dauke shi ? " " ni dai sai na dauki babyn Nesi

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});