Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 16

Chapter 16

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,093 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nufi hanyar Fada bakinshi da sallama cen kassan makoshi ya shigo Fadar , nan ya tardo duk mutanan fadar shi , su na zaune su na ganin shi kowane ya saki murmushi ya na mikewa tsaye su na gaishe shi cike girmamawa sai da ya karaso tsakiyar fada sannan ya juya ya kalli side din su tsayawa ya yi ya kare musu kallo na dan lokaci kafin ya ce " na ji dadin ganin ku cikin koshin lafiya " a tare duk su ka saki wani kyawatencen murmushi su na fadin suma sun ji dadin ganin shi a raye dan sunkuyar da kai ya yi kafin ya dago ya ce " okay , zan so ku fara shirye shiryen nada sabon Malik ranar Friday , sannan Dalil ( sabon Sarkin bayi ) zan so ka mayar da bayinka part din su , sannan gobe ka sa su je part din Malik su kwashe duk kayan da ke ciki za a zuba sabi , duk wani abu da ke bukatar gyara a cikin masarautar nan har ma wajen ta kawai ku aiwatar , kar ku damu da adadin kudin za a kashe , Idris ( shi ne sabon me kula da dukiyar Daular ) ka bude bankin masarautar , na ba da dama a fitar da kudin da su ka dace dan ganin an kyara masarautar , amma abu na farko da na ke son ku fara shi ne cire min wadanacen banzan status da a ka kafa min bakin Daula , General Abdallah , duk mutanan Fadar Aymane da ke hannun jami'an ka , ku yi executed din su kawai , ita kuma Hafsat a mayar da ita wajen mahaifiyar ta , sannan ku shirya min zama da yan JARIDA a matsayin Mr president ba Malik ba ran monday " ( Idan ba ku manta ba tun farko na ce muku Malik shi ne shugaban kassar Saudiya , kuma duk wata maganar administration a hannun shi ta ke , hakan na nufin shi ne sarki kuma president din kassar Saudiya , mutanan Fadar shi kuma duk yawwancin su ministers ne ) " an gama ya shugaba " su ke fada a tare sannan su ka shiga jero mishi addu'a cikin zuciyarshi ya ke amsa musu da Ameen kafin ya juya ya sa kafa ya baro fadar tafiyar shi ya ke cikin konciyar hankali ya na bin Daular da kallo , a haka har ya karaso cikin word room kai tsaye dakin da ya kai Inaya da farko ya nufa , kawai sai ya ga babu kowa a ciki da sauri ya juya ya koma reception ya na tambayar matar shi cikin nitsuwa Wata nurse ta ce mishi " an sauya musu daki , su na cikin room 5 " bai bata amsa ba ya juya ya nufi room 5 , babu ko sallama ya tura kofar ya shiga ya na idanunshi su ka sauka saman ta , ta na konce saman gado ta na sanye da wata gown blue irin ta ma su jinya , idanunta a lumshe da allamun barci ta ke ko har yanzu ba ta farka da ga sumar ta ba kusan gadon ya ga wani dan cradle tsayin shi daya da gadon Inaya a ciki ya hango babys din su konce a ciki , an dunkule su cikin wani towel , Macen pink , Namiji kuma blue , Ita dai Nailah idanunta a rufe da allamun barci ta ke , Nayel kuma idanunshi na bude ya na kallon ceiling , idanunshi Tak tak irin na Malik wato hazel wata nanauyar ajiyar zuciya Malik ya sauke kafin ya tako a hankali kamar barawo ya karaso gaban su tsayawa ya yi ya na bin babys din shi da kallo kamar ya hadiye su ya na a haka kawai ya ga idanun babyn sun juye kamar yadda a ke juya PAGE din littafi su ka koma farare kal kafin su dawo dai'dai wani dan karamin murmushin geffen fuska ya yi murya cen kassan makoshi ya ce " idanun momynka ka dauko " ya na gama fadar haka ya tako a hankali wajen shi , har kai hannu zai daukar babyn ya tsaya cak ya na kallon Tambarin masarautar a wuyan babynshi ya so ya duba hannun Nailah , amma ya san tunda a ka yi wa Nayel ba makawa ita ma an yi mata lokaci guda kawai ya ji ranshi ya baci da sauri ya janye hannunshi ya juya da sauri ya fice dakin kai tsaye office din doctor din da ta karbi haihuwar Inaya ya wuce babu ko sallama ya tura kofar office din ya shigo ya na fadin " wa ya ba ku izinin yi wa babyna tambarin masarautar nan ? " a hankali Doctor ta mike ta na fadin " ranka shi dade b..... " ba ta kai karshen maganar ta ba ya katse ta da cewa " ki ba ni amsar tambaya ta kawai " " MALIKAT AL'UMU " ta fada a takaice bai ce mata komai ba kawai ya juya ya fice office din , kai tsaye word room din ya baro ya nufi part din MALIKAT AL'UMU ya na taku da sauri , duk yanayin face din shi ya sauya da allamun ranshi ya baci babu ko sallama ya shigo parlourn MALIKAT AL'UMU ya na kiran " momy ! , momy ! momy ! " ya ke fada da karfi ya na tsaye tsakiyar parlourn da sauri MALIKAT AL'UMU ta fito da ga corridor a rude ta ke fadin " lafiya ka ke min irin wannan kiran ? me ya faru ? " cikin bacin rai ya ce mata " momy , why za ki ce a yi wa babyna tambarin masarauta ? , why ? " " zo mare ni Nawfel , mare ni na ce don Allah " ta fada cikin tsare gida wani dan karamin tsaki ya ja ya na kauda kai gefe kafin ya ce mata " momy , ni fa ban bada izinin yi wa babyna wannan abun ba , why za ki min haka ? " " saboda yaron Malik ne , kuma dole a yi mishi tambarin masarauta , kar ka ce za ka goge shi , wlh za ka ji musu ciwo ka ga har yanzu ba wani kwari ne da su ba " " momy ba na son abun da zai hada babys di na da wannan masarautar , that's why na yanke shawarar komawa US da su bayan nadin Malik " dan zaro idanu MALIKAT AL'UMU ta yi ta na fadin " what ? ban gane ba , kamar ya za ka koma US da su ? ka na nufin ba za ka zauna ba ? " cikin sanyin murya ya ce mata " yeah , ba zan zauna ba , ni dama ban dawo da Niyar zama ba , kuma in sha Allah Next Friday zan koma US , dalilin da ya sa ban bada izinin yi mishi tambarin masarautar nan ba , amma kin je kin ce a yi mishi , gaskiya momy ban ji dadin haka ba " a hankali MALIKAT AL'UMU ta nufi Sofa , ta zauna ta na kallon shi fuska a marairaice ta ce " yanzu tsakani

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});