Chapter 21
Chapter 21
dawowa dan na rushe wannan bakin mulkin nashi , kuma cikin yardar ubangiji na yi nassara , ga duk al'umar Saudiya da ke sauraro na a wannan lokacin , zan so ku sani , ni Malik Nawfel HICHAM bin JAABAR na dawo kan kujerata ta Malik , kuma in sha Allah zan ci gaba da kula da kassar Saudiya kamar yadda mahaifina Malik HICHAM BIN JAABAR ya kula da ita bisa gaskiya da kyakyawar zuciya , da ga yanzu duk wani mai laifi za a yanke mishi hukunci dai'dai abun da ya aikata bayan kwakwaran bincike , mai gaskiya kuma a ba shi gaskiyarshi , duk wasu makarantu da a ka rufe za a bude su , a ci gaba da bawa yaranmu karatun da ya dace , da ga Maza har zuwa Mata , I'm sorry ba ni da isashen lokacin sauraron tambayoyin ku , amma ministers za su amsa muku , ina yi wa kowa fatan al'heri , Allah ya mayar da kowa gidanshi na lafiya , Thanks a lot " ya na gama fadar haka ya mike , da sauri su ma yan JARIDA su ka mike su na kokarin su nufe shi amma sojoji sun tare su , a haka har Malik ya sa kafa ya fice wajen , ya na fitowa sai saman wasu dankareren motoci ma su nunfashi duk black , cike a wajen , na yi kokarin kirga motocin amma gaskiya na kassa sai ka ce companyn buga mota dan wajen cike ya ke da motoci ga kuma motocin sojoji kamar su ci kan su , ga kuma sojoji cike da harabar wajen 200 ma Albarka , kowane rike da gun Malik na fitowa duk sojojin wajen nan su ka tsaya cak waje guda , da sauri wani ya nufi wata dankareriar mota Fara kal dan duk cikin motocin nan fara guda tak na gani sai motocin yan JARIDA , a haka sojan nan ya sa hannu ya bude mishi gidan bayan motar hannu ya kai cikin aljihun wandon shi , ya fiddo wasu glass bakake ya saka a idanun shi , maimakon ya shiga motar nan da soja ya bude mishi kawai sai ya raba ta geffen ta ya wuce , ya ci gaba da tafiyar shi ya nufi hanyar fita wajen , duk inda ya wuce sai sojojin nan sun daga kafa su na sara mishi ko sannu bai ce musu ba , a hankali ya dago hannun ya cire button din Jacket din suit din , ya fida jacket din ya yadda a kassa ba tare da ya tsaya ba ya kai hannu ya fido kassan farar shirt din shi da ya soke cikin wandon shi , ya kai hannu cikin dayan aljihu ya fiddo wata bakar face mask , ya saka , ya sa kafa ya fice wajen shi kadai duk mutanan wajen sai da su ka yi mamaki baki sake , sun ma rasa abun da za su yi , su bi shi ko kuwa ? kawai dai sun tsaya su na bin shi da kallo har ya fice bangaran Malik kuwa kai tsaye hanyar Daular Saudiya ya nufa da kafa , duk inda ya wuce sai ya jiyo Muryoyin mutane su na ta yabon shi , dan taron da su ka yi yanzu on live ne kowa ya na kallo ba karamin dadi ya ke ji ba jin yadda mutane ke yabon shi , wasu na jefa mishi Albarka , wasu na jero mishi addu'a kai abun dai Masha Allah , ya amshi sunan shi na Malik dan kowa cikin garin Saudiya ya shaide shi ya na tsaka da tafiyar shi kawai ya karaso wajen wani plaza , cak ya tsaya ya na bin plaza din da kallo , ya na nan yadda ya bar shi bai sauya ba , lokacin guda ya saki wani cool murmushi ya na kallon plaza din dan a wannan wajen ne ya hadu da Diya for the first time a haka dai ya ci gaba da tafiyar shi hannayanshi na cikin aljihun wandon shi , har yi dan nisa kawai ya jiyo Muryoyin wasu samari da ga bayan shi su na fadin " ranka shi dade ! " su ka fada da karfi cak ko ya tsaya , kafin ya ci gaba da tafiyar shi ba tare da ya juyo ba ya na haka kawai ya ga wasu samari guda hudu a gaban shi kamar sun fado da ga sama sun tare mishi hanya daya da ga cikin su ya na ce " ku yi hakuri mun tsayar da ku , ni sunana Adel , tun mu na wancen layin ne mu ka hango ku , to na cewa abokai na mai martaba Malik ne , amma sun ki yarda , shi ne mu ka biyo ku dan mu tabbatar " a hankali Malik ya dago musu hannu ya nuna musu kunnenshi kafin ya yi musu kwatancen shi kurma ne kuma makaho , ba zai iya magana ba " wayo , ba ka gani kuma ka ke tafiya kai daya ? ina dan jagoran ka ? dama dama yanzu akwai security a masarautar da tuni an yi gaba da kai " daya da ga cikin su ya fada a hankali ya girgiza musu kai allamun ba shi da Adel ne ya kalli abokanshi ya ce " kun ga , bari mu raka shi ni da Hadi , kun ga zirga²r da a ke a masarautar nan ya dawo kamar da farko , kar a je mota ta buge shi , ku/ku koma shop , ba za mu jima " ba musu biyun su ka raba ta geffen Malik su ka koma inda su ka fito su na barin wajen wanda ya yi magana da farko ya riko hannun Malik ya na fadin " mu tafi " ba musu Malik ya bi shi su ka tafi tare da wanda ya kira Hadi sai sun karaso wajen da a dakwai kwana sai su tsaya su tambayi Malik wace kwana za su yi , sai ya girgiza musu kai ya na nuna musu gaban su allamun su ci gaba ba musu su ke yin hanyar , a haka har su ka karaso bakin kofar Daular Saudiya , ba tare da sun kawo komai a ransu ba sai da su ka zo dab da kofar shigar sannan Malik ya kwace hannunshi ya na fadin " okay , na gode sosai da rakiya , rike wannan " ya fada ya na cire face mask din shi ya daura saman hannun hadi sannan ya cire glass din shi ya daura saman hannun dayan ya na fadin " na gode , amma na san hanya , zan ci gaba da ga nan , see you next time " ya kai karshen ya na shiga Daular ya bar su nan sun yi sumar tsaye sai da ya shiga sannan ya su ka juyo su ka kalli junan su baki sake su na zaro idanu , wata yar karamar kara su ka saki da dariya a tare kafin Adel ya ce " sai da na ce muku Malik ne amma ba ku yarda ba " wani dan karamin murmushin geffen fuska Malik ya saki dan ya jiyo abun da ya
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31