Chapter 4
Chapter 4
masarautar nan , duk Malik din da ya hakura da kujerar shi , ba shi da izinin komowa da sunnan zai koma saman kujerar shi , dan haka ba ka da ikon ce min na sauka " ya na gama rufe bakin shi ya ga Rafik ya shigo cikin fadar ya na fadin " as a direct descendant of Malik HACHIM bin JAABAR, he has every right to claim the tron โโof his late father, even if he renounced him " " Gaskiya Rafik ya fada , dan haka malam ka tattara kayanka ka yi gaba " Fadin Diya ya na karasowa geffen Malik ya tsaya ya na sakin murmushi " No ! " Aymane ya fada da karfi ya na mikewa tsaye ya ci gaba da cewa " No , ba ka da izinin ce min na sauka , ba ka san irin famar da na sha kafin na hau saman kujerar nan , tun kafin ka shigo duniya na shirya hawa na kujerar nan ta Malik dan har yaron MALIKAT INAS na kashe , na kuma sace mahaifar ta dan kar ta samu wani babyn , amma wannan banzan uban naka ya auri kanwar Daddy , ta haife ka , tun ranar da ka shigo duniya , tawa duniyar ta ruguje , ni na sakawa part din Malik wuta shekara shidda baya kawai dan ka mutu na dawo na kashe Malik , amma wani ikon Allah dan banzan yaron nan ya rayu , okay na hakura , why za ka dawo ? me ya sa ba ka yi zaman ka a cen ba ? amma sai da ka dawo ka shiga tsakanina da burina , amma ban hakura ba ni na juya kwakwolwar Hakim ya harbi Malik saboda ya kassa kashe shi , ni na sa Rouksar zuba mata poison cikin abincinka , ni na saka ta sace ruhin MALIKAT AL'UMU , amma wacen banzar yarinyar ta ruguza shirina baki daya , why ba za ku bar ni na hau kujerar nan cikin konciyar hankali ba ? why ? , wlh ko da sama da kassa za ta nade , ba zan sauka da ga kan kujerar nan ba , ita ce burina a duniyar nan , tun da na taso da son zama saman wannan kujerar na taso , yanzu kuma da na hau ta shi ne za ka ce na sauka ? no , hakan ba zai taba yiyu ba " ya fada cike da bacin rai da allamun fasuwar rai ta kama shi duk mutanan wajen sai da su ka yi salati su na sauraron abun da Aymane ke fadi , bacin rai ya sa ya tonawa kan shi asiri da kan shi shiru Malik ya yi ya na sauraron abun da Aymane ke fadi , dole ya yi mishi ta wayo dan ya samu ya sauka da ga kan kujerar nan , Idan ya ce zai ta karfi , ba zai yi nassara ba , dole shi ma ya yi tunani kamar na su na mugaye , dole ya meda kwakwolwar shi irin tasu kafin ya samu Aymane ya sauka da ga kujerar nan , dama an ce mugu shi ya san makwontar mugu , cuta ce za ta dau cuta a hankali Malik ya sauke ajiyar zuciya , cike da nitsuwa ya ce "as the heir of Malik HICHAM bin JAABAR I have the right to claim the throne of my late father, but since you do not want to give in passively okay, Aymane Abdoul Mujeeb Me Nawfel HICHAM bin JAABAR I provoke you in a duel, the winner will ascend the throne of Saudiya and the loser will pay with his life " a dubu dari Rafik da Diya su ka kalli Malik su na zaro idanu , har su na hada baki wajen cewa " ka na jin abun da ke fada kuwa , hakan na nufin idan ka fadi kashe ka zai yi " cikin kwarin guyiwa Malik ya ce " Eh , na ji abun da na fada " ya na gama fadar haka Aymane ya bushe da wata shegiyar dariya har da tapi ya dafe ciki shiru kowa ya yi ya kallon shi kamar wani zarrare sai da ya tsagaita dariyar shi sannan ya dago ya kalli Malik ya ce " kai a ganin za ka iya kashe ni ? , ko ka kashe ni kamar ka kashe maciji ba ka cire kai ba , Okay na yarda , wane irin duel ka ke so mu yi ? " " Sword Duel " ya fada a takaice ya na kallon Aymane sake bushewa da dariya Aymane ya yi ya fadin " okay , na yarda , in dai ta haka ne kawai zan zauna saman wannan kujerar , na yarda , kai kuma ka shirya tarda tsohon mahaifinka , dan har yanzu ba a yi wanda zai ga bayan Aymane bin Abdoul Mujeeb , ko mutuwa tsorona na ke , bare kai ragon banza " " All right , tun da ka yarda fine , yau ranar monday , za mu yi shi a ranar Friday , amma kafin nan , da ga kai har wadanan mutanan fadar taka , ba ku da izinin shigowa fada da sunnan aiki , har sai mun kammala duel din mu , sannan da ga yanzu ka fita da ga Malik Aymane , ka koma Aymane , har zuwa lokacin da za mu kammala , a nada wanda ya yi nassara a matsayin sabon Malik " " okay " Aymane ya fada a takaice kafin ya sa hannu ya cire Alkyabar Malik da ke jikin shi ya ajiye saman chair din bayan shi , ya cire Rawanin kan shi ya ajiye saman Alkyabar , sannan ya juyo ya fara takawa ya karaso gaban Malik ya tsaya sai da ya kalle shi cikin ido sannan ya ce " mu zuba mu gani , shege ka fassa , Nawfel Hicham Bin Jaabar tun yanzu ka sa a shirya kabarin ka , da ni ne kai zan ce a yi shi nesa da na mahaifina dan kar ya ga wane irin lusarin yaron da ya haifa " ya kai karshen ya sakin wata yar karamar dariya ya raba ta geffen shi ya wuce ya na fita Malik ya saki wata yar karamar sheet da ya rike a hannun shi a baya nan take wajen ya fara zubar da jini a dubu dari Rafik ya riko hannun nashi ya na fadin " Inallillahi , ranka shi dade , why za ka ji wa kanka haka ? " a hankali Malkk ya sauke ajiyar zuciya ya na fadin " dole na yi hakan , if not zuciya za ta debeni , na buge shi " ya na gama fadar haka ya dago kai ya kalli mutanan fadar Aymane , wani mugun kallo ya wurga musu nan take su ka sha jinin jikin su cikin ba da umarni ya ce musu " idan ku ka yi one minute a cikin wajen nan , ka tabbatar gawarku ce za su fita " bai gama rufe bakin shi ba su ka tashi daya bayan daya da gudu su ka fice fadar , ta rage da ga Diya sai Malik
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30
- 31 Chapter 31