Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 7

Chapter 7

Exiled Princess Book 4 Complete Hausa Novel 1,068 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

yeah , na ce ki fadi abun da ki ke so , amma ba abun da zan iya yi ba , ina kuma zan samo miki Island " " Nooooo , ni fa ba ka gane abun da na ke fada ba " " to , explain me , me ki ke nufi ? " ya fada ya na daga mata gera guda wani dan karamin murmushi ta saki kafin ta ce " let me explain to you , Cewa na yi mu samu kanmu a wani tsibiri da ke tsakiyar ruwa babu kowa kawai da ga ni sai kai a cikin wani katafaren gida kusa da ruwa, tare da kallon teku, da faɗuwar rana mai ban sha'awa " " ba dan ki gani abu a film ba za ki ce sai kin yi ke ma " ya fada ya na kai hannu ya dan zunguri kanta wata yar karamar dariya ta yi ta na fadin " It's a problem to have a dream ? ni kawai abun da na ke so kenan " ta kai karshen ta na turo dan bakin nan nata dan jinkirtawa ya yi kafin ya ce " okay , yanzu fada min , idan na cika mafarkin ki , me za ki ba ni ? " cike da zumudi ta ce " duk abun da ka ke so " " don't be sure , da gaske za ki iya ba ni abun da na ke so ? " " ya fada ya na daga mata gera guda a hankali ta gyada mishi kai allamun Eh " ko da kuwa ....... " ya rada mata karshen a kunne , ni dai ban ji abun da ya ce ba da sauri ta girgiza kai ta na marairaice fuska ta ce " no gaskiya ba zan iya ba baby , wai har yanzu ba ka bar maganar nan ba ? " " ta ya ki ke so na bari , idan kin shirya yi min zan saya miki Island din baki daya , na tafi na yi wanka " ya kai karshen ya na mikewa ya nufi toilet ya shiga jim kadan ya fito sanye da bathrobe , ya na fitowa ya wuce kai dressing room , kamar ko ya san kayan su na nan jim kadan ya fito sanye da wani wando Jeans black color , da T-shirt black color ita ma a hankali ya karaso wajen ta , kawai sai ya ga har ta yi barci bai yi kokarin tashe ta ba , ya janyo duvet ya rufe ta har zuwa kirji sannan ya manna mata kiss saman forehead kafin ya juya ya nufi kofar fita dakin security din ya cire sannan ya bude kofar ya fito kai tsaye parlour nan ya tardo su zaune sun yi zugum kamar an aiko da mutuwa cak ya tsaya ya na kallon su murya a sanyaye ya ce " lafiya ku ka zauna a haka ? mutuwa a ka yi ? " a tare duk su ka dago kai su kalle shi , ya na tsaye ya rike hannayan shi a baya a hankali ya bude hannayan shi ya na kallon RIANNA , da gudu su ka tasso ita da Tesnim su ka fada jikin shi , su na sakin kuka cikin sigar rarrashi ya ce " wlh in ba ku yi min shiru ba sai na koma inda na fito " da sauri RIANNA ta ce " shikenan , shikenan , mun yi shiru , ba kuka mu ke ba " " that's good , yanzu ku sake ni , kar ku karaya min baya " va musu su ka sake shi , su ka tsaya gabanshi har su na hada baki wajen cewa " i have really missed you " " ni ma na yi kewar ku over " ya fada cikin sanyin murya wata yar karamar dariya RIANNA ta yi ta na sakin kuka lokaci guda , na lura RIANNA kamar MALIKAT INAS ta ke , abu kadan sai ta saki kuka a hankali ya raba jikin shi , ya raba ta geffensu ya nufi MALIKAT AL'UMU ya rungume ta rungume shi tsam ta yi ta na fadin " na yi kewar ka sosai my baby " a hankali ya raba jikin shi da nata sannan ya nufi MALIKAT INAS tun kafin ya karaso ta nufe shi da sauri ta rungume shi ta na fadin " kar ka sake tafiya ka bar ni don Allah " cikin sigar rarrashi ya ce mata " kar ki damu Ammie , ba zan sake rabuwa da ku ba " wata yar karamar ajiyar zuciya ta sauke ta na murmushi a hankali ya raba jikinshi da nata ya juya ya kalli MALIKAT HOUDA cikin zolaya ya ce mata " wai ke tsohuwar nan har yanzu ba ki mutu ba ? " " karbi nan dan rainin hankali kawai , don Allah zo kashe ni in ka gaji da gani na " ta fada ta na matse mishi fuska dan tabe baki ya yi ya na kauda kai ya ce " ni tambaya ce kawai na yi " wata yar karamar dariya MALIKAT INAS ta yi ta na fadin " kai dai ka na son takurawa mamie , me ta yi maka ? ko dan ta na son ka shi ne za ka yi mata wannan shegantakar ? " " ai ni ban ce ta so ni ba " ya fada ya na kara shan tsami da ga haka ya ce musu " kun ci abinci ? ko ba ku jin yunwa ? " " Yanzu mu ke wa Inas mu koma part din mu , mu shirya muku abinci " fadin MALIKAT AL'UMU cikin nitsuwa ya ce mata " No , ba na son kowa ya bar part din nan , mamie bedroom nawa ne a part din ki ? " ya kai karshen ya na dawo da kallon shi kan MALIKAT HOUDA kai tsaye ta ce " bedroom takwas ne a ciki " gyada kan shi ya yi a hankali ya na fadin " okay , ba damuwa na san za su ishe ku kafin a gyara masarautar , ba na son ku fita bayan wannan azzalumin ya na cikin masarautar , duk wani abu da za ku bukata zan kawo muku " da sauri RIANNA ta ce " kai kuma fa Akhie ? " dan jinkirtawa Malik ya yi kafin ya ce " kar ku damu a kai na , kawai ina son na tabbatar ku na cikin koshin lafiya " " wacen Azzalumin kuma fa ? ya ce zau sauka da ga saman kujerar ? " MALIKAT INAS ta fada " Yeah , nan da Friday za mu sani " ya na gama fadar haka ya nufi hanyar fita parlourn ya fice da kallo su ka raka shi har sai da ya fita sannan MALIKAT INAS ta tasso ta riko hannun RIANNA ta na fadin " mu je ki sauya kayan nan " ba musu RIANNA ta bi bayan ta su ka shiga corridor bangaran Malik kuwa ya na baro part din ya shiga motar shi kai tsaye ya fice masarautar ▪AFTER SOME HOURS bai dawo masarautar ba sai karfe goma sha biyu na dare , ko

Table of Contents

Chapters

31 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
  31. 31 Chapter 31
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});