Chapter 9
Chapter 9
sani idan yaso kirki yanayi Zama sukayi,Nikuma nashiga kitchen da kyar na iya bude firij saboda kauyan cina yayi yawa lemu na dauko musu da ruwa na Basu. Nan baba Ayuba ke tambayar Ammi Abba Tace Aiko bayanan,sun tafi kano,wani takaicine ya lullubesu baba sani kuwa har Yana kwarewa yace kano Kuma? Baba Ayuba yace oh rayuwa yanzu muhammadu ne da wannan gidan?harda zuwa kano? Idan natuna sanda yake kwasan masai da bola abin mamaki yake bani. Magana suka gasama Ammi itama Kuma tagani,Murmushi nayi nace wallahi kuwa baba gashi yanzu a dalilin katsalan dan dina muka shiga daukar nan,yaran da ake tsine musu idan ba iyayensu ke tsine musu ba ai abin sai kaga Yana tafiya yanda akeso,yau da hjy 'yar mai goro nanan nasan da zatayi alfahari(wato mahaifiyar Abba) harara baba Ayuba yasakin min yace Mai Hali dai Sam baya canza Hali to yanzu dake nayi magana?Nima hararar na wurga mai nace maganar mahaifina fa kakeyi shiyasa nasa baki. Kwafa baba sani yayi yace ai yanzu Dole muhammadu yayi aure tunda arziki yasamu kaga ni saina samo Mai bazawara. Daka tsalle nayi kamar nice za'ama kishiya nace wallahi bazai yuwuba Kuma Abba bazai dauki shawarar na ba,galala suka saki mouth suna kallo na,Ammi tace Shakeerah tashi kiwuce ciki,da toh na amsa mata na mike Suma mikewar sukayi daganan suka fara Dora ashar,inaso in rama saboda jikina har tsuma yake sai dai Ammi ta hanani. _I need ur comment and sharhi_ Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami🖋️Yafi takobi 🗡️ 💕💕 ❤️ [7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨ ( Daukar Fansa ) Story& writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL ______✍🏽______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* 🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah)) *_T.W.A_* _________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________ Marubuciyar⬇️ _ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_ *DA* _ _MIJIN ZAHRA_ *Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.* Bismillahir-rahmanir-raheem. *Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai...* Page:1️⃣1️⃣--1️⃣2️⃣🖊️ _________Tunda suka shigo cikin school din kallonsu ake daga student din har lecturer's din,bawai kwalliyar su kadai ke burge mutane ba,hadda salon tafiyar su day kyansu da iya magana ke burge mutane,uwa uba Kuma ga kwanya suna jinsu kamar gifted. Shigar larabawa sukayi gaba daya,Wanda yasake haskasu. Shiga hall sukayi domin gabatar da Exam nan sukayi suka gama batare da sun kula kowa ba. Bayan sun fito suka wuce gida Cike da gajiya,da yake yau khadee ce da girki,cake kawai sukasha da lemu ta Shiga kitchen don dora girki. Sai da aka yi sallar magrib sannan khadee ta sauke shinkafa da miyar souce Wanda yaji attarugu,basuci abincin ba sai da suka gabatar da Isha tukuna sannan sukaci abinci sunayi suna shewa da hira. Sun kammala cin abinci ,Fauzi ta dubi Shakeerah tace"babee muna jinki. Murmushi Shakeerah tayi tace"dama nasan kina Nan kina kwakwa da kokarin son Jin labari. Dariya suka sa gabadaya,khadee tace wallahi nima haka shi naketa kwa-kwan son ji. Shiru tayi ta dauki tsawon minti 3 zuwa can tafara magana kamar haka. "Da fari dai ni Sunana Maryam Muhammad Adali, Ni haifaffiyar Zaria ce anan na girma anan nataso,gaskiya tun tasowar mu muka taso masu rufin asiri azahiri bamu dashi domin kuwa mu ba 'yayan masu kudi bane,ba musan wani Abu karatun boko ba sai dai na Allo wannan fa akwai shi Wanda mahaifin mu yatsaya Kai da fata yabamu nida Aunty ta. Mu biyu ne Abba ya haifemu Dani da yayata mafi soyuwa a gareni ta nuna mun so fiye da komai,kun ganni hatta talla nayi tallan biredi saboda tsaban rashi,tun Ina karama ake daurawa Aunty Saudah tallah,macace mai hakuri tare da kawaici irin Ammi,kada kuyi tunanin Wai a son ran iyayen mu muke talla a'ah Babu CE takawo haka,tun farko Abba shagon Saida agoguna yake Rana Daya Bari suka tsiyatar dashi. Aunty Saudah haka zata dauki tallah batare da ta karya ba,Kai hatta ni mutan gidan,da yawa idan takai ba siya ake ba sai dai a lallatsa a tafi a bar mata,wani ma a kwance aci,ace baza'a siya ba. 'Yan uwan baban mu suna da Hali dai dai gwar-gwado sai dai temako ne baza suyi ba. Aunty Saudah kuwa duk abinda ke faruwa bashi yake hanata gobe fita da bread ba,ana cikin haka na girma Wanda na taso da shegen rashin ji da fitsari,ba anuna mun yatsa a maida lafiya ba'amun na kyale,tun Ina gida,dalilin haka yasa Ammi ba kasa fai take Bari na fita ba. Koda nakai 9years tsiyata kuwa ta karu,domin kuwa rigima nasa akan abarni Nima nadinga fita talla kamar yanda Aunty Saudah ke fita,munada kyau daga mu har iyayen mu,Amma tsabar wahala tasa mun kode,kafafuwa na kuwa duk Sunyi faso tsabar gantali yamun yawa da yawo Babu takalmi. Kullum nasihar Ammi da Abba shine mu natso,nikuwa Shiga takeyi tanan tafita ta can. Tallah nafara bin Aunty Saudah ita a lokacin tana da 14years, Nikuma Ina Daukar pure water. Wata rana muka dauki tallah da ita gashi garin da Rana sosai,wani gareji mukazo wucewa kunsan dai garejin masu gyaran motoci to nan. Alamu sukayi mana da baki kamar fito, Aunty Saudah ce ta juyo da Sauri ta nufi wajen su,domin ita burin ta a kullum da tafito a siye tanajin nauyin komawa gida ba ayi ciniki ba. Zugwi-zugwi nabi bayanta kamar tsohuwar munafuka,wasu maza ne suka kariso tare da Daukar bread din,Daya ya bude ya dauki na hamsin ya ciye tassss tare da Daukar pure water na yasha,gyatsa yayi irin na 'yan iskan Nan,shikuwa dayan da ya dauki bread din rabi yawafce sannan ya aje ragowan. Daure face Wanda yacinye ledan bread Daya yayi,sannan ya dubi Aunty Saudah yace"wareee anan wajen,Cike da tsoro Aunty Saudah ta sungumi farantin bread dinta domin gudu. Dubana yayi yace"kema dauki wannan ajawon ruwan naki ki wuce,yayi maganar Yana wurgi da bucket din ruwana. Nan kuwa ruwa ya fadi wasu Kuma suka farfashe,cikin bacin Rai na dago na dubeshi sannan na dube bucket dina. Daya a cikinsu yace"ba magana ake Miki ba don uwarkiiiiii? Itakuwa Aunty Saudah fara jana tayi Cike da tsoro tana cewa"Shakeerah zo mune gida mu barsu da Allah . Fusge hannuna nayi na nufi inda bucket Dina yake,da yake irin na karfen nan ne Mai murfi,dauka nayi ba nufo su,sukuma a lokacin sun juya sai dariya suke tikawa ba suyi aune ba sukaji saukar bucket akan daya a cikinsu,ihu yasaka,a firgice dayan shima yajuyo Aiko na sakin mai bucket din a gushi,duk cikansu ihu sukasa domin wajen ya fashe bucket din datsan su yayi. Cikin Sauri ragowar mutanen dake garejin suka kariso ana tambayar meke faruwa?a ciki kuwa harda ogan wajen. Cikin bacin rai nafara magana"Saboda zalunci irin naku da mugunta akan me zakuci bread kuce mutafi sannan kuyimun fatali da bucket din ruwa,oho dayake tasaba zuwa ita kadai dama kume masu Mata haka Koh?to idan ita ta dauka Ni bazan dauka ba eheeee,na karishe maganar Ina murguda baki. Ogan su ya tambayi ba'asi Nan kuwa na zauna na zayyane komai harda karawa da gishiri,Cike da bacin rai yake dubansu yace"lallai abinda yarinyar nan tayi tamun dai-dai gaba kwasake......cikin Sauri nace"wallahi gobe ma kuka sake sai nayimuku mafiyin wannan,kudena ganina 'yar karama akan
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30