Chapter 26
Chapter 26
sai dai Shakeerah taki aminta,fita tayi ta shiga part din ta shi kuma Daddy ya wuce toilet. A bangaren hjy Sameera kuwa wayan ta ta dauka cikin zumudi takira wata kawarta da suke kungiya guda ta sanar da ita halin da Aunty Amarya ke ciki. Kawanta tace"A hayye nanaye wallahi halinki Hjy sameera na hatsabiban ci na burgeni Sam bakima kishiyoyi da wasa,ke kina aiki mijinki nayi,nasan a yanzu zaki gama da daya,sannan kidawo kan amaryan nan. Cike da takaici Hjy Sameera tace"Ai hajiya karime wannan karan Alhj bala'i ya dauko mana domin kuwa wannan Amaryan da kissa,makirci,kisisi na tashigo gidan nan ke uwa uba bariki yarinyar da na haifeta na juya Amma wallahi cin ubana take,ke akwai Ranar da naso nazane ta kaman yanda nake ma sauran wallahi Marin da tamun sai da nakusa fitsari,nidai riban da naci kawai shine na hanashi kusantar ta da yayi shine kawai ribata, yarinya karama ta gama zautar dashi,ko yanzu na barosu suna iskanci da juna,kinsan Allah da ban tashi ba?da a gabana zasuyi romance. Ta cikin hjy karime ta rabka salati tace"lallai ankawo miki karuwar miji cikin gida, nidai ba wannan ba wallahi Hjy a bukace nake dake munkwana biyu bamuji dimun juna ba yakamata muhadu. Hjy Sameera tace"kamar kinsan abinda ke Raina kenan,mezai hana kishirya kizo idan yaso sai mu wuce asibitin kungiya muga halin da 'yar iskan can ke ciki. Hjy karime tace"toh shikenan hjy na sahibata ganinan tafe,takari she maganar tana bata wani kiss ta cikin wayar. _innalillahi wa inna ilaihirrajiun lallai rayuwa irin nasu hjy Sameera da Daddy masifa ce,Dole Allah yadinga hukun ta mu,Allah na jarabtar mu muna zagin shugaban ni alhalin mu bamu tuhumar kawu nanmu Dole Allah yadinga hukun tamu domin homosex da luwani yazama ruwan dare,har da tsofaffi?ya Allah ya yafe mana,yasa mugama da duniya lafiya Ameen_. Daddy ne yakira Shakeerah yace"ta shirya zaizo ya kaita asibiti wajen Aunty Amarya, Shakeerah tayi murna sosai, Cike da zumudi ta shirya cikin wani hadaden shadda peach 🍑 colour yayi mata kyau sosai,babban mayafi ta yana white sai wani platshoe mai tsada shima white,fitowa tayi dai-dai lokacin bakuwar hjy Sameera tashigo da motar ta shima Daddy yafito daga farlon,tundaga nesa ta kafe Shakeerah da kallo har tana kusa faduwa, tsayawa tayi suna gaisawa da Daddy,Cike da bariki tafara zolayar Shakeerah,wanda itama ta Bata amsa Cike da taku,sallama ta musu tashige part din hjy Sameera jikinta babu inda baya rawa. Sosai Daddy ke kallon Shakeerah Saboda kyanda tayi Masa sosai,a gaban motar yasata sannan suka nufi hanyar,tunda suke tafiya babu Wanda yacema wani kanzil,sosai suke tafiya har suka fara shiga daji,abin ya daure ma Shakeerah kai,juyowa tayi ta dubi Daddy tace"Papi wai hospital din da nisa ne? Daddy yace"Mekika gani ne? Shakeerah tace"toh papi naga anata lula tafiya ne ni sam bana kaunar tafiya Mai nisa ko lokacin da nazo garin nan ikon Allah kawai yakawo ni da kuma bin umarnin mom. Kada Kai Daddy yayi yace"Rabon na ganki baby na, rabon muzama Abu daya,rabon kizama matata. Dariya Shakeerah tayi tace"hakane,pls muyi mukai nakosa na ganta naga halin da take ciki. Daddy yace yqnzu kuwa,tafiyan minti talatin suka Kara,suka kawo hospital din,koda suka shiga asibitin wani yammm Shakeerah taji a jikinta,a hankali suka fara shiga asibitin duk dakin da suka wuce Sai dai kaganshi a rufe gashi yayi irin Jan duhun nan jazur,firgita Shakeerah tayi a zahirin gaskiya ta kankame hannun papi jikinta na wani irin rawa a hankali tace"Papi wannan wane irin hospital ne? Hannu yasa a bakinsa yace"Shiiiiiiii bari idan mun koma gida zamuyi maganar. A hankali suka Isa dakin da take shine kawai da haske da sallama suka shiga,idanuwan ta biyu sai dai tana bacci fusge hannun ta Shakeerah tayi daga na Daddy ta nufi gadon Aunty Amarya, itama Cike da farin ciki tafara yimata murmushi Cike da karfin hali. Shakeerah ta Isa wajen ta tace"Aunty Amarya sannu,cikin wahalalliyar murya tace"Shakeerah kinzo ne?naji dadin zuwanki sosai,ta gefen Ido Daddy ya dalla mata harara,dama sunja mata kunne Akan Muddin tafadawa wani sai ankarar da dangin su don haka sosai take tsorata da lamarin su Daddy. Sosai taba Shakeerah tausayi ganin yanda take bleeding duk da anrufe ta da wani farin mayafi,duban Daddy Aunty Amarya tayi tace"Alhj katemakeni jini na zaikare in mutu ta karishe maganar tana me fashewa da kuka. Juyowa Shakeerah tayi ta dubi Daddy tace'Pls papi a canza mata hospital mana don Allah,inba haka ba muna cikin maseefa domin idan Aunty Amarya ta mutu bakai va hatta mu da dangin ka muna cikin bala'i. "Domin naji ma kunne na 'yan layin mu sunfara zargin Kai kake kashe ahalinka,cikin Sauri Daddy yadubeta a firgice,latso hawayen gulma Shakeerah tayi tace"inaso muje waje nafada maka wani magana Wanda bakasan da ita ba papi. Cikin Sauri Daddy ya fita yace"muje kifada mun ko menene. Mikewa tayi ta aje wata 'yar karamar motan wasan yara wanda tashiga video ta seta batare da kowa zai gane ba tabar dakin. Cikin Sauri yarike mata hannu suka fito farfajiyar asibitin dai-dai lokacin Hjy Sameera da hjy karime sunxo da harara hjy Sameera tabisu suka shige asibitin. Duban Shakeerah Daddy yayi jikinsa na matukar rawa yace Ina saura ranki. Kara latso hawayen Shakeerah tayi tace"Papi idan ka lura duk 'yan unguwar ku da yaran sun dena rububin zuwa wajena Koh? Daddy yace"hakane hakane. "Toh Wai zama 'yan unguwar sukayi aka hada committee Wai ana zargin Kai ke kashe ahalinka Saboda dukiyan ka tayi yawa Kuma Wai da ba haka kake. Muryan Daddy na cracking yace"Ni.....n..nnii na shiga uku yacire hula yafara fifita zufa na ketomasa,murmushin gefen baki Shakeerah tayi zuwa can tasake kwabe face tace"Papi meyasa kake zufa haka? Wayancewa Daddy yayi da cewa"babu komai kawai naga lokaci Daya za'ayimun sharri ne,ni akewa sharri irin wannan?lallai dole na dau mataki. Kwalo idanuwa Shakeerah tayi waje domin gudun kada yaje yayi rigima a Unguwa tace"mezakayi Papi? Daddy yace"Zansa aimana iyaka ne ai kashe Rai ba abun wasa bane,yanzu kinsan menene muje kishiga hospital din zanje nadawo yanzu kinji?,kukan shagwaba Shakeerah tasa ka Papi kan ita bazata iya zama ita kadai a dakin ba kawai yaje da ita. Daddy yace"bazanje dake da nisa ba,muje in kaiki gidan matar me gadin hospital din nan tunda sunada yawa ki zauna kafin nadawo. Nan kuwa Shakeerah ta amince domin tasan motar da ta aje yananan yana mata video,daukan ta Daddy yayi ya kaita gidan,tsohuwa ce ba can-can ba domin ko Kai fulani batayi ba. Bayanin Shakeerah Daddy yayi Mata,cike da fari'ah ta tarbi Shakeerah sannan tashiga da ita gidan,gida ne wanda kaman na haya ne domin dakuna ne sunkai goma sha a jere,sosai Mutanen gidan ke kallon Shakeerah domin su kallo daya zaka musu kasan cewa sai a hankali,dakin ta matan tashiga da Shakeerah Wanda yakejin shi fess Babu abinda Babu ma Jin dadi duk da cewa ciki daya ne,Zama tayi kan sofa matar ta kawo ma Shakeerah abinci da ruwa,haka kawai Shakeerah taji bata yarda da matan ba. Duban Shakeerah tayi tace"lallai yarinya kuna damawa kingan ki kuwa? Shakeerah bata fahimci maganar ba Amma dayake gulma na cinta sai tayi Murmushi tace"Mama kenan mungode. Tsohuwar tace"Amma kema kina cikin kungiya ne koh?haka kawai Shakeerah ta tsinci bakin ta da furta Eah. Tsihuwar tace"Yawwa kokefa ai nasan kishiyar
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30