Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 14

Chapter 14

Deejamah Book 1 Complete Hausa Novel 1,305 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

bakin ciki,na rantse da Allah duk Wanda yasake batawa mahaifiyata Rai sai na ci du........Ammi tace"ke ke ke Shakeerah. Cikin bacin Rai Shakeerah tace"Ammi don Allah kiyi shiru,har yaushe su baba Sani da baba Ayuba zasu Dena cimmiki Kashi kina shiru?wa billahillazi bazan dauka ba Ni sai na yiwa mutum rashin mutumci. Saria su baba Ayuba sun San halinta yasajikinsu na rawa suka bar gidan. Nan Ammi tayiwa Shakeerah ta tas sannan Tace tashirya taje tabawa 'yan uwan babanta hakuri. Da toh Shakeerah ta'amsa ma Ammi bawai Yana nufin taji ba,sannan tasake bawa Ammin tata hakuri. Shiryawa tayi cikin wani Riga da wando Pakistan purple nd white gaskiya Sunyi Mata kyau sosai part din fulani taje gaisheta,ta cidda mota a harabar gidan hannunta rike da foodflask ne a hannunta da sallama ta shiga falon wata mata tataras a zaune a zaune mai Kama da Goggoji duk cikansu da fara'a suka dago suna duban Shakeerah,fulani tace"A'ah Shakeerah ur welcome,da Murmushi ta Isa wajen gaida fulani tayi sannan tagaida bakuwar,amsawa tayi face nata dauke da Murmushi aje foodflask tayi tace"fulani ga alalen inji Ammi. Murmushi tayi tana jawo cooler din ta bude"Wow Masha Allah fulani tafada,ita kanta bakuwar hadiye miyau tayi,duban matar fulani tayi tace"Kinga Shakeerah jikata jikan arziki. Shakeerah wannan 'yata ce itace ta hudu. Murmushi Shakeerah tayi tana kallon matar tace"Allah sarki ai Ina ganin ta naga kamar ku,mikewa tayi tashiga kitchen ta dauko mata roban wanke hannu da plates biyu da spoons,duk cikansu suka wanke hannnayen sannan matar tazuba ma fulani abinci itama ta zuba nata. Shakeerah tace"Fulani n atafi zanje kasuwa. Fulani tace"Toh Shakeerah Sai kin dawo,fita tayi ta nufi part dinsu. _I need ur comment_ Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami πŸ–‹οΈ Yafi takobi πŸ—‘οΈ πŸ’•πŸ’• ❀️ [7/18, 2:05 PM] XahrattyπŸ₯°πŸ˜˜: πŸ’βœ¨ *DIAMOND LADIES* πŸ’βœ¨ (Daukar Fansa) Story&writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL _______✍🏽_______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* πŸ”±(( Home of Expert and talented writers,da tamvarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah)) *T.W.A* _________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________ Marubuciya:- _ *A DALILIN 'YAR TSUNTUWA* _ *MIJIN ZAHRA* *ND* *NOW* *DIAMOND LADIES* (Daukar Fansa) *Littafin diamond ladies (Daukar Fansa)na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari 100 na waya ta wannan number 08060719719,sai nayi adding dinsa a group din* Bismillahir-rahmanir-raheem. *Da sunan Allah mai rahama mai jin kai....* _FREE PAGE_ Page:2️⃣2️⃣--2️⃣3οΈβƒ£πŸ–ŠοΈ __________Mezai hana muhada wannan yarinyar da Jalaludden Aure?duk cikansu suka ce Eah,tadai Hjy Kaltume tana ta kallon su,hjy shamsiyya tajuyo tace"Aunty Kaltume ko a kika gani? Hjy Kaltume tace"hjy shamsiyya idan matanshin ce ita Allah ya Sanya alkhairi. Hjy shamsiyya ta dubi fulani tace"fulani to kefah? Fulani tace"tun Ranar da na fara ganin ta nayiwa Jalal sha'awar ta a matsayin mata. Hjy shamsiyya tace"to Alhamdulillah abun kam yayi kyau sai ayi zaman meeting na musamman koh? Gaba dayansu su suka amsa da Eah,cigaba sukayi dacin dambun naman zabin da kunun ayar sai Santi Sukeyi,suma su Alhj kabeer ba'a barsu a Baya ba,domin suma sunci. Washegari Shakeerah da sassafe da wuri ta nufi kd domin suna da Exam da karfe takwas da Rabi, direct KASU ta wuce,tayi mamaki matuka na ganin su Fauzi,nan sukayi Exam suka fito,nufar capteria sukayi don zuwa susha coffee. Nan fa aka dasa hirar yaushe rabo,Baya sun sake fitowa Exam suka wuce gida,a lokacin da suka Isa a zahar yayi,don haka suka gabatar da sallar da ke kansu. Shakeerah taciro musu dambun naman da Ammi ta hada musu,cike da farin ciki suka fara ci Fauzi tace"Wallahi Shiyasa nakeson Ammi domin ita din akwai kula,khadee tace"kedai bari,kunsan matsalar da nake fuskanta kuwa diamond ladies? Cikin Sauri suka girgiza kai tare da mai da hankalin su kanta khadee taci gaba"Hmmm kannena yaran amaryan Daddy gaba daya anwayi gari sun rasu,biyu a ciki mata ne duk an kwakule musu Ido,dayan na miji ne anyanke masa joyst*ck nasa. "Innalillahi wa Inna ilaihirraji'un su Shakeerah suka ambata ita da Fauzi,Fauzi tace"gaskiya khadee matsalar ki yakamata a fara warware wa yanzu,domin bai kamata a bar Daddy yana cigaba da wannan aika aikar ba. Shakeerah tace"haka ne nidai a bangare na matsala daya ne wanda Kuma bazai yuwu ba,duban ta sukayi suna cewa menene matsalar? A jiyan zuciya Shakeerah ta sauke tace"a cikin mu biyu nida ke fauza sai wata ta auri Daddy,duk cikansu su a firgice suka dube ta,tace"Yes ta haka ne kawai zamu iya cimma burin mu na daukar fansa a wajenshi babu wanda zai iya hakan sai makusan cinshi,wato matar shi,zufa ne yafara kwararo musu. Yake Shakeerah tayi tace"Diamond ladies ku kwantar da hankalin ku lokaci yayi da zamu fara daukan fansa fa nasake jaddada muku,idan dame mgn Ina saura ransa. Khadee tace"Shakeerah wannan shawarar ba me yuwuwa bace gaskiya yakamata a canza ta a memi wani. Duban khadee Shakeerah tayi tace"Yaushe ne akayi rasuwar? Khadee tace"jiya ne Wallahi. Shakeeerah tace"to Kingani,abinda za'ayi shine insha Allah yazama wajibi wannan week end din muyi shi a gidan Daddy.....duk cikansu su a firgice suke duban ta,bakin Fauzi na rawa ta dubi Shakeerah tace"Shakeerah kada kiman ta Daddyn khadee nada matukar hadari. Shakeerah tace"yess I know but hakan shine mafita,pls kada kuman ta taken mu mana,mun day alkawarin daukan fansa ga duk wani azzalumi,Muddin bamu cire tsoro a zuka tanmu ba to tabbas Babu yanda za'ai mu cinma buri kanmu,mudai musa Allah Daya a zuciyan mu,kuma Yana tare damu a duk inda muke, duk cikansu suka ce hakane kam. Mikewa Shakeerah tayi ta nufi dakinta don gyarawa sai dai ko da tashiga taga dakin fesss Banda kamshin turare babu abinda yake,juyowa tayi face data dauke da smile Tace"Wow dakinfa yayi kyau ngd muku sosai diamond ladies domin nasan mutum guda bazata gyaramun daki ba sai guda ta hadaka,suma murmushin suka mai da mata. Cigaba sukayi da zuwa school, yanzu Exam saura 1week su gama cikin ikon Allah suka shirya Ranar friday ita da Fauzi don tafiya bauchi,da yake duk after 2 weeks suke zuwa week end shiyasa wannan week din nan bazasu gida ba,sun samu damar zuwa bauchi. A motar Shakeerah suka nufi garin bauchi Cike da kewar khadee,sai dai sunja mata kunne akan fita tinda da komai a gida pls kada tafita ita kadai har sai sun dawo. Tun 7:00am suka fita Basu Isa ba sai 5:00pm,a gajiye suka Isa gidan Daddy tabbas gidan sa abun kallo ne sai da suka tabbatar da gidan Alhj Sani Bukar Mai Iyali ne sannan suka kutsa kai cikin gidan bakinsu dauke da addu'an shiga gida" _bismillahi walajna wa bismillahir-rahmanir-raheem kharajna wa'alallahi rabba na tawakkal na_,sannan suka shiga yanacan sama yana hangen su,zumbur ya mike don 'yan matan sun Gama tafiya da imanin sa,duk abinda yakeyi Shakeerah na ankare dashi. Direct dakin Mai gadi suka nufa,tambayar shi sukayi ko yasan part din hjy saddiqa? Amsawa yayi da Eah yasani,ya nuna musu wani part yace gashi can shine nata. Shakeerah tayi wani makirin Murmushi tace"pls idan Babu damuwa zanso ka hadamu da ita wato Kai Mana iso gareta. Diddilo idanuwa Mai gadi yayi yace"bayin Allah ai yanzu shekaru kusan goma Kenan da rasuwar hjy saddiqa........." _Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun_ suka fada a tare suna dafe chest Cike da pretending,babu zato babu tsamanni Shakeerah tafara hawayen munafinci,"Kingani Koh Fauzi Shiyasa naso tun kafin motaho mukira ta mom tace bata da number nata sai dai adrees ai gashinan.

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});