Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 21

Chapter 21

Deejamah Book 1 Complete Hausa Novel 1,285 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

nake sonka Alhj na Saboda wayanka. Shima dariya yayi,Nan suka shiga cikin gidan. Alhamdulillah su Shakeerah sun Isa gida lpy sosai suke farin cikin ganin juna,murna khadee take sosai,lafiyayyan waina da miyan da tayi ta zobo musu. Zama sukayi gaba dayansu,fauzy tadubi khadee tace"khadee me aka girka Mana ne?Murmushi khadee tayi tace"waina ne gashi nan kuyi manage don kunsan vazai taba kaiwa dadin na Shakeerah ba bari na dauko muku man shanun Kila ya soyu. Sosai sukaci wainar gabadayansu daganan aka dasa hirar yaushe rabo,bawa khadee labarin komai sukayi,fauzy tace"gaskiyanki khadee mahaifin ki hatsabibin mutum ne,mgnr zargin Hjy sameera da ake babu karya domin kungiyar su daya,Cike da damuwa khadee ke duban su tace"Dama Daddy baiyi nadama ba,hasalima neman mu yake yakashemu,duk soyayyar dake tsakani na da Daddy?sosai suka fara lallashinta,khadee tace"munsamu dama ta farko Wanda shine mafita Shakeerah da Daddy na yace"Yana sonki mekika ce?Murmushi Shakeerah tayi tace"nace masa yabani lokaci nayi shawara. Khadee tace"Toh shikenan Allah yakara dauramu bisa kan kowa. ______*SAUDI ARABIA*_____ Tas! tas!! tas!!! Karar cover shoe dinsa ne kawai ke tashi,duk da alamu yana da tsayi ko ba'a fada ba Saboda tsayin kafar sa, Wow Masha Allah kirarren namiji Mai jikin Kira ko da ganin jikin sa kasan cewa ana motsawa Saboda yanda yake da Kira,da yawan mutanen asibitin sai gaisuwa suke aika masa dashi,face dinsa babu yabo babu fallasa da alamu dai kaman shi irin mutanen nannne marasa son hayaniya ko wace iri ce,face dinsa zagaye yake da saje Wanda ya kwanta yayi lufff dashi gashi bakin Kirin,mutum ne shi mai manyan idanu ba su cika manya ba,hancinshi har baka sai mouth dinshi dan dai-dai a tsakiyar sajenshi,fari ne shi irin farin larabawan nan. Shirt ne ajikinsa da wandon suit,yayi tokin sai neck tight dake wuyan sa,gefen hannun sa na hanu rike da briefcase na dama Kuma rike da labcourt. Bude office dinsa yayi ya shiga da alamu jiran sa akeyi ma,Bayan ya zauna wani yashigo musabaha sukayiwa juna suna sakin ma juna smile suna tafa hannu,Jalal Wai ina kashige ne kwana biyu nakira wayoyin ka duka switch off,dafe kai Wanda aka kira da Jalal yayi yace"Kai dai Bari Marwan wallahi hutu naba kai na cox kan nawa yana daukan caji fa da yawa ga hidiman yara kafin nafito sai na shirya su,daganan sai su wuce school. "Af dama nasan hakan zai faru, kirir-kiri kaki daukan shawara ta ne,na e ma kadauko matar ka Amma kaki,wannan hidiman mata ne ba namiji ba. Murmushi Jalal yayi yace"bazaka gane ba Jalal Amma kabari idan lokaci yayi zaka fahimci komai. Kada kai Marwan yayi yace"Ok tohm shikenan fatan kayi breakfast koh? "Yeah da zan fito nasha coffee nd biscuit yayi maganar yana daddana laptop din da ke gaban sa. Marwan yace"yadai kamata kadinga breakfast mai kyau gasu Chip's su Arish nd egg,plantain but kadena Shan wani coffee da biscuit kullum,kasan cewa anjima munada tiyata da zamuyi har uku koh? "Yeah I know,yayi maganar batare da ya dago ba,dage kafadu yayi Marwan yafita domin yasan halin Abokin nasa. Wayar sa ce tafara neman agaji hannu yakai tare da dauka, wifey yaga an rubuta,picking call din yayi tare da karasa a kunnen sa, kuka ake sosai daga can bangaren,haba haba Abban siyam mai na akaita maka daka zabi rabani da 'yayana?wallahi kadawo mun da yarana wallahi nayi regret din Auran ka tunda kai tarbiyyan wancen tsohuwar kawan ce...... Bata karisa ba yadaka mata wani tsawa duk da cewa a waya ne Amma Sai da tsoron da taji ya bayyana. Jalal ya hade fuska kamar tana gaban sa cikin wani irin murya yace"Laweezah!!!! Ina fada miki duk wani rashin kunyar da zakiyi ya Kare a kai na yadena taba fulani domin ba sa'ar ki bace,fulani itace dalilin aure na dake,domin da bata matsamun ba da bazan Aure gidahuma jahila mara tarbiyya irin ki ba, maganar yara kuwa bazan dawo dasu ba,wallahi muddin kika gansu a 9ja hutu muka zo,kuma zamu koma. Idan kinyi hankali Zaki dinga Zama da yaranki,nan ne bazan kawo kiba kidau mataki,Yana gama mgnr ya kashe wayar sa gabadaya. Dafe kai yayi yana kyamar hallaya irin na Laweezah Sam ballagaza ce,tumowa yayi da mgnr Hjy shamsiyya(Duk wanda yahada iri da Inna Baraka sai yayi nadama),a hankali ya furta nima gani nan ina nadamar. ______ _NIGERIA_ ______ Laweezah wannan wani irin maganar banza ce kikce wai yasake ki? Ashe dama baki da hankali?kin manta mahaifiyar ki Sam tatsani farin cikin ki da zarar an sake ki murna zata fara ita da sauran 'yan uwanki,dariya wata kanwar maman Laweezah tayi tace"Hjy kenan kintaba ganin uwar da tahaifi danta ta tsaneshi,sai dai tatsani halinsa.......ke dallah ki mana shiru ai duk halinku daya don Allah tashi kibani waje salima. Salima auta ce a wajen Hjy Baraka Kuma sa'ar Laweezah ce sai dai ba sunfiye shiri bane tunda halinsu ba daya ba, mikewa tayi tace"Allah yabaki hakuri don Allah. "Eah din Ameen Hjy Baraka ta fada,tabe baki Laweezah tayi tace"munafuka ba. Hjy Baraka tace"Rabu da ita hassada take miki Saboda ita har yanzu babu mashin shini. Dariya Laweezah tasa tace"Hjy Autar ki cefa,ni ban taba ganin inda mama bata shiri da Autar ta ba sai ke da salimah, Hjy Baraka tace"ita dince batajin magana halin mu da ita ba daya bane,keda halin mu guda ba gamu a inuwa guda ba? Laweezah tace"Hakane Kuma. Sosai su Shakeerah suka maida hankalinsu akan Exam din su duk da cewa yau saura kwana guda su gama,Kuma hutun 2weeks suka samu,bangare daya Kuma suna kokarin ganin sun nemawa juna mafita, Daddyn fauzy ne yakira,sisai sukayi video call dashi gaba dayansu har da mommy din ta(kada ku manta marikan ta,iyayen gidan kanwar ta dijee),Nan Fauzy ta rokeshi kan yabarta wannan Karan tayi hutun ta a gidan su Shakeerah.......shiru yayi sai can da kyar ya amince shima sai da sukayi karyan Ammin Shakeerah Babu lafiya. Bayab sun gama Exam a Ranar suka wuce zaria Cike da farin ciki a zukatan su,da kokarin ganin wannan hutun zaisa su gano mafita akan Daddy. Tafe suke a mota da yake hanyar kaduna duk ana gyara sosai Shakeerah ke gudu akan titin,juyowa fauzy tayi ta dubeta tace"Shakeerah Anya wannan mafitar da muke nema basai anhada kai da wani ba? Shakeerah tace"nima tunanin da nake kenan,abinda za'ayi yanzu mufara wucewa gidan su khadee don tattaunawa da Ummi. Gabadaya suka amsa da toh,koda suka shigo Zaria yamma tayi sosai domin sallar magrib wasu masallatan ma Sukeyi,direct tudun wada suka nufa. Sosai ummi da sajeeda suka tarbi su Shakeerah cikin farin ciki,sallah suka gabatar sannan sukayi wanka sukaci abinci,Bayan anyi sallar isha'i nan su Shakeerah suka bawa Ummi labarin gidan Daddy da bukatan sa akan Shakeerah. A jiyan zuciya Ummi tayi tace"lallai Shakeerah kunyi kokari barin ma ke,ina son alakarki dasu domin kina basu karfin gwiwar yin Abu da ciremusu tsoro,to yanzu maganar Auren naki da yace zaiyi fa?ki amince tanan ne kawai zamu iya Samun mafita kije kiyi shawara da Ammin naki. Diddilo idanuwa Shakeerah tayi tace" _I NEED UR COMNENT_ Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami πŸ–‹οΈ Yafi takobi πŸ—‘οΈ πŸ’•πŸ’• ❀️ [7/18, 2:05 PM] XahrattyπŸ₯°πŸ˜˜: πŸ’βœ¨ *DIAMOND LADIES* πŸ’βœ¨ ( Daukar Fansa ) Story& writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL ______✍🏽______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* πŸ”±(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});