Chapter 16
Chapter 16
Hjy Baraka ake da iyalenta kamar ba 'yan uwa ba,kinganmu nan uwa daya uba daya muke da bala'i Hjy Baraka tasa Jalal babban jikan fulani ya auri Laweezah ba don Yana sonta ba,shine fa kullum Basu da aiki sai korafe-korafe. Shakeerah tace"Allah ya kyauta Babu mnyan 'yaya ne? Matar tace"Akwai mana Aida ana biye tatasu da tuni anyanke zumunci,Bata da kirki Saboda taga fulani nada hakuri sosai. Dayan matan tace"Shiyasa Sam Auren zumunci yafita kaina domin gashi a dalilin halinta na yanke zumunci da ita. Shakeerah tace"Allah dai ya kyauta kawai shine abin cewa itakuma Allah ya shiryeta. Ameen gabadaya suka fada. Duban fulani Shakeerah tayi tace"Fulani zan koma school gobe insha Allah. Duk cikansu fatan alkhairi suka yima Shakeerah sannan tamusu sallama tafita. A harabar gidan taga motoci sun shisshigo akalla zasuyi motoci uku a tunanin Shakeerah ko Hjy Baraka ce tadawo da iyalenta,sai Kuma taga maza ne manya sosai su uku domin zasu haifeta ma tare da mata biyu. Wucewa part dinsu tayi cikin Sauri. Sukuwa da sallama suka Isa part din fulani kyawawan yara masu tashe da jindadin rayuwa,ilimi,kyau,addini,uwa uba Nairaaaaaaaa. Cikin Sauri duk cikansu sunkai su biyar suka Isa wajen fulani suna tambayarta meke faruwa? Itadai fulani Bata tanka ba tace Babu komai,kuyanginta gidan suka shiga hidima dasu sosai. _WACECE FULANI_ Sarki Abdallah Sarki ne na garin itophia Sarki ne Mai adalci Wanda iyayenshi shi kadai suka Haifa, yataso talakawa na alfahari dashi a rayuwa Yana kula da talakawa,duk zaluncin da sarakan Bayan sukayi shi Sam baiyyi ba. Akwana atashi Allah ya azurta shi da 'Yaya hudu duka mata,da hjy Rahma (Fulani) da Hjy Baraka da Aisha sai autansu hjy Maryam. Manyan garin azzalumai da Basu son mulkin adalci sukayi kokarin kashe Sarki Abdallah,suka bashi zabi ko ya zabi iyalensa ko ya zabi mulki. Jin haka yasa Sarki Abdallah ya hakura da mulkin ya zabi iyalensa,shi yasanya ma fulani suna fulani,sannan suka bukaci ya bar kasar sa na haihuwa tare da dukiya Mai tarin yawa. Nigeria yadawo da Zama ya sauka a garin maidugri,Bayan zuwansu da shekara guda mahaifiyar su fulani ta rasu Sarki Abdallah ya cigaba da kula da 'yayansa mata,jikin hukuncin Allah,Allah ya kawowa fulani miji hamshakin mai kudi da sarauta domin Dan Sarkin ne Alhj yunusa Hameed dan garin Senegal,kasuwanci yakawo shi Nigeria nan yayi arziki sosai Bayan iyayenshi sun rasu. Sosai yake son fulani da Bata kulawa na musamman a haka aka daura Aure cikin hukuncin Allah tasamu cikin danta na fari Bayan tahaifeshi yaron ya rasu. Still ta kuma Samun cikin Allah ya azurta ta da haihuwan 'ya mace hjy Kaltume kyakkyan jinjira me sirrin wani irin kyau,bayan ta haifi Alhj kabeer shima kyakkyawan namiji mai jida kyau,sai Alhj Khamees shima haka,sai Hjy shamsiyya sai Alhj Ahmad shine autan ta. Itakuma Hjy Baraka tayi Aure a garin zamfara wani kauye ne duk da bawani kauye bane can-can Amma Basu da wani wayewan kai,sai dai suna takama da rashin mutumci 'yan garin basa saurarawa kowa,dama Hjy Baraka fitinanniya ce tafison kanta akan komai. Sam 'yan uwanta da mahaifinta Basu Jin dadin hulda da ita don ya zame musu Dole ne,itama hjy Aisha tayi Aure sai dai bata taba haihuwa ba, Hjy Maryam ma tayi Aure don tanada yara biyu. Hjy Kaltume dan ta daya ne a duniya Jalal Bayan ta haifeshi tayi aure ta auri wani babban costume yanzu suna garin Abuja,domin mahaifin Jalal dan Sudan ne,shine babban jikan fulani jalal daga baya Allah ya ma mahaifinsa rasuwa,itama babban jikan Hjy Baraka itace Laweezah tunda tataso takeson Jalal duk da cewa shi Sam baya sonta,hasalima dabi'unta da habbit nata sam basuyi masa ba,bata cikin tsarin kalan matan da yakeso,hakanan yayi ma fulani biyayya ya aureta domin yana kallonta kamar uwace a gareshi. Dalilin zuwan fulani kaduna kuwa nan mijinta ya'ajeta tare da kuyangi,ko Bayan rasuwarsa batai Aure ba. A hakadai aka daura Auren Jalal da Laweezah Yana karatun Dr ne a Saudiya bangaren zuciya,sai dai Sam bai tafi da Laweezah ba.Sun haifi yara biyu Bayan sun girma yatafi da su saudiyya yasasu a MAKARANTA to shine rikicin da akeyi suna cewa fulani ke zugashi. _CIGABAN LABARI_ Nan su hjy Maryam suke sanar da su Alhj kabeer duk abinda yafaru,da labarin Shakeerah ajiyan zuciya hjy Kaltume tayi da yake macece mai sanyin hali,hjy shamsiyya ko Banda huci Babu abinda take tace"Jar uba! Aiko da inanan sai naga ubanda yatsaya mata Kuma wannan yarinyar Allah ya mata albarka. Cikin sanyin murya hjy Kaltume tace"Fulani ina yarinyar take ne?Fulani tace"Suna can bangaren nan bana cemuku na siyar ba?duk cikansu suka ce suka amsa da hakane Akira musu Shakeerah,Kiran daya daga cikin kuyangin fulani akayi akace ta Kira Shakeerah,cikin biyayya ta amsa da to ta fita. Shakeerah kuwa Bayan fitan ta direct part din su ta nufa ta cidda Ammi tana kitchen tana hada Mata dambun naman zabi Wanda zata tafi dashi gobe,Shiga kitchen din tayi tafara tayata aiki sunayi suna hira batare da tasanar ma Ammi abinda yafaru a part din fulani ba, knocking din kofar Falon su akafara,cikin Sauri Shakeerah ta nufi kofan tare da budewa. Kuyanga ta dubi Shakeerah tace"ranki yadade fulani na san ganinki cikin gaggawa,da Sauri Shakeerah tace"toh kice mata ganinan. Juyawa tayi ta Shiga bedroom dinta ta dauko long hijjab dinta pink colour ta zira,Shiga kitchen tayi ta sanar da Ammi xataje sashin fulani tana kiranta,da toh Ammi ta bata amsa,har ta juya zata fita, Ammi ta kirata. Dawowa tayi sannan Ammi tace"bude cikin carbinet dinnan ki dauko min karamin bowl. Budewa Shakeerah tayi ta Ciro taba Ammi,amsa tayi ta cika shi da dambun nama,sannan tace ta dauki jug ta zuba mata kunun ayar da tahada a cikin firij. Duk haka Shakeerah tayi ta dauki Kayan niki-niki ta nufi part din fulani,da alamu bakinnan na falon,kamar ta juya sai dai ta daure da kyar ta nufi cikin farlon. Da sallama tashiga,duk cikansu suka amsa tare da zubama mata idanuwa sosai,kura mata idanu tayi gabanta na faduwa duk da tasan face din sai dai ta rasa inda tasan face din. Karisowa tayi tana murmushi ta nufi wajen fulani,dire Mata jug din da bowl din d ke rufe da murfinshi tayi tace"fulani gashi inji Ammi na,cikin Sauri Hjy kaltume ta Kuma kallon ta,tasan muryan sai dai ta mance wacce tasani da muryan. Shakeerah ta juyo ta gaida duk bakin dake falon,da Murmushi ko wannen su ke amsa was,hjy shamsiyya tace"munji abin arzikin da kikayi 'yan Mata,yabaki miji nagari mai kula dake. Shiru Shakeerah tayi tana me amsawa da ameen a zuciyar ta,hjy shamsiyya tace"kinsan me nakeso dake?girgiza Kai Shakeerah tayi. "Ga amanar fulani nan a hannunki duk Wanda yayi mata ba dai-dai ba kici kaniyar sa kada ki saurarawa kowa ninasaki. Murmushi Shakeerah tayi tace"Aunty aini ko ansa ni ko ba'asani ba,ba'a Isa ataka fulani Ina wajen na kyaleva Koda kuwa kashe ni za'ayi. Dariya ma abun yabawa su Alhj Khamees dariya, Alhj Ahmad yace"hjy shamsiyya adaiyi hudubar arziki Koh? Duk cikan su dariya sukasa hjy shamsiyya tace"Wallahi abun ne daban haushi sai kace Laweezan 'yar gwal ita ba kyau ba ba komai ba,Wallahi bacin zumunci da tuni yadanna mata saki kowa ya huta. Shakeerah tace"Fulani gani. Dafa kanta fulani tayi tace"tashi kitafi Shakeerah Allah ya Miki albarka,kicema Maryam din ina gaisheta
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30