Chapter 13
Chapter 13
a gidan da bana Ubanta bane?Kuma ai tsintacciyar mage bata tutuya da gidan uban wani. Duk cikansu amsar da taba Baba Ayuba yamusu Dadi idan kacire magajiya talatu da baba sani. Baba Sani yace"sam ke baki da kunya kinyi gadon uwarki Sam bakiyi na Ubanki ba. Shekeke Shakeerah tadago tana dubanshi"hmmm baba sani kenan babban da be girmama kansa ba Babu yanda za'ai na kasa dashi ya girmamashi,maganar rashin kunya Kuma ban gado uwata ba balle ubana tunda duk cikansu Basu da wannan halin,ku na gado sarai,tayi maganar tana nunnunasu da makullan motan ta. Duk cikansu a jiyan zuciya sukayi baki yamutu,Ciro a tamfofin tayi taba magajiya talatu baba sahura sannnan tabisu da dubu goma gama taji suyi dinki,aiko nan magajiya tasaki guda godiya gabadayansu Sukeyi Mata. Dubu talatin-talatin taba mazan,baba habu ne kawai yayi godiya suko sauran cewa sukayi a cikin gadon dan uwansu ne,mikewa tayi zata tafi tadubi su magajiya tace"Wai Ina su Aunty raheena ne?magajiya tace"Aiko tatafi bikin kawa itaakuma salamen talatu taje gaida maman saurayinta batajin Dadi,hadeezan balaraba Kuma 'yar wahala tatafi makarantar boko. Shakeerah batace komai ba tamusu sallama tafito har zaure suka rakota, Baba Ayuba ya leko yace"wani zuwan kada ki kuskura kizomin Babu mijin Aure,sai da Shakeerah tasaka space dinta sannan ta'aje jakanta tataso ta matso har gabansa tace"Baba Ayuba idan nadawo ka koreni gabadaya sandarewa sukayi taja motarta tayi gaba. Sai Bayan tafiyanta yaketa zage-zage Kan wai Shakeerah ta rainasa,Babu wanda yatanka masa sai abokin haushinsa baba sani. Sai wajen 6 ta Isa gida gate din fulani tashiga da motarta,fitowa tayi a gajiye ta nufi hanyar part dinsu,sai dai Jin hayaniya a part din fulani yasata juyowa ta nufi hanyar part din. _I NEED UR COMMENT_ Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami🖋️Yafi takobi🗡️ 💕💕 ❤️ [7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨ ( Daukar Fansa ) Story& writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL ______✍🏽______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* 🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah)) *_T.W.A_* _________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________ Marubuciyar⬇️ _ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_ *DA* _ _MIJIN ZAHRA_ *Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.* Bismillahir-rahmanir-raheem. *Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai*.... Page:1️⃣6️⃣--1️⃣7️⃣ ___________A haka rayuwa ke tafiya gaskiya Abba yabar dukiya sosai munsamu,a gefe daya na adana files dinda Abba na ya bani ajiya. Rayuwa muke mai cike da farin ciki fulani kuwa tazama tamkar wata step mother dita,tanamun Abu irin na da da mahaifi tana bani kulawa,har yau ban taba haduwa da family dinta ko daya, business din Abban mu tasamu wani Mai Amana tadora shi akai muna cemasa Abba kabeer Yana kula da dukiyar mu damu kammu,taso Auren Ammi ta dakatar dashi tunkafin tafiya tayi nisa domin bazata sake aure ba tace,zuciyarta kuwa tace Abba yariga yatafi dashi Babu yanda za'ayi wani yasamu makwafin zama. Lokacin Exam yazo muka yi jarabawar fita daga secondry,jamb nafara Alhamdulillah nasamu score masu kyau domin nafita da 240 wannan DALILIN yasa fulani tabani gift dinta ba komai tabani ba sai mukullin mota hadaddiya kirar KIA gata derk Ash sosai. Nayii waec da neco dama A.B.U da KASU da B.U.K nacike. Koda nagama Suma gaba daya na cinye don haka fulani tasama mun gida a kaduna na sannan aka nema mun add mission a kASU na samu. To wannan shine cikakken tarihina,yanzu kuwa kusan wasan zai fara diamond ladies. Su Fauzi sukace haka ne,gaskiya Shakeerah kema Kinga rayuwa Amma tunda duk kanmu zamuje weekend gida mu Bari mudawo sai asan abinyi. Shakeerah tace"hakane to aini da khadee gari Daya zamu. Fauzi tace"hakane kuwa na manta ba 'yar bauchi bace da mun jera. Dariya khadee tayi Tace"Hakane to babe's yanzu sai mun dawo tukuna za'ai solving din matsalolin mu? Shakeerah tace"Har sai mungama Exam ma domin bazamu hada karatun mu da matsalarsu ba,matsalar fah ba karama bace Dole muna bukatan kwakwalwarmu tayi caji domin muna bukatan temako. Gabadaya suka hada baki wajen fadin"hakane daimond love Dole mudauki fansa,a dade anayi sai gaskiya. Sosai suka mai da hankali wajen karatun su,weekend kuwa ya zagayo da yake duk ranar Friday suke tafiya gida sannan paper daya sukayi,shiri suke sosai duk cikiansu. Sai da suka fara zuwa suka saka Fauzi a motar gombe sannan su sukayi Zaria sai wajen seven suka iso,direct Shakeerah tudun Wada takai khadeee Bayan ta sauketa,ita kuma ta wuce gaskiya. A dai-dai randar agwaro wani Mai mashin yazo da gudu saura kiris ya buge Shakeerah da Mutane da dama ma,juyowa yayi yafara zage-zage Wai ana ganinshi ba'a kaucemai ba gaba daya ya hada goslow 'yan kasteliyan dake wajen duk sunkasa tabuka komai Wai Dan daba ne kada mutum yayi maganar ya Burma masa wuka. Cikin bacin Rai Shakeerah tafito daga cikin motar ta,tsiya tafara yimai akan hada gaslow din da yahada,Aiko dama jiran Mai tankasa yake,Nan kuwa yafara duddura ma ta zagi Wanda ko jare bazai ciba. Ranta ne yagama baci Aiko ta bashi punch a hanci,ihu yasa yakuwa zaro wuka yayo Kant dashi da niyyar cakamata a ciki,aikuwa Allah yabawa Shakeerah sa'a ta samu hannun ta murde har Sai da wukar ta Fadi,sannan ta murde hannun sai da ta balle Tace kassss! Da yawon mutanen wajen mamamki suke yaza'ayi wannan 'yar ficiciyar yarinyar nan tayi fada da shago?nan kuwa akadinga murna ansamu mai cin ubanshi. Ihu sosai shago yakeyi Yana Bata hakuri domin kokarin karya dayan hannun takeyi dubanshi tayi cikin fresh voice nd sweet Colin natsuwa tace"Meyasa Mutane Sam basu da tunani ne son zuciya yayi yawa a gari inbanda haka baka da wani isashshen sana'ah,makarantar bayi kuke ba sai dai zaman banza da neman magana agari inbanda haka Meye naka na Tara dubban jama'ah haka ,kaduba Mana,tayi maganar tana nuna masa mutanen wajen. Muryansa na rawa yace"don Allah kiyimun aikin gafara ki yafemun don Allah. "Ni daka ganni am simple kanemi gafara da yafiyan wadnda kataba yimawa ne but ni Babu abinda kamun a yanzu,fatana dakai kanemi abin yi ka natsu kasan Allah ya faku. "Insha Allah nayi Miki alkawarin zan shiryu da yardan Allah to jirani,Shiga motar tayi ta dauko Masa kudi dubu goma casss tace"yaje yayi magani,mutanen wajen kusan Rabi duk sai da tabasu sadakan dubu biyar-biyar sannan taja motar ta tayi gaba. Wani yadaga murya a cikinsu yace"Yarinyar Alhj Muhammad Adali ne,Aiko nan akkafara yaban mahaifinta akadinga Masa addu'o'i,ita Kuma akadinga sa mata albarka. A gajiya tayi hon a bangaren su ta Shiga cikin Falon tundaga Nan tafara Jin ana ta hayaniya kamar muryan baba Ayuba taji, jitayi yana cewa"don munafunci irin naki algun guma kin hau dukiyan Dan uwan mu kinyi kane-kane dashi kin dauki fitsararriyar 'yarki kin sakata a makaranta makaranta ko karuwanci? Baba Sani yace"Ayuba bama wannan ba abin da ke bamu mamaki yanda ta maidamu kamar almajiranta idan munason wani Abu sai munzo mun tambayeta,to baki Isa ba banza tsintacciya kawai,tsintacciyar mage,dama ance tsintacciyar mage Bata mage......Cike da bacin Rai Shakeerah ta buga kofan falon duk cikansu suke duban ta Ammi kuwa kuka take ganin Shakeerah yasa cikin Sauri ta goge tears din, Shakeerah tace"ai gwanda tsintacciyar mage Akan wasu masu iyayen domin ku naku matan Babu abinda suka Sani sai duddura muku
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30