Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 23

Chapter 23

Deejamah Book 1 Complete Hausa Novel 1,283 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

jiyar zuciya ya sauke Wanda da ka lura zakasan cewa da kyar yakeyin magana"Saboda inajin kunyar duniya,Ina tsoron mutumcina ya zube a idon duniya,na manta cewa da kunyar lahira gwamma na duniya. Dan jaridar yace"To Allah gafarta malam Aida an nemeka anrasa ko,ko zaka iya sanar damu inda ka gudu? Girgiza Kai yayi yace"Sanar daku bashida amfani,nidai abinda nasani wasu 'yan mata suka biyu ni har inda nake suka daukeni suka kaini kango,bayan sun min dukan tsiya shine suka konani,har yau Cike nake da mamaki da tsoro, Ina tunanin Anya su din mutane ne?saboda suna da karfi,sannan kuansu yayi yawa,a tunani na aljanu su suka aikata mun wannan lamarim. Dariya Dan jarida yayi sannan yace"to masu aikata wannan lamarin da masu niyyar aikatawa,Kila wannan abun fa da yafaru da Allah gafarta ya zame muku ishara a gaba. Nan dai aka gama labaran aka gama labaran,mikewa shakeera tayi tare da shigewa kitchen,ita kuwa khadeeja banda kuka Babu abinda takeyi saboda ita khadeeja akwai tausayi. Tsaki Fauzi taja tace"kedai Kika sani Sai kace ba kece mai soya mai a risho ba.....khadeeja batasan sanda ta fashe da dariya ba,don maganar ya bata dariya. Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi🗡️ 💕💕 ❤️ [7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨ (Daukar Fansa) Story&writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL _______✍🏽_______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* 🔱(( Home of Expert and talented writers,da tamvarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah)) *T.W.A* _________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________ Marubuciya:- _ *A DALILIN 'YAR TSUNTUWA* _ *MIJIN ZAHRA* *ND* *NOW* *DIAMOND LADIES* (Daukar Fansa) *Littafin diamond ladies (Daukar Fansa)na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari 100 na waya ta wannan number 08060719719,sai nayi adding dinsa a group din* Bismillahir-rahmanir-raheem. *Da sunan Allah mai rahama mai jin kai....* _FREE PAGE_ 3️⃣0️⃣--3️⃣1️⃣🖊️ ____________Daddy tagani Yana kokarin kai hancinshi Kan shoulder din ta,cikin Sauri ta goce tare da janye jikin ta daga gareshi,kallon ta yayi idanunshi ya rine yayi ja jazir kaman banashi ba,a hankali yake takowa inda Shakeerah take. Duk da cewa ta tsorata da yanayin nasa Amma Sai ta dake tare da kura Masa Ido ko kiftawa batayi,jikinsa ne yayi matukan sanyi a hankali ya zauna kusada ita a gefen gadon. A hankali yace"pls my Darling kiyi kokarin bani hakki na mana,a firgice Shakeerah ke duban sa tace"Papi???? Takira sunanshi da alamun question mark. "Papi nace maka Ina period pah. Daddy yace"Don kina period sai akacemiki ba'a kokarin sex a haka? Wani kallo Shakeerah ta jefeshi dashi na kana da hankali kuwa,a hankali tace"yau da asuba kaje ka tambayi liman hukuncin mai gidan da yasadu da iyalinsa tana period. Shiruuuu papi yayi kamar mai tunani zuwa can "My Darling kenan kina burgeni kodan bakin nan naki na tsiwa kekoh?yayi maganar cikin sigar wasa yasa Yana nunata. Itama Shakeerah da murmushin shin tabishi zuwa can tace"pls Papi kabani pad Ina Jin yanazuba sosai,mikewa Daddy yayi cikin kasala yaciro wani Dan karamin key a aljihun shi,wani walkiya Dan karamin key din yake kamar diamond. Bude wadrope din yayi sai ga wani Abu ya bayyana kamar laptop domin har wasu harufa za'asa,Jim Daddy yayi ganin haka yasa Shakeerah dukar da kai,juyowa yayi ya tabbatar da Bata ganin shi sannan yasaka haruffan guda bakwai duk da cewa bansan meyasa ba Kuma bansan meya a ciki ba,sai dai da alamu wadrope din nan ba'abin arziki bane a ciki. Sai da yagama rashin gaskiyar da zaiyyi Sannan ya ciro wata Riga a Leda sai packet din pad guda ya maida kofar ya rufe. Karisowa yayi kusa da Shakeerah yace"Darling ga pad can kidauko sai wancan nyte gown din shima kidauko kisaka yanzu.Karkatar da wuya Shakeerah tayi tace"Why not bazaka dauko min ba papi?tayi maganar cikin muryan shagwaba. Murmushi Daddy yayi sannan ya juya,dauko pad din yayi da night gown din yabata,amsa tayi ta mike tace"Sai da safe papi pls bani key din part Dina. Da alamun baiso barin ta tafiya ba sai dai yakasa musa mata duk abinda tace Masa. Gudu-gudu Sauri-Sauri Shakeerah ta shiga part dinta,wani kamshi ne Mai Dadi ya bugi hancinta lumshe idanuwan ta tayi a hankali sannan tabude,farlon madai daici ne sai dai yanada matuoan kyau sosai,sai da tazaga ko Ina sannan ta shiga toilet bata saka pad din da Daddy yabata ba domin dama tana tafe Dana ta pad din a dalilin wani tambari da taga ansa Mai Kan maciji yasa Taki saka pad din Daddy,Ciro night gown din tayi daga cikin ledar shima tambarin Kan maciji ne a jiki. Wani tunani tafara wanda bansan metake aiyanawa ba,tana rigar kallon rigar Sani ko antaba yimata nayani akan sa. Toilet ta shiga tasake wanka sannan ta dauro alwala,app din complete Qur'an ta bude a wayar ta sai karanta was takeyi,Bayan ta kammala tayi addu'o'in bacci sannan ta shafe ko Ina ma jikin ta dashi daukar rigar night gown din ta tayi tasaka, harta ja bargo sai can ta tuna key kawai tasaka,mikewa tayi cikin Sauri ta saka sakata a kofar sannan tayi ajiyar zuciya. Hawa gadon tayi tafara kokarin yin bacci don shi takeji sosai,Bayan takashe fitilan dakin da take,gani tayi an wulkita ta window dakin ta da alamun inuwar mutum zuwa can sai Kuma shiru yabiyo Baya,ba a dauki lokaci ba taji alamun an bude kofar farlon ta. Kirjinta ne yafara bugawa jikake fat! fat!! fat!!! A hankali ta sauka akan gadon ta cikin sando tafara leka jikin kofan ta,cikin Sauri taka baya a dalilin mummunar halittar data hango ya tunkaro dakin ta,ruwan maganin da fulani ta anso mata ta dauko a jarka aikuwa tabude tadinga yayyafawa a jikin kofan ta da bakin kofan nata. Wani murya ne mai amo Babu dadin ji ko saurara ya kwala wani irin kara a dalilin karisowa bakin kofar,a hankali kasan dakin yafara wani irin jijjiga,sosai Shakeerah abin ke Bata mamaki sai kace a film ko a labaran da ake badawa. Can Kuma Sai shuru wani Abu bai sake faruwa,a hankali aka fara ihu a farfajiyar gidan Daddy,cikin Sauri Shakeerah ta nufi window dakin ta,wasu irin Mutane masu wani irin halittu taga sun nufi part din Daddy su kusan bakwai,zuwa can Hjy sameera itama tafito daga part din ta tashiga na Daddy. Shiru Shakeerah tayi tana mamakin shaharan su Daddy tunda lamarin har yakai suna hulda da aljanu. A bangaren Daddy kuwa Bai San wani yashiga part din Shakeerah ba,domin shi muguwar sha'awar ta ce takama sa Wanda yasashi baccin wahala batare da ya shirya ba. Karan da yajine yasashi mikewa da Sauri ya bude window,Karan ihun dodon kungiyar su yakeji kuma da alamu a part din Shakeerah ne tunda gashinan wani irin hayaki ya turnike,zuwa can kasan gidan sukaji yafara girgiza, Murmushi Hjy sameera tayi tace"nasan yanzu aljani lamzit yagama Miki aiki don haka yarinya sai dai uwarki ta haifi wata bake ba,tasake sakin wani shu'umin Murmushi tace'Daga zuwan ki kinemi ki fadamun mgnr banza,to zanfara maganin ki wannan somun tabu ne. Daddy kuwa ganin abinda ke faruwa ba kankanin firgita shi yayi ba,burin shi Allah yasa Shakeeran shi tana lafiya Lou, nufar hanyar fita yayi,a take zoben hannunn sa yayi haske,kirjin sa ne yabuga domin da alamu 'yan kungiyar su suna tafe tunda hasken ring din is too much. Aikuwa ilai Mr Patrick ne da wasu su shida,sai dai sun canza

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});