Chapter 7
Chapter 7
Suma matan makota da suka shigo ko wacce mikewa tayi ta fita,baba ladi tace"Eah MUNAFUKAI a gayas shegu. Inna tace"Ai a sararru ne masu kwana da Ido daya. Da nida Yaya kaltume da dijee kuka muke sosai,Ina nadama da danasanin wannan rayuwar na ahalinmu. Washegari da safe muka shirya nida qanwata muka nufi gidajen aikinmu,domin bamuga amfanin Zama da matsiyata irin ahalinmu ba,baba ne Kuma ya rasu Babu abinda yake bukata sai addu'ah. Dijee nafara rakawa gidan aikinta,daganan Sai na na wuce nawa. Tabbas bazance muku banyi dace da gidan aiki ba,sai dai Sam matar da nakewa aiki batasan darajar Dan Adam ba ita da yaranta,idan Ina aiki bana fuskantar komai sai wulakanci da kyara. Inda Allah ya temakeni akwai mahaifiyar Hon Ahmad itace take taka musu burki. Abinci kuwa sai anci an rage ake bani,ban damuwa nakeci saboda a gidanmu ko kwantan kwatan shi bazan gani ba,wata Rana na ragewa khadeeja wata Rana Kuma Yaya kaltume. A daddafe nayi wata Daya a gidannan,albashina aka bani dubu goma,nayi farin ciki sosai,ji nake kaman anbani wan manyan kudi. Dijee itama dubu goma aka Bata a gidan da take aiki sai kwancen Kaya kala biyar. Duk da cewa girman mu Daya da karamar kanwar tawa sai tabani kala biyu a cikin Kayan,muka gyara dakin baba muka koma. Dama abinci nace muku andade da ciremu a cikin 'yan gida. Rayuwa muke mai cike da nishadi,Ina manta Ina da damuwa sai na je gidan aikina,mahaifiyar mu Bata damu dajin matsalolinmu ba,a haka nafara al'ada Wanda da temakon Yaya kaltume nasan komai,ita takasance mana tamkar uwa,ita ke mana nasiha danuna mana tsoron Allah, barimma ni Dana fara wannan Jan motar,tafi jamun kunne saboda gidan danike aiki suma 'yayan Allah shirya ne,mazan duk suna neman mata. A kwana a tashi muka dauki shekara da fara aiki Babu karatun Arabic ta bangarena balle na boko,itako dijeee gabadaya tana xuwa makarantun,ta cika tazama big girl Bata da matsala wajen uwar daki da mijinta,sun dauketa tamkar 'ya! Da yake Basu taba haihuwa ba. A hankali tafara koyamun karatu daga bokon har islamiyar. Hmmmmm da mahaifiyar mu a raye gwanda Babu ita,domin mun koma kamar abokan gabarta,gashi bamusan dangin mahaifiyar mu,ita kanta tsintar ta akayi,mahaifiyar babam mu. Wata rana haka na tashi da ciwon ciki Wanda yahanani zuwa wajen aiki,Kuma idan banje ba Koro na za'ayi Bayan Ina samu Ina rufawa kaina asiri nida kanwata. Dijee na roka Wanda takoma amfani da khadeeja Aliyu,Akan tajemun gidan aiki a makofin ni A take anan Fauzi da fashe da kuka Wanda yasa Shakeerah da khadee Suma kukan,ta cigaba da cewa"da nasan abinda zai faru da khadee kenan wallahi da ban turata gidan aiki ba. Domin kuwa Daya daga cikin yaran Hon Ahmad yayimata fyade na wulakanci da tozarci,Wanda tunda ya haike mata sai da Allah yayi mata rasuwa. Dalilin haka Inna ta tasake tsanata sannan Tace nabar gidan ta. Kada kumanta a kasar nan mai hali shine Mai gaskiya,don haka kirir-kiri akaki hukunta yaron Hon Ahmad,sannan sukace karyane take tsintar ta sukayi,Bayan masu aikin gidan da masu gadi sun sheda haka. Inna kuwa korar cin Kare tayimun Wanda zaka rantse ba ita ta tsuguna ta haifeni ba,Yaya kaltume na kuka Ina kuka mukarabu,sai dai takara jadadda mun duk inda zanje a fadin duniyar Nan nakula da kaina da rayuwata sannan kada na manta da mahaifata,nayimata alkawarin haka mukarabu. Rasa inda xan nufa nayi,daga karshe nayanke hukuncin nufar inda khadeeja ke aiki,matar Cike da mutumci ta tarbeni tana tambayar Ina khadeeja? Anan nake sanarda ita da mijinta abinda yafaru. Tayi kuka sosai,saboda sunji mutuwar khadeeja. Daganan rayuwata ta koma hannun Daddy Alhj Kamal da mama hjy rahama,tunda ga wannan ranar ban sake komawa takan gidammu ba,daga karshema garin fantami muka koma da maza. Sai dai na dauki alkawarin daukar fansan abinda akayiwa dijee Ina Mata addu'ah ita da baba. To wannan shine labarina. Gaba daya ajiyan zuciya suka sauke,itako khadee Banda kuka Babu abinda takeyi. Shakeerah cikin bacin rai da kunar zuciya tace"tabbas dole mu dauki fansa a rayuwar mu,Amma meyasa Kika CE kinada matsalar matar uba? Fauzi tace"gud question daimond lady dama nasan a halinki sai kimmun tambayar Nan,to abinda yasa da naso boye Miki asalina ne,Amma Dana fahimci mu din hadin Alla NE sai na bayyana Miki komai. Shakeerah tace"Kai duniya Ina Zaki damu?wannan kalubale da muke fuskanta a rayuwarmu,diamond ladies so nake mu dauki fansa Wanda tunda ake ko a tarihi ba'a taba jinsa sai dai dole ya Zama na da temakon wani namiji. Shiru sukayi gabadaya ko wacce tana thinking...... Shakeerah tace"yauwa khadee kince brother naki barrister ne,ya kamata ace mun fara hada kai dashi tunda babban lawyer ne ko ya kuka ganin babe's? Cikin Sauri sukace gsky ne hakane. Shiru sukayi gaba dayan su ko wacce da abinda ke damunta. Shakeerah tace"ya kamata mu kwanta saboda school gobe da wuri zamu Shiga idan mundawo munci abinci sai na Baku nawa labarin. Amsawa sukayi da to kowacce ta shige bedroom dinta don bacci. Asuba tagari diamond ladies. Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi 🗡️ 💕💕 ❤️ [7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨ ( Daukar Fansa ) Story& writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL ______✍🏽______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* 🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah)) *_T.W.A_* _________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________ Marubuciyar⬇️ _ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_ *DA* _ _MIJIN ZAHRA_ *Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.* Bismillahir-rahmanir-raheem. *Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai....* Page:1️⃣3️⃣--1️⃣4️⃣🖊️ _________Kijina ne yaketa aikin lugude da faduwa tashin hankali ya bayyana a fuskata nace"A'ah Abba karabu dasu Sunaso ayi kure ne Kuma ni banaso na fallasa abin kunyar da yayi namai haka. Abba yace"koma menene sai anje islamiyar. La'asar nayi Abba yatasa keyata har office din headmaster sannan aka Kira mal shafi'u,Nan kuwa ta zayyane duk abinda yafaru. Cikin bacin Rai Abba yace katanan ku zaneta,ko Kuma ni nazaneta da kaina,kukan munafurci na saka Ina fadin wallahi shegemaster ba haka akayi ba(Wai headmaster ne shegemaster) gabadaya saura rena akayi nayi nawa bayanin,nafara da cewa"tunda nashigo islamiyar yake mun maganar 'yan iska Yana cewa yasan mu talakawa ne nazo yayi iskanci Dani zai bani kudi,kullum-kullum haka yake fada da yaga naki yarda ne shine ya tsaneni yayi ta zanana,abin duka da bana duka ba yadau jibgata,shine ranan yatareni a lungun oske Wai zaiyyi iska*ci Dani nikuma na masa haka. Gabadaya Office din salati Akasa,shikuwa mal shafi'u Banda zufa Babu abinda yake alamun rashin gaskiya, shegemaster yace Ashe Mal shafi'u baka bar wannan banzar halin naka ba?to ni bazan iya ba wallahi wannan Karan Dole kabar islamiyar nan kada ka lalata yara azo ana kuka dani. Malamai kowa yace gaskiya kam kada wani Abu yafaru ayi kuka da makarantarmu,hakuri Mal shafi'u ke badawa,Ina nan kuwa akabashi red card,Ni kaina sai da yabani tausayi,but a zahiri hakinsa kenan sai dai ni baimun ba,kawai nema ma kaina mafita nayi. Nan naciga da zuwa islamiya, Aunty Saudah ma tadawo,yanzu tadena zuwa talla ni ke zuwa Ni kadai,wata Rana nayi sha'awar shiga kasuwan tudun Wada don Kai tallah,wata matace na hango tsohuwa da ita tana tafe tana
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30