Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 15

Chapter 15

Deejamah Book 1 Complete Hausa Novel 1,289 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

Muryan fauzi na rawa tace"mun shiga uku to yau ya zamuyi? Mai gadi yadu besu yace"meke faruwa ne?ko da matsala ne? Ko kafin su bashi answer Alhj Sani ya kariso Yana tambayar Mai gadi"Mal sale meke faruwa?nan me gadi yake sanar dashi duk yqnda sukayi dasu Shakeerah. Dawo da dubanshi yayi ga su Shakeerah yace"Ayya 'yan mata sai dai kuyi hakuri,but mushiga ko ruwa ne kusha don na ganku da niki-nikin akwati,tafiya yafara sukuma suka bishi a baya wannan ta kalli wannan,wannan ta kalli wannan a haka duk suka shiga Falon gidan. Wata kyakkyawan mace suka tarar akan 3sitter tana zaune tasaka tagumi,gyaran murya Alhj Sani yafara cikin Sauri ta dago tana fadin sannu da zuwa Alhj. Daure face Daddy khadee yayi tamkar Murmushi bai taba wanzu wa a face din sa ba yace"Yauwa pls shiga Daya ciki ki bamu waje,sannan ki dauko ma baki lemu. Gaishe ta su Shakeerah sukayi face nasu dauke da murmushi,itama mayar musu da murmushin tayi ta shige. Gaishe shi su Shakeerah sukayi daga nan daddyn khadee yafara tambayar su daga Ina suke,ko su 'yan uwan marigayiyar ce?lokaci daya Shakeerah karyan da zata shirya mai yazo mata a kwakwalwa tafara magana kaman haka"Daddy mu ba 'yan uwan ta bane,wata shekara ne sukayi aikin hajj da mom namu shine fa suka hada kawance tare da zumunci Bayan sun dawo sukayi exchanging din address tayi kwatan cen gidan nan shine fah mom namu tunda ga garin zaria ta turomu don duba mata ita. Girgiza kai ya shiga yo a hankali,yace"lallai kam ai tun tuni tarasu to gashi dare yayi 'yan mata ya Kenan? Shakeerah tace"No bb komai yanzu zamuje munemi hotel da safe sai muwuce. Murmushi yayi yace"A'ah ai ba za'ayi haka ba Muddin muna garin nan ai ba zaku wulakan ta ba 'yan mata yayi maganar Yana lashe harshe kaman tsohon maye yana duban Shakeerah. Shakeerah tace"Toh Daddy GODIYA muke. Daddyn khadee yasa hannu a mouth yace"shiiiiiiii babu godiya tsakanim mu,kuma kada kisake cemun Daddy as from today. "Ok daddy.....bata karisa ba tace"Au Ok tohm bazan sake ba,Murmushi yayi yace"kyawawan 'yan mata dakin ku daya? Cikin Sauri Shakeerah tace"Eah dakin mu daya baban mu daya. "Ayya anyway Bari nasadaku da daya daga cikin Mata na. Da toh suka amsa mishi sannan ya mike yatafi. Ba'a dauki wani dogon lokaci ba,matar da suka tarar a falon still itace ta dawo fuskanta still dauke da Murmushi cikin sanyin murya tace"kutaso muje ciki koh? Mikewa sukayi tare da binta ciki,sosai dakunan nasu ya burge su Zahra wani daki da basu da alamu dakinta ne,nan suka gabatar da sallolin da basuyi ba,suka kimtsa tare da wanka,ko suka fito matar ta dubesu tace"Alhj yace kuje waje Yana jiranku ku tafi, diddilo idanuwa sukayi gaba daya. Shap shap suka shirya ciikin arnayen wasu dogayen riguna masu tsada wadanda suka gaji da kyau da duwatsu. Fita sukayi suka sameshi a cikin motar sa yaci babban Riga,tun daga nesa yake sakem musu murmushi har suka kariso,baya duk kansu suka bure domin shiga,daga murya yayi yace"pls Shakeerah dawo nan mana. Sai da tayi dan jim tare da yatsine face sannan tashiga gaban,hadadden park ya kaisu suka sha ice-cream Banda kallon Shakeerah yake zuciyar sa na raya masa abubuwa da dama akan yarinyar,duk suna ankare da halin da Daddy ya shiga,ta wutsiyar Ido suke ma juna magana itada Fauzi. Daga nan wani super market yawuce dasu ya siya musu kayan shafa da takalma. Godiya sosai suka masa,daga nan daukan su yayi suka wuce gida,ledan balango ya siyo hudu da gasassun kaji Suma hudu. Koda yafaka motar a harabar gidan Fauzi tafara fita,itama Shakeerah ta balle murfin motar don fita,hannunta yariko,cikin Sauri Shakeerah tajuyo jikinta na wani irin shock don tunda take ba'a taba kokarin taba ta haka ba. Wani irin kallo ta wurga masa Wanda yasashi sakin hannun ta batare da ya shirya ba,a jiyan zuciya yayi sannan ya dubeta yace"Shakeerah yarana kusan goma sha Amma yau duk Allah yamusu rasuwa Banda sauran ko daya, sannan mata na biyun nan duk Basu haihuwa sai dai yanzu inason haihuwa sosai. Cikin bariki da sanyin jiki Shakeerah tace "ayya Allah yayi musu gafara yasa suna kyakkyawan matsayi.Ameen! Daddy ya fada can dai yace"Shakeerah Aure nakeson na kara,Ina neman wacce zata kula dani sai yau Allah yanuna mun ita. Duban shi tayi yanda yake magana like saurayi dan 30 da wani Abu. Shakeerah tace"wacece ita? Kece Mana Shakeerah kece macen da nakeso _I NEED UR COMMENT_ Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi🗡️ 💕💕 ❤️ [7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨ ( Daukar Fansa ) Story& writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL ______✍🏽______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* 🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah)) *_T.W.A_* _________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________ Marubuciyar⬇️ _ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_ *DA* _ _MIJIN ZAHRA_ *Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.* Bismillahir-rahmanir-raheem. *Da sunan Allah Mai rahama Mai Jin Kai....* _FREE PAGE_ Page:2️⃣0️⃣--2️⃣1️⃣🖊️ _________Koda ta nufi part din fulani jitayi hayaniyar tasake yawa,cikin Sauri tashiga Falon, fulani tagani duke a kasa tana kuka,wata yarinyace tsaye akanta a kalla bazata wuce sa'an marigayiya Aunty saudah ba sai wasu mata manya akan sofa su uku duk tana Kama da fulani sai guda a cikinsu,fulani tace"Hjy baraka a gabanki jikanki na zagina ba zaki tanka ba? tabe baki wacce akakira da hjy baraka tayi tace" Ai anyimata ne,nikaina Yaya kinbani mmki Saboda Kuna da kudi shine duk wulakancin da kuka ga dama sai ku sauki kan laweezah Saboda ta auri Jalal?to Meye Jalal din yakedashi da ake wannan abun? Su dai sauran matan babu wacce tatanka Banda zare Ido babu abinda suke,Laweezah ta juya tadubi fulani tace"Ku rabu da munafukar tsohuwa,tsohuwar banza wacce a haka zaki Kare. Kutumar uba kayyasa, Shakeerah tafada tana shigowa falon, gabadaya suka tsaya kallon ta ko da takariso jikake tassss! Ta dauke Laweezah da Mari,ko kafin ta Kuma cewa wani Abu tasake dauketa da Mari ihu Laweezah tasaka tana sake dafe kuncinta. Shakeerah tace"Bura ubaki wacece ke Dan Ubanki?da Zaki Zo kitsaya a gaban tsohuwa kamar wannan kina zaginta sa'anki ne? Mikewa hjy baraka tayi tace"wacece ke kekuma daga Ina kike harda zakizo kishiga fadar da ba'a gayyace kiba? Harara Shakeerah ta maka ma Hjy Baraka tace"Sanin ko Ni wacece Sam baida amfani,mgnr shshhigi kuwa yanzu nafara indai Akan fulani ne. Tajuyo ta dubi fulani tace"kekam baki da tarbiyya wallahi tallahi Muddin Ina Falon nan Kika sake zagin fulani sai na hada Miki jini da majina,tsoro sosai Shakeerah tabawa Laweezah,su kansu matan dake falon Sunyi farin cikin faruwar wannan lamarin. Karisawa wajen fulani Shakeerah tayi tare da sharemata tears ta dagata ta dorata Akan sofa,dubanta fulani tayi tanason tayi magana tasaka. Kama hannun Laweezah hjy Baraka tayi tace muje diyar albarka,wallahi kuma Marin nan dakika mata kisan cewa kinci bashi ne zanga ubanda yatsaya maki,dage kafada Shakeerah tayi tare da tabe mouth tace"Ganinan daram dam dakam a turo ubanda za'a turo dai-dai nake da kugun kowa. Fita sukayi daga cikin Falon suna zage-zage,Daya daga cikin matan tadubi Shakeerah tace"yarinyar nan Allah yayi Miki albarka wallahi duk cikin zuri'ah namu Mutane suna tsoron

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});