Skip to content
bode

Hausa Novels Portal

Chapter 3

Chapter 3

Deejamah Book 1 Complete Hausa Novel 1,294 words 0 views Progress saved
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});
Download Book

saboda suna da kokari sosai barimma shakeera,direct gida sukayo. Koda suka dawo shakeera ce da girki don haka kitchen tashiga bayan ta cire hijjab dinta. Girki tafara,tunanin Dora Abu Mai sauki tayi....a karshe ta yanke shawarar yin taliya da manja da yaji. Kwala mata Kira fauzi tayi,cikin Sauri tafito daga kitchen din tana fadin"Meye haka fauzi?irin wannan Kira haka,wat hppnd? Duban ta fauzi take tace"Zauna ki kalli TV kiga meke faruwa. Sai a lokacin ta maida dubanta kan TV. Labarai aka fara tare da pic din wani mutumi zai kai 46years,dan jaridar ne yafara magana kamar haka"To jama'a ana dara ga dare yayi,wannan wannan bawan Allahn ne malamin makarantar islamiya da yayiwa dalibarsa fyade 'yar 12years,Wanda aka dade ana nema,to gashi yau ya kawo kansa a dalilin wasu 'yan mata da suka hukuntashi a cewar su kotu ta kasa yanke masa hukunci dai-dai da lefinsa. An dai sameshi a wani kango ne Rai a hannun Allah domin an Kona masa abin fitsarin sa,a binciken da likitoci ma sukayi da wuya wajen ya sake aiki,sai dai bari muhadaku da bawan Allahn da iftila'in nan ya sameshi. Fauzi ta saki ihu tare da cewa baka ga komai ba ma kadan akayima. Nuno shi akayi a gadon asibiti an nannade joyst*ck din nasa da bandeji magana yafara bayan"Assalamu alaikum jama'ah,a yau dole na amsa lefin da na gasgata a kotu, tabbas ni nayiwa wannan yarinyar fyade. Dan jarida yace"To Allah gafarta malam me yahanaka da amsa lefin ka a kotu? A jiyar zuciya ya sauke Wanda da ka lura zakasan cewa da kyar yakeyin magana"Saboda inajin kunyar duniya,Ina tsoron mutumcina ya zube a idon duniya,na manta cewa da kunyar lahira gwamma na duniya. Dan jaridar yace"To Allah gafarta malam Aida an nemeka anrasa ko,ko zaka iya sanar damu inda ka gudu? Girgiza Kai yayi yace"Sanar daku bashida amfani,nidai abinda nasani wasu 'yan mata suka biyu ni har inda nake suka daukeni suka kaini kango,bayan sun min dukan tsiya shine suka konani,har yau Cike nake da mamaki da tsoro, Ina tunanin Anya su din mutane ne?saboda suna da karfi,sannan kuansu yayi yawa,a tunani na aljanu su suka aikata mun wannan lamarim. Dariya Dan jarida yayi sannan yace"to masu aikata wannan lamarin da masu niyyar aikatawa,Kila wannan abun fa da yafaru da Allah gafarta ya zame muku ishara a gaba. Nan dai aka gama labaran aka gama labaran,mikewa shakeera tayi tare da shigewa kitchen,ita kuwa khadeeja banda kuka Babu abinda takeyi saboda ita khadeeja akwai tausayi. Tsaki Fauzi taja tace"kedai Kika sani Sai kace ba kece mai soya mai a risho ba.....khadeeja batasan sanda ta fashe da dariya ba,don maganar ya bata dariya. Xahratty ce✍🏽 Lallai Alqalami 🖋️ Yafi takobi🗡️ 💕💕 ❤️ [7/18, 2:05 PM] Xahratty🥰😘: 💐✨ *DIAMOND LADIES* 💐✨ ( Daukar Fansa ) Story& writing By PATEEMA ZAHRA LAWAL ______✍🏽______ *TAMBARI WRITER'S ASSOCIATION* 🔱(( Home of Expert and talented writers,da tambarin mu muke tafe domin kawo gyara da cigaban Al'ummah)) *_T.W.A_* _________________________ https://www.facebook.com/Tambari-writers-Association-106058867819812/ _________________________ Marubuciyar⬇️ _ _A DALILIN 'YAR TSUNTUWA_ *DA* _ _MIJIN ZAHRA_ *Littafin diamond ladies (Daukar Fansa) na kudi ne duk maiso ya turo katin Naira dari#100 katin waya ta wannan number 08060710719,sai nayi adding din mutum a group din.* Bismillahir-rahmanir-raheem. *Da sunan Allah Mai rahama Mai jin Kai....* Page:1️⃣3️⃣--1️⃣4️⃣🖊️ _________Kijina ne yaketa aikin lugude da faduwa tashin hankali ya bayyana a fuskata nace"A'ah Abba karabu dasu Sunaso ayi kure ne Kuma ni banaso na fallasa abin kunyar da yayi namai haka. Abba yace"koma menene sai anje islamiyar. La'asar nayi Abba yatasa keyata har office din headmaster sannan aka Kira mal shafi'u,Nan kuwa ta zayyane duk abinda yafaru. Cikin bacin Rai Abba yace katanan ku zaneta,ko Kuma ni nazaneta da kaina,kukan munafurci na saka Ina fadin wallahi shegemaster ba haka akayi ba(Wai headmaster ne shegemaster) gabadaya saura rena akayi nayi nawa bayanin,nafara da cewa"tunda nashigo islamiyar yake mun maganar 'yan iska Yana cewa yasan mu talakawa ne nazo yayi iskanci Dani zai bani kudi,kullum-kullum haka yake fada da yaga naki yarda ne shine ya tsaneni yayi ta zanana,abin duka da bana duka ba yadau jibgata,shine ranan yatareni a lungun oske Wai zaiyyi iska*ci Dani nikuma na masa haka. Gabadaya Office din salati Akasa,shikuwa mal shafi'u Banda zufa Babu abinda yake alamun rashin gaskiya, shegemaster yace Ashe Mal shafi'u baka bar wannan banzar halin naka ba?to ni bazan iya ba wallahi wannan Karan Dole kabar islamiyar nan kada ka lalata yara azo ana kuka dani. Malamai kowa yace gaskiya kam kada wani Abu yafaru ayi kuka da makarantarmu,hakuri Mal shafi'u ke badawa,Ina nan kuwa akabashi red card,Ni kaina sai da yabani tausayi,but a zahiri hakinsa kenan sai dai ni baimun ba,kawai nema ma kaina mafita nayi. Nan naciga da zuwa islamiya, Aunty Saudah ma tadawo,yanzu tadena zuwa talla ni ke zuwa Ni kadai,wata Rana nayi sha'awar shiga kasuwan tudun Wada don Kai tallah,wata matace na hango tsohuwa da ita tana tafe tana dingisa kafa daka ganta bata cikin wahala sai dai daga gani rigimammiya ce,wani ne ya taho da Sauri ya bangaje ta,Aiko tsohuwar nan ta baje a kasa,babu Wanda yamasa magana nan kuwa yafara magana Yana karkata mouth alamu dai Dan daba ne ku tsofaffin nan 'yan iska ne taya Zaki shigo kasuwar mu wallahi kinci darajar ke tsohuwa ce da nayi Miki bakin aiki,cikin tsiwa na taho na dagata ina cewa sannu kaka,amsawa tayi tanamun godiya. Zagina yafara Yana cewa Ni ajawon inace don uwata?banza na masa ganin hakan yasa yajiyo gabana ya dauke ni da mari dafe kunci na nayi Cike da azaba don naji zafi sosai kada kumanta a lokacin 12years gareni bansan sanda nayi kukan kura na dauki bucket din pure water Dina ba na buga masa, dai-dai lokacin wani Dan sanda yazo wucewa Aiko ya kariso Yana tambayar neje faruwa?Nan kuwa tsohuwan nan ta zayyane mai komai tana kuka,albarka yasamun sosai sannan yace nakai tsohuwar gida,tab nida bansanta ba daga haduwa taya zansan gidanta,a gaskiya tacema Dan adai-dai tan da ya daukemu take,tayimai kwantancen layin Aiko nan aka kaimu. Wani dankareren gida mukaje Wanda tunda nake bantaba ganin gida mai kyau da haduwa irin gidan ba don haka nema cikin zumudi nabita gidan,gani nayi ma'aikata kowa na ya duke a kasa Yana kwasan gaisuwa tsoro ne yakamani bansan sanda na diddilo idanuwa waje ba Fadi nake " _innahu min sulaimanu wa innahu bismillahir-rahmanir-raheem_ yau nakawo kaina mahallaka garin temako,wani falo muka isa babba mai cike da Kayan alatu wallahi kamar ba gidan mutane ba Zama tayi a wani kujeran one sitter tare da dannna wani kararrawa,can sai ga masu aiki sun Kai goma suka taho ajere,kirari suka fara mata tare da zubewa suna kwasan gaisuwa,Murmushi tayi ta dubi daya daga cikinsu tace"Jakadiya!wacce akakira da jakadiyar na kalla babban macece sanna tafi sauran shekaru kayanta daban ne Kuma duk cikansu suna jinsu neat. Murmushi tayi jakadiyar tare da karisowa tana fadin"gaisuwa nake uwar dakina uwar gida sarautar mata gani gareki fulani. Murmushi tsohuwan nan takuma tace"Uhm kuntashi hala baku ganni ba? Eah wallahi fulani tunda banganki ba nace yanzu haka kinje zaga gari ne kamar yanda Kika Saba. Murmushi tayi tace"Aikam nan take Basu labarina tanuna ni sannar ta sanar masu da duk abinda yafaru,duk cikansu kallo na suke Cike da mamaki da yanda nayi fada da Dan

Table of Contents

Chapters

30 chapters
  1. 1 Chapter 1
  2. 2 Chapter 2
  3. 3 Chapter 3
  4. 4 Chapter 4
  5. 5 Chapter 5
  6. 6 Chapter 6
  7. 7 Chapter 7
  8. 8 Chapter 8
  9. 9 Chapter 9
  10. 10 Chapter 10
  11. 11 Chapter 11
  12. 12 Chapter 12
  13. 13 Chapter 13
  14. 14 Chapter 14
  15. 15 Chapter 15
  16. 16 Chapter 16
  17. 17 Chapter 17
  18. 18 Chapter 18
  19. 19 Chapter 19
  20. 20 Chapter 20
  21. 21 Chapter 21
  22. 22 Chapter 22
  23. 23 Chapter 23
  24. 24 Chapter 24
  25. 25 Chapter 25
  26. 26 Chapter 26
  27. 27 Chapter 27
  28. 28 Chapter 28
  29. 29 Chapter 29
  30. 30 Chapter 30
(adsbygoogle = window.adsbygoogle || []).push({});