Chapter 29
Chapter 29
alamun ta nagane ita din ba 'yar hannu bace,domin ambatar sunan Allah da take tayi,na bata abincin Wanda na girki da jini sam taki ci. Daddy yace"Yauwa wannan ba damuwa bane Muddin bata gane ko mu su wanene ba. Tsohuwa tace"wannan Kan bata gane ba. Kudi Daddy yaciro masu yawa yaba tsohuwa sannan ya mata sallama,sai daga musu hannu take shikuma Daddy yaja motan shi yayi gaba. Duban shi Shakeerah tayi tace"wallahi papi Dole Allah ya dauka ka Saboda temakon da kakeyi tsohuwar nan tabani labarin komai,Ashe ita 'yar gudun hijira ce na maidugri ankashe mata kowa nata,shine ta gudo nan ka temaka? Murmushi Daddy yayi yace"hakane My Queen. Shakeerah tayi face din tausayi tace"Allah sarki papi na I luv yhu. Peck yabata a forehead dinta sannan yace"Me too dear. A hankali suka Isa asibitin,wasu mutane ne masu Kaya jajaye Riga da wando da hula duk sun cika asibitin,face dinsu Sam babu alamun wasa ko alheri,kallon tsana Shakeerah ke binsu dashi,maza goma mata uku duk sun fahimci kallon da Shakeerah ke musu,hannun ta sakale da na Daddy,duk inda suka wuce gaishe da Daddy kawai suke har suka Isa cikin dakin. Nan suka cidda Mr Patrick da matemakin shi Alhj Hamza sai matansu,duk Kayan su iri Daya ne harda matan wato jajaye suna zagaye da Shakeerah. Sosai hankalin Daddy yatashi don Sam baisan da zuwan su ba. Idanuwan su babu kyan gani suke duban Daddy Shakeerah,shikuwa Daddy Cike da rudewa yqce"Welcome sir dama zakuzo ne baku sanar Dani ba? Duk da cewa Shakeerah da zaka shiga cikin kokan ranta wani mahaukacin tsoro da tashin hankali ne a ciki,daya bayan daya take kallon su,sannan tazaga inda gadon Aunty amarya n Yqke,lokaci daya ta dashe tayi wani irin fari fat kaman babu jini a jikinta,taba jikin ta Shakeerah tayi sannan ta dago tana duban Daddy,duk cikan su Kira mata Ido sukayi,Cike da bariki Shakeerah tace"Wayyo Allah na,Papi pls wallahi yunwa nakeji kazo ka kaini gida ko wajen Shan ice cream,kazo ka kawoni wajen wasu mutane masu kama da aljanu,kawai Allah bai canza ku ba,ku kun canza kanku. Ransu gabadaya ya baci, Mr Patrick yace cikin gwarin husar shi"Sani wannan kuma wacece mara kunya ka taho da ita ko gaishe da mutane bata iya ba,Cike da bacin rai Mr Patrick yayi maganar Wanda sai da gadon dakin w Yayi wani irin girgiza,sosai Shakeerah ta tsorata sai dai duk kokarin ta na dakewa sai da dan tsoro kadan ya bayyana a face din ta. Muryan Daddy na cracking yace"Itace matar da na kara Aura. Gabadaya suke mata wani irin kaskan taccen kallo,Babu wani tsoro ko tantama Shakeerah ta rama,duk cikan su diddilo idanuwa sukayi waje,cikin muryan tsawa Mr Patrick yace"Sani ka dauko Mana annoba kayi gaggawar daukan ta kubar asibitin nan. Cikin rawar jiki Daddy ya ruko hannun Shakeerah yajata zuwa waje,a zafafe yake tafiya,bude bayan motar yayi ya wurgata wanda Sai da Shakeerah ta buge"Auchhhhh tafada tana shafa inda ta bige,sosai Daddy ke gudu a motar da yake dare ya fara. Allah kadai yakawosu gida lafiya,ya shiga da motar tare da fusgota ya dinga Jan hannunta har zuwa part dinta,sosai baba megadi ya shiga tashin hankali Saboda ganin abinda ke faruwa yau a gidan. Dakinta ya shiga da ita ya wurga ta akan daya daga cikin sofan falon,a zafafe ya nufo gareta,wanda tunda Shakeerah take bata taba ganin sauya wa irin na Daddy haka ba,kamo kafadunta yayi cikin kakkausar murya da daga tsawa yace"Shakeeerah wacece ke pls?wace irin hatsabibiya ce ke? andade ana jamana kunne Akan akwai wacce zata rushe mana kungiya dama kece?yasake daka mata wani uba uban tsawa. Jikin Shakeerah babu inda baya rawa tafashe da kuka domin tsakani da Allah don tsorata Shakeerah ta tsorata muryan ta na rawa tace"Papi bansan me kake nufi ba,wallahi niba kowa bace face matarka.... Bata karisa magana ba ya fisgota tare da dauketa da mari,Kara Shakeerah tasaka,ya shakota yqce"karya kike munafuka Sai na kasheki,wallahi Shakeerah na tsane ki,duk Wanda zai shiga cikin sabgan al'amura na zan kauda shi wallahi I hate yhu. Yayi maganar yana buga kanta da jikin bangon dakin,wani Kara Shakeerah tasaki wani Kara tare da sulalewa a kasa jini nabin goshin ta. Wayan Daddy ne yayi Kara Koda ya duba yaga Mr Patrick ne, picking call din yayi,cikin kakkausar murya Mr Patrick yace"kuyi maza kuzo akwai meeting. Fashewa Daddy yayi da kuka yace"Shakeerah kin cuce ni,nayi dana sanin saninki,Kuma da hannu na zankashe ki,ya karishe maganar yana hambare ta da taka mata ciki sannan yafita ya barta kaman matacciya. Shida hjy Sameera suka fita a mota guda. ^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^^ Wajen shiru ne Babu abinda ke tashi sai hucin Mr Patrick suna tsaye curku curku duk kawunan su a katsa. Daddy ne duke a kasa yayi kneel down hankalin sa a tashe. "Kacuce mu Sani, wallahi wallahi wallahi inaso kasani Dole ka kawo mana jinin ta wannan Karan kada ka kuskura kace zakamun gardama. Dole ne musha jinin jikin dubban jama'ah wannan Karan sannan harda megadin ka driver naka, sannan wancan mun kasheta mun yarda gawarta,inaso ka maida hankali zakaji abinda boka mukhit zai fada. A hankali tsohon ya taho da sanda a hannun sa,yanajin sa da wani gajar ta,Kai a takaice dai wada ne ma,sai kace wani tsohon aljani. Wani irin dariya bokan ke saki yana kyalkyalewa da dariya lokaci daya ya miko musu kwaryan jini ya aje a babban saman table din dake wajen jini ne a cikin kwaryan,duban Daddy yayi a furgice cikin muryan tsawa yace"Sani matarka daukan fansa yakawo ta cikin gidan ka,bamu fahimci abinba sai dazu a asibiti da sukayi ido hudu da Patrick nagane ko ita wacece, idan bamuyi wasa ba itace silar tarwatsewar kungiyar mu Muddin bamuyi wasa ba, idan muka bi wannan hanyar shine zaisa musamu rufin asiri duniya da lahira. Cikin Sauri Mr Patrick da Alhj Hamza suka dubi boka mukhit suka hada baki wajen cewa"Menebe wannan Boka? Kualkyalewa da dariya Boka mukhit yayi zuwa can ya turbude face yace"Saimun bawa aljanu jinin yarinyar sun tsotsa sun shanye tass mukuma mun cinye danyer naman ta,wannan dalilin zaisa musamu nasara a kungiyar mu. Mr Patrick ya dubi Daddy yace"Toh kaji Sani saika zaba ko Kai ko hjy Sameera ko Amaryan ka. Cikin Sauri hjy Sameera tace"Inah badai niba sai dai shi da fitsararriyar Amaryan sa. Daddy idanuwan shi Sunyi ja jazur yace"Nariga nabada jinin ta domin yanzu na tsaneta,na mallakama aljani misewit jinin matata Shakeerah. Wani irin ihu aka saka a wajen suna bubbuga sandina a kasa suna fitar da harshe Cike da farin ciki,Wanda rabon da susamu kamarshi tun kafin Daddy ya Aure Shakeerah. Ranar sunsha jini kaman babu gobe kamar ba jinin bil'adama ba, Mr Patrick ya wakilta Daddy da matar sa da hjy Sameera da Alhj Hamza,kan zuje sudauko Shakeerah. Sosai hjy Sameera ke farin ciki yau yarinyar da tafi tsana zata mutu a wulakan ce,motoci biyu suka hau sukayo gidan Daddy wajen karfe 1:30 na dare. Layin tsit babu abinda ke tashi sai karar motar su Daddy,Koda suka zo bakin gate din gidan a wangale suka ga gate din don haka cikin Sauri suka shiga da motocin a zafafe wasu katti suka nufi dakin baba megadi,abin mamaki babu baba megadi Babu dalilin sa,a hargitse suka nufi part din Shakeerah Wanda yake a
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30