Chapter 5
Chapter 5
din Chip's sukayo gida. Sallah suka gabatar Cike da gajiya suke,sannan bayan sallah isha'i khadee ta cigaba da Basu labarin a baya. "Bayan rasuwar Aunty sakina gaba daya 'yan gidanmu sun gama tsorata da al'amarin,haka Kuma 'yan Unguwa har takai ba'ason hulda dasu Ummina. Aunty Nana kuwa jikinta yariga ya gama sanyi tasan cewa yanzu itace next. A kwana a tashi Babu wuya har shekaru suka shude da watanni babu Wanda aka sake kashewa a gidanmu,kwatsam inada 13years lokacin Ina j s s 2 aka wayi gari an tsinci gawar ya Anas Wanda yakebin Aunty sakina innalillahi wa Inna ilaihirrajiun a lokacin hauka ne kawai hajy saddiqa batayi ba,ganin haka yasa Ummina ta shirya wata ranar laraba Babu kowa a gidanmu domin Daddy da hjy sameera wajen aikinsu daya,itakuwa hajy saddiqa tatafi gidansu sha'ani. Shiryawa Ummina tayi ta hada Kayan Aunty Nana gaba daya tasa driver ya daukemu ya kaimu tasha, daganan motar maidugri muka hau wajen yayar Ummina da bata taba haihuwa. Already tasan da zuwan mu,don haka munsamu tarba mai kyau,Bayan munvi abinci munhuta Ummina tayima yayarta bayanin abinda ke faruwa,itama tabata goyon baya hundred percent,sannan Ummina tace to ga amanar Aunty Nana nan tabata ita Amana. Tayi farin ciki mara misaltuwa saboda macece Mai hakuri da son yara,uwa uba ga addini da dukiya,mijinta ma yayi farin ciki duk da bada izini Daddy aka kawo Aunty Nana ba. Washegari suka shirya da Ummina da yayarta sukaje hospital aka juya mata mahaifa bazata sake daukar ciki ba,domin ummina tace"ita tana zargin Daddy ke kashe masu yara. Kwanan mu daya muka dawo duk da nida Aunty Nana munyi kukan rabuwa da juna sai dai hakan shine mafita. Koda muka dawo gida Daddy da Hjy sameera Basu dawo ba sai hjy saddiqa,nan Ummina ta sanar da ita abinda ke faruwa,itama tayi farin ciki sosai Kuma ta bata goyon baya. Wata Rana hjy saddiqa tafara ciwo Wanda anyi magani abin kaman gaba yakeyi,Ashe Daddy ne yafara amfani da ita ta baya,shine fah tsutsotsi suketa cinye mata wajen,hatta kashi Bata iyayi sai dai wajen yayi ta zubar da jini,dalilin sanin ummina kuwa ita da kanta hjy saddiqa ke sanar da Ummina, gaba daya ta rame taui bakinkiri babu kyan gani. Duk mutuwar da akeyi ba'a taba wanda ya girgiza ummina ba sai na wanna Karan,domin Allah yayiwa hjy saddiqa rasuwa,a dalilin homosex da Daddy yayi da ita,sai dai abin takaici likitoci sun boye,shida kanshi yamata sittura aka kaita. Sajida tadawo hannun Ummina da Zama, nida ita sai muka koma kamar twins,ummi dalilin ta dena fita ita kadai saidamu,sanna ta dena aikemmu ko Ina hatta wajen Daddy,wannan dalilin ne yasa Daddy suka fara tsiya da Ummina,sanna yace saita nemo Aunty Nana duk inda ta kaita, Ummina tace bazata nemo taba. Wannan dalilin yasa Daddy ya tsani Ummina sannan hatta abinci yadena bamu,da kula damu,hatta ni saboda tsanar da nanuna Ina Mai karara. Ummina ta Kira ya mashkur ta sanar dashi abinda ke faruwa,yaso daukar mataki,Amma Ummina tana tsoron kada mutumci na Daddy ya zube. A sirrince Daddy ya siyama Ummina gida a garin Zaria. Wani dare Ya mashkur yaturo wani abokinshi ya daukemu muka gudu,komai bamu dauka ba hatta kayan sawarmu,bayan komawarmu da wata biyu aka daura Auren ya mashkur cikin jimamin rashin ganin Ummina da yaranta,ko taron biki 'yan bauchi da dangin Ummina basuyi ba saboda jimami,Daddy na kuwa hankalinshi ya tashi na rashin ganinmu. A halin yanzu Daddy yakara aure da matansa ta haifi yara biyar,Amma yanzu saura uku biyu sun rasu,a shirye nake yanzu Dan daukar fansa da hukunta Daddy na da temakon ki Shakeerah,domin nasan Babu mai temako na sai ke, mahaifina babban mai lefi ne. To wannan shine labari na. Cike da tausayi duk cikansu fauzi da shakeera ke duban khadee, Shakeerah tace"Innalillahi wa Inna ilaihirrajiun tunda nakejin labari bantabajin irin labari irin wannan ba,tabbas Sai an hukunta shi,ke da duk Wanda keda hannu a wannan annobar hatta munafikin likitan Daddyn ki. Fauzi tace"Tabbas wannan yacika azzalumi Allah yasaka muku,insha allahu sai yayi mummmunar karshe,ki yahakuri mahaifinki ne,Amma meyasa kikace mun ke 'yar bauchi ce? Khadee ta share tears din da suka zubo Mata tace"Eah Mana ni bauchi nasani garinmu,bakiji labarin bNe? Fauzi tace"ok naganae sorry kinji kada kidamu kinji? Khadee tace"kada kidamu am ok. Shakeerah tace"to ya maganar sajida ita tana wane skul ne yanzu? Khadee tace"tana A.B.U teaching hospital ne yanzu tana karantar dental. Shakeerah tace"Allah sarki ummi taga iftila'i,to maganar Aunty Nana fah? Khadee tace"tayi aure yanzu haka tana kasar Argentina ta auri wani dan jarida. Shakeerah tace"Allah sarki rayuwar duniya duk babu dadi,idan kana ganin damuwar ka idan kaga na wani sai jikin ka yayi sanyi. Fauzi tace"Allah sarki ni kuwa sai na dunga ganin kamar tawa damuwar tafi ta kowa. Shakeerah ta buga tagumi tace"Fauzi muna sauraranki. Fauzi ta cigaba dafari dai, "Sunana Fauziyya Aleeyu ni haifaffiyar garin gombe ce,mahaifina mutum ne mai rufin asiri dai-dai gwargwado gaskiya mu ba masu kudi bane,mahaifiyata wacce nike cema Inna mu uku ta haifa nice babba Sai kannena su biyu duka Mata,sana'ar mahaifiyata sai da manja da man gyada Kuma Alhamdulillah Yana rufa Mana asiri,shikuwa mahaifina icce yake siyarwa,a haka Allah ya rufa musu asiri suka samu a makaranta. Kishiyar Inna ta muna kiranta da baba ladi tanada yara hudu duka mata,tunda muka taso muka cidda baba ladi itace ke mulkar gidan mu sai abinda tace ayi akeyi,da yake Inna macece mai hakuri Sam magana ba yadameta bane,a hankali nataso da bakin jini a gidanmu har a wajen Inna ta wanda narasa dalili,ana cewa babu Wanda yakai mahaifiya son 'yayanta,Amma Banda tawa mahaifiyar domin kuwa a cikin wahala na taso,mutum Daya ne zuwa biyu nake raba naji dadi,mahaifina da yayata 'yar-'yan baba ladi itace babbar 'yarta. Sune kawai kesani bakin ciki abubuwa da dama idan Inna ta tayimun Zama nake na tambayeta anya ita ta haifeni? Tunda nataso bantaba Jin dadin uwa ba,itace kyara hantara,lokuta da dama nasha kwana bansa abinci a bakina ba,inda Allah yake temako na wajen kanne na nake kwata nace wallahi Muddin bazanci ba Suma ba zasu ciba,saboda inada bakina to abubuwa da dama su suke temakona,a cikin kannena akwai khadeeja wacce muke cema dijee,yarinya ce mai natsuwa jinimmu ya hadu sosai,hadasiyya itace ke bina sai dai ko kadan bamu ga maciji,itace 'ya mafi soyuwa a zuciyar Inna saboda ita ta amince da talla,muko nida hadasiyya da babbar yayarmu munason karatu ,sai dai ita Kuma baba ladi duk cikin yaranta babbu wacce takeso kamar Yaya kaltume babbar yayarmu,kujifa wayau,eah Mana wayo saboda ita baba ladi tana zuga Inna ta mana tijara Amma ita Sam Bata ma yaranta,yaranta tamkar kawayenta,zata zauna taji duwarsu Amma Banda tamu uwar. Kullum idan na zauna Ina tunanin anya hakanan baba ladi tabar Inna?sai dai ance zato zunubi don haka cikin Sauri nake goge wannan zaton a Raina. Har yazo takai mahaifinmu yakwanta jinya,duk tausayi irin na Inna sai da ta canza hali,daga ita har baba ladi Babu Wanda yadamu da rashin lafiyar baba,nida dijee da Yaya kaltume ke jinyar sa wannan dalilin yasa Inna tace Muddin bamu rabu da jinyar baba ba zata tsine mana nida dijee. Nikam cewa nayi bazan bar jinyar mahaifina mai tausayamun ba,sai dai duk abinda zatayi mun tayimun. Inna bata tsine mana ba,sai
Table of Contents
Chapters
- 1 Chapter 1
- 2 Chapter 2
- 3 Chapter 3
- 4 Chapter 4
- 5 Chapter 5
- 6 Chapter 6
- 7 Chapter 7
- 8 Chapter 8
- 9 Chapter 9
- 10 Chapter 10
- 11 Chapter 11
- 12 Chapter 12
- 13 Chapter 13
- 14 Chapter 14
- 15 Chapter 15
- 16 Chapter 16
- 17 Chapter 17
- 18 Chapter 18
- 19 Chapter 19
- 20 Chapter 20
- 21 Chapter 21
- 22 Chapter 22
- 23 Chapter 23
- 24 Chapter 24
- 25 Chapter 25
- 26 Chapter 26
- 27 Chapter 27
- 28 Chapter 28
- 29 Chapter 29
- 30 Chapter 30